← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 93

Sashe 20

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya saka Hafsatu manga a gaba sai kallonta yake kamar yau ya fara ganinta, a kullum Hafsatu canja masa take, yanayinta yana masa kamar na Haleema duk da kasancewarta karama. Hannu ya kai saitin fuskarta ya shafa kumatunta da yatsansa, take yanayinsa ya canja bacin rai ya mamaye masa zuciya, kokarin kawarda abun yake tare da jan numfashi a hankali ya sauke yana jin babu dadi.

Haka yake ji a duk lokacin daya tuna abunda ya sameta, gani yake kamar shine silar komai ya kasa yafewa kansa, kansa yake ta dorawa laifin, sosai yake tausayin halin da take ciki, idan ya tuna wanda zata shiga sai ya nemi sukunin dake tare da shi ya rasa, hakan yasa ya kasa cireta a ransa da kuma al'amurransa, duk kuwa da irin fada da kuma halin ko inkula da Anty Ummi take nuna masa akanta, duk abunda yake tana cikin ransa ba shi da  natsuwa idan baya kusa da ita, gani yake babu mai mata daidai sai shi, gani yake babu mai fahimtarta sai shi, idan dare ya raba kuma yana gadinta har garin Allah ya waye, saboda razana da take idan ta farka babu kowa a kusa da ita, gashi duk dare sai ya mata addu'a take iya bachi, ji yake kamar zata nemi wani abu ta rasa idan baya tare da ita.
  Kallonta yake sosai irin kallon da ba zaka iya gane na minene ba, ji yake kamar ya cire maganar dake cikinsa ya maida mata, ina zai samu yan'uwata? Idan ma an samu ya zasu zauna da ita? Idan kuma sun mutu fa anya yan'uwanta za su yarda su rike ta yadda ya dace a yanayin da take ciki yanxu?
Ya kasa dauke idonsa daga gareta kamar a fuskarta zai karanci amsar tambayoyinsa.

Hafsatu manga kam bachinta take hankali kwance fuskarta sai sheki take sam ba zaka tsammaci akwai wata matsala ko damuwa a tattare da ita ba.
Yana kula da duk wani motsi nata ciki har da shiga da fitar numfashinta, motsin da take lokaci zuwa lokaci ya tabbatar masa da bachin ya fara gimtsarta, a wata daya da yan kwanaki data kwashe asibitin tare da shi ya karanci komai nata yanzu ya fahimci abubuwa da dama game da ita, ya san yadda zai yi communication da ita duk kuwa da rashin maganar da take.

Hankalinsa ya kara tattarawa gaba daya ya maida kanta, juyin da take ma burgeshi take domin izuwa yanzu ya dan saba da kiriniyarta ko da kuwa tana bachin ne balle kuma idan tana farke, ta shiga ransa sosai wannan yasa yake kyaleta tana masa yadda take so, da kuma tausayinta da yake hakan yasa yake mata daukar yar cikinsa.

Hannayenta duka biyu ta saka saman idonta tana mitsitsikawa alamar ta farka kenan, zuwa can kuma ta bude idon tana hamma, karkato kanta tai kadan ta kalli gefen da yake, fuskarsa na nan kamar kullum babu dariya kuma babu daure fuska, ma'ana ba yabo ba fallasa.
Tashi yai tsaye ya rikata yana kokarin sauko da ita saman gadon, sai ta bata fuska kamar zata fasa kuka har yau ha taki ta saba da wanki baki da brush saboda gani take kamar shine silar daya saka bata magana tunda kauyensu ba da shi suke wanke ba, gashi ita kullum zafi yake mata idan yana goga mata a hakora. Be kula yadda ta hade rai ba ya nufi bandakin da ita, dan indan sabo a yanzu ya saba da halinta na kin son brush shi kansa yasan dan kawai yana cilasta mata ne.

Da kansa ya zuba mata toothpaste ya wanke mata bakin iya yadda yake jin zai fitarda dattin dake cikin hakoranta, sannan ya fita yaja mata kofar, sai da tai fitsari da alwala sannan ta fito.
Ko da ta fito daga toilet din baya dakin, dan haka ta bude durowar dake gurin ta dauko katon hijab din da ya siyo mata yadi uku ta saka ta shimfida carpet ta soma sallah asuba, bayan ta gama ta kama gadon ta hau ta zauna tana ta bata fuska kamar an mata wani abun sai kokarin hawaye take, ba'a yi minti goma da zamanta ba Zain ya turo kofar dakin ya shigo Phone dinsa makkale a kunne sai amsa wayar yake kadan kadan kamar an masa dole, har ya gama wayar idonsa da hankalinsa na kan hawayen da suke mata tsiyaya. Bayan ya saka wayar aljihu ya zauna ykusa da ita ya zuba mata manyan idanuwansa kamar zai cinyeta.

“Minene?”

Ya tambaya kamar baya son magana.  Bakinta ta wangale masa ta nuna masa halshenta, sam taki ta saba da rashin maganarta lokuta da dama tana ganin abun magana amman ba bakin yi, ita gani take kamar wanin abun ne yai mata wanda yasa maganarta ta dauke.
Kallon halshen yai kamin ya kalli cikin idonta, hannunsa ya kai ya share mata hawayen.

“Ni kaina ban san abunda ya hanaki magana ba Mama, ban san ina matsalar nan take ba”

Ta kara bata fuska tana ta kukanta marar sauti. Dauke kansa yai daga barin kallonta ya maida dubansa gurin wayar dake hannunsa duk da kasancewar hankalinsa gaba daya yana gunta, yana jin kukanta har cikin ransa saboda yasan dalilin kukan kuma ta cancanci tai kukan ko da babbace balle karamar yarinya kamar Hafsatu.
   Sai da tai kukanta iya yadda take jin ya isheta sannan tai shiru dan kanta. Tashi yai tsaye ya hada mata tea ya mika mata, sai taki karba ta kwanta saman gadon ta rumgume hannayenta a kirjinta ta juya masa baya, ita ala dole tayi fushi.
   Gira daya ya daga irin he can't believe it sai ya soma kurba tea yana kallon kofar da akayi knocking. Ya tsammaci daya daga cikin nurses ne ko Doc Hafsat ko kuma abokinsa Ibrahim, but abun mamaki Anty Ummi ce wace ta kwashe sati biyu bata leko asibitin ba, saboda fushin da take da shi.
     Kallon mamaki yake mata da kuma kauna irin ta yan'uwa daman yasan Anty Ummi ba zata iya fushi da shi har na tsawon lokaci bata zo asibitin ta duba Hafsatu ba duk da kasancewar shi yana zuwa gidanta sai dai ba kamar yadda ya saba ba, cikin rashin kuzari dake bayyana damuwar dake fuskarta ta karaso cikin dakin ta aje kulolin dake hannunta daga bisani ta zauna saman kujerar dake gaban gadon Hafsatu Manga m.

“Good morning Anty”

Ya fada yana kallon yanayinta, ta dan kalleshi kadan ba tare da ta amsa ba ta maida dubanta gurin Hafsat da har yanzu bata juyo ba balle tasan wanda ya shigo dakin duk da kasancewar taji motsin shigowar mutum kuma tace ya ambace Anty dan haka tasan Anty Ummi ce duk kuwa da kasancewar ita ma kanta Hafsatu bata cika son Anty Ummi ba.

“Ya mai jikin?”

Sai da ya aje kofin tea dake hannunsa sannan sannan ya amsa.

“Taji sauki”

Hannu Anty Ummi ta kai ta taba kafarta hakan yasa Hafsatu juyowa ta kalleta sai kuma ta kalli Zain.

“Gaisheta”

Zain ya fada, sai ta hade hannayenta guri daya ta gaishe da Anty Ummi kamar yadda ya koya mata. Murmushi Anty Ummi tai tana kallonta cike da burgewa.

“Har tsawon wane lokaci zaka cigaba da aje yarinyar a nan?”

“Har zuwa lokacin da za a samu iyayenta, ko kuma nace zuwa lokacin da bakinta ya bude”

Wani irin kallo Anty Ummi tai masa na rashin fahimta, da kuma jinjina nacinsa.

“Zain kasan abunda kake fada kuwa? Taya iyayenta zasu tararda kai a nan suce sune iyayenta? Ina tsoron abunda zai taba martabar gidanku, dukan abunda ya same ka a yanzu ni za a dorawa laifi saboda yarinyar nan bangarena ta fito...”

Ya tari numfashinta.

“Yarinyar nan bata gane garinsu Anty, taya zan saketa taje ta fada wani hannun na dabam, secondly yanzu yarinyar nan bata iya magana idan wani abun take so wa zai mata”

“Zuciyarka na yaudararka Zain kana dorawa kanka laifin abunda ya samu yarinyar nan, yau kusan wata daya kenan da wani abu baka kwana a gidanku, baka wuni a gidana, ka jingine komai naka hankalinka gaba ya koma gurin yarinyar nan... ”

“Kamar yadda taki zuciyar take yaudararki game da Farhat ko?”

“Farhat abar tausayi ce Zain ko baka gani ba? Yarinyar nan marainiyace kuma yanzu ta rasa yar uwarta, sanadin hakan takoma kauye da zama, sun kuma cilasta mata auren mijin yar'uwarta da wanne zata ji? Ni ce silar komai Zain da ban fadawa yayartaba da har yanzu sirrin yana nan a sirri be fito ba, amman yanzu fa komai ya bace saboda ni... ”

A tsawace take maganar hawayen na sauko mata. Hannayensa yasa aljihu yana kallon Anty Ummi cike da mamaki.

“Wannan yarinyar tafi Farhat zama abar tausayi, saboda bata magana a yanzu, kuma batayi boko ba balle ta iya rubuta abunda take so sai dai tai nuni...”

Ta daki gadon da Hafsatu take zaune.

“Fine ka cigaba da rikonta har karshen rayuwarka, amman karka kuskura ka kusanci gidana da ita kuma dole Mai Martaba yasan da zamanta...”

Tana kaiwa nan ta tashi tsaye ta fice a fusace. Kansa ya daga sama ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kalli Hafsatu, sai a yanzu ya lura da hawaye take, daman a rayuwarta babu abunda ta tsana kamar taga babba yana fada, tana tsoron fada ko da ba da ita ake ba, balle wannan da tasan danta ake yinsa gashi kuma taji an ambaci Mai Martaba duk da bata san shi ba, tasan yadda nasu sarkin yake, dan haka tana tsoron sarakuna sosai.

“Kina son allura?”

Tayi saurin girgiza kai ta saka hannunta ta share hawayenta, dan tasan idan bata share ba zai iya cewa allura zai mata. Zaunawa yai a kujerar da Anty Ummi ta tashi ta bude kulolin ya zuba mata wainar kwai da dankali, ya sake hada mata wani tea ya mika mata.
Chapter 20 · 0% Book details