Sashe 41
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Amman kamin ta saba din ai aiki ne, ina ganin replacement din ta za ayi da Hindatu, akai gurin wanda mu kai maganar da shi daman ya ce Hindatu tayi masa girma, sai a bashi wannan yarinyar mu huta”
“Haka ya dace, amman kuma an mata allurar yanzu idan kika kaita, ai bata san komai ba”
“Idan ta fara can suka ji ba zasu iya ba su dawo da ita, sai ta karasa a nan, ni bana son kuka so kadan”
Likitan ya yi dariya. Haka yabi yara yana ta musu allura wasu ta biyu wasu kuma ta uku har ta hudu ma, bayan ya gama ta kirga kudinsa ta mika masa.
HAMEEDA POV.
Kamar yadda Isma'il yai mata alkawarin zuwa dare sai gashi ya zo, sai yau ba inda suka saba tsayuwa ta tsaya da shi ba, sai ta koma da shi can wani bangaren na gidan inda ba kasafai ake sauke baki a can ba.
Bayan sun zauna ya mika mata wayarta.
“Kin ga hoton yarinyar, Doc Hafsat ta fada min cewar ba a san inda iyayenta suke ba, rikon da Zain ya bata na yarinyar sai da ya roki karta fadawa kowa, daga lokacin da yaji labarin Yayanta Dsp ne sai ya dauke yarinyar daga gidan ya maida ita gidan yayarsa wacce daman can a bakin gida ya tsinta kamar yadda Doc Ibrahim ya fada mata”
“Karamar yarinya ce balle na ce Zain son ta yake, amman har ga Allah ina kishin abunda Zain yake so”
“So ba shi da kankanta Hameeda, zai iya yayuwa Zain sonta yake, idan har ba son ta yake ba, miyasa zai damu da ita har haka?”
“Ka daina zigani da yawa Isma'il ka san ina son Zain sosai”
“Gaskiya nake fada miki”
“Ina tunanin yarinyar nan tana gidan Anty Ummi ko? So yanzu ina za a samu iyayenta?”
“Samun iyayenta abu ne mai wahala gurin yarinyar da ba a san inda ta fito ba, ance yarinyar yar kauye ce kauyen Kufawa kuma ana zargin an kashe kowa nata, Hafsat ta fada min Yayanta yafi zargin sata to Zain yai yi”
“Babu abunda zai sa Zain ya sato karamar yarinya kamar wannan, amman les assume wannan bakar Ummi ce ta sato ta”
“Taya?”
“Nima ban sani ba, amman ina son ka kara bincike ka tabbatar yarinyar nan bata iyaye a kusa sannan kuma ina son ka bincika idan tana gidan Anty Ummi yanzu haka”
Ta mika masa atm din dake hannunta.
“Akwai 500k a ciki, zasu isheka kudin transport”
“Ki tabbatar wannan abun da zaki yi be shafe ni ba, kar ki sake ko sunana ya fito ciki”
“Baka da matsala”
Daga haka ya tashi ta zakoshi har gurin motarsa sai da ya shiga sannan ta dawo ciki gida, part din Dada ta nufa tana shiga ta samu Zain zaune sama kujera ya lumshe ido kansa a sama kamar mai bachi.
“Sannu Yarima”
Be amsa ta ba, be kuma bude idonsa ya kalleta ba har ta shige dakin Dada sannan ya tashi ya fice daga falon.
[3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *HAFSATU MANGA*
31
HAMEEDA POV.
Farhat na fita Hameeda ta koma dakinta, ta kira Abida waya ta sanar mata tana nan ciki tana jiranta, kamin abida ta shigo dakin ta bude handbag dinta ta dauko wani rubutu a gora rike a hannunta, fitarta ta mata dadi daman tana neman hanyar da zata saka zuba mata wannan rubutun. Abida na shigowa ta mika mata.
“Je ki zuba mata a kofar shiga falonta, kuma ki tabbatar ko ina ya samu”
Cikin yanayin damuwa Abida ta kalleta
“Ranki ya dade idan kuma wani ya ganni fa?”
“Babu wanda zai ganki, wai Abida mi yasa kika yi sanyi ne? Sai kace bake ba, a abaya fa ke kike nuna min wata hayar amman yanzu kina zame jiki kamar kina munafuntata, ko dai so kike na cigaba da zama a haka? Na bar mutane da suka cuceni su ci bulus? Baki son farincikina ne?”
“Allah ya taimaki Shugabata, nafi kowa farinciki da farincikiki, amman ina tsorona abunda zai biyo baya, kin ga ni bani da gata a masarautar matukar aka kamani da laifi Zain ba zai taba yafe min ba”
“Ki kwantar da hankalinki babu abunda zai faru, idan har na rasa abu to ya kamata kowa ma ya rasa shi, tun har sun fara min wani kallo na daban, ya kamata na nuna musu ko wacece ni”
Abida tasa hannu biyu ta karba.
“To ranki ya dade”
Tashi tai ta fice daga dakin bayan ta rufe rubutun cikin zanenta. Wata number Hameeda ta nemo ta aika mata sako.
_Fauziya gani nan zuwa_
Hijabinta ta dauka ta saka sannan ta dauki makullin dakinta ta rufe dakin, ta sauka kasa ta nufi sashensa Dada kasancewar ita part dinta a kasa yake.
“Assalamu Alaikum”
“Amin Wa'alaikussalam, Hameeda”
“Na'am Dada sannu da hutawa”
“Yauwa fita zaki yi?”
“Ee gidansu Fauziya zanje, na ce ko kina da masaniyar Farhat ta fita?”
Dada ta kalleta da sauri.
“Wace Farhat?”
“Farhat dai, dazun nan ta fita ita kadai, babu yadda zan yi ba na tsayar da ita, amman sai ta rika fada min magana marar dadi”
“Ita Farhat din?”
“Ee ita fa”
“Waya bata izinin fita?”
“Nima ban sani ba, amman in ba Zain ba wa zai bata? Yau dai anyi abunda ba a taba yi ba a gidan nan, ni dai na fita”
Dada ta dauki wayarta ciki da bacin rai ta kira number Zain...
“Saboda mai zaka bawa Matarka izinin fita bayan kasan mace bata fita a gidan nan sai tayi wata biyar, Haleema ma watan ta nawa kamin ta fita”
Yana picking Call ta fada masa haka, shiru yai yana nazari, shi dai be san ya ce Farhat ta fita ba.
“Ko baka jina?”
“Wadannan dokokin Dada Farhat ba zata iya binsu ba, zamani ya canja babu amaryar da zata iya zama a wadannan watannin ba tare data fita ba”
“O kai kai nata izinin fitar kenan”
“Idan ban bata ba ai ba zata fita ba”
“To yayi kyau bari Mai Martaba ya dawo”
Sai Zain ya saka mata dariya.
“Haba dai uwargida miyasa kike haka ne? Komai akai da wanda ya kai da wanda be kai ba ki dauka ki kaiwa Mai Martaba, gaskiya wannan kishin naki ya yi yawa”
“Ba wani kishi yarinyar nan ta malleka mal, komai tai maka baka iya cewa komai”
“Ba wani mallaka tsananin biyayyace kawai, ba fa nesa taje ba gidan Anty Ummi ta tafi”
Taja tsaki ta kashe wayar, shi kuma yasa dariya. Ba shi tabbacin inda taje amman ya san ba zata wuce gidansu Anty Ummi ba, idan kuma har ba can taje ba to ina taje...?
“Wannan yarinyar banza yarinyar ce”
Ya sauka daga saman motar dake zaune ya bude ya shiga, ya dauki hanyar gidansu Anty Ummi.
ANTY UMMI POV.
Zain mutumen daya fara zuwa mata a rai, domin shine kadai mutumen da ta san zai iya komai akan Hafsatu manga, amman anya Zain zai iya ci mata mutunci har haka? Taya zai iya runtse ido ya yarda a wulakanta police ya shigo mata har cikin dakinta? Idan kuma yan uwan Hafsatu ne ko iyayenta taya aka yi suka san ta yi zama gida? Waya fada musu gidan?
A take tambayoyin suka zo mata, bata samu amsar tambaya ko daya ba, daya daga cikin police din wacce ta kasance mace taje ta rika kafadarta. Tashi tai ta nufi inda Hijab dinta yake ta dauka ta saka, sannan suka sakota gaba kamar wacce tai kisan kai. Gurin motarsu suka nufa da ita sai ta tsaya ta ki shiga.
“Ku min alfama mana na shiga motata tare da police biyu”
“Ba za a miki wannan ba”
“To bari na shiga motata”
Bata gama rufe baki ba, daya daga cikinsu ya sauke mata mari a fuska, kana ganinsu kasan babu wasa a tare da su, da alama an fada musu karsu sassauta mata ne.
“Akan me zaka daga hannunka ka mareni? Kasan abunda ka aikata kuwa? Kana da uniform amman baka san dokokin kasa ba? Babu dokar da tace a dake ni, ko da an tabbatar da laifin balle zargi kuke yi, i know my right no one can humiliate me”
Ta fada cikin fada, tun da take a rayuwarta ba a taba wulakantata kamar haka ba, mutumen kamar jiranta yake sai ya tisa keyarta da karfi cikin motar, bata tsaya tirjiya ba, gudun kar su sake wulakantata. Farhat da Baba Asabe na tsaye jikin kofar falon suna kuka har suka wuce da Anty Ummi, Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un kawai Malam Adamu ke fadi, kamin ya dauko wayarsa ya kira Alhaji Masa'ud wato mijin Anty Ummi ya sanar masa.
Sai da Farhat ta kama hanyar fita daga gidan Anty Ummi ta tuna da Zain be san da fitarta ba, ya zata tayi yanzu ta koma gida? A dayan bangaren kuma tana tsoron haduwa da Ya Bashir saboda unguwarsa ce ga shi kuma gidansa baya da tazara sosai tsakaninsa da na Anty Ummi.
Cikinta ta soma jin yana murda mata kamar yadda yai mata a daren farko, a haka ta daure ta kama hanyar titi ba dan ta san abun yi ba, wasa wasa cikin ya fara motsa mata sosai har ta soma kasa magana, risinawa tai kasa ta rike cikin bakinta na cika da jini. Babu mutane sosai a gurin amman hakan be hana daidaikun motoci da kuma mutanen dake kai da kawo kallonta ba.
Wani Mai napep ne ya faka kusa da ita
“Malama lafiya”
Tana dago kai tai ta kalleshi, sai da ta tofar da yawun bakinta sannan ta ce
“Ba komai”
“Ba komai naga jini a bakin ki?”
Kokarin mikewa take tsaye, sai amai ya cika mata baki, a take ta fara kwarara aman jini a gurin tana wani numfashi kamar ranta zai fita.
“Sannu”
Ya fada yana yana fitowa daga Napep din, a nan mutane suka fara tsayawa ana kallonta.
“Dan Allah kai ni gidan can”