← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 93

Sashe 66

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fadar hakan ya nufi kofar fita har yanzu hawaye take, amman bata karyaba saboda ta shirya wannan tana ganin lokaci yayi da wasar Hameeda zata kare. Cid police ta fara wuce ta fara wucewa domin duba Hafsatu manga sai ta samu bata nan an kaita gidan yarin yara, daga nan ta wuce gidan yarin kai tsaye amman suka hanata ganinta babu yadda ba tai ba amman suka hana, wai kaifin babbane tun da tayi kisan kai. Sabon dpo ta kira wanda aka kawo bayan dauke Auwal, sai da suka gaisa yake sanar mata cewar an sake dauke shi amman akwai sabon da aka kawo, bata jidadin hakan ba, saboda ta dan soma sabawa da shi sakamakon irin aikin da suke na kare hakkin dan'adam.

Cikin rashin kuzari ta nufi station din, bata sha wahala gurin wuce ba, domin ta fada musu daga kunyar kare hakkin dan 'adam take kuma tana son magana da Dpo ne,sai da aja tambaya mata uzini a gurinsa sannan ya bata damar shiga. Jikinta ne ya kara mutuwa lokacin da tai arba Auwal, ta sanshi kamar yadda shi ma ya santa sanadiyar Farhat da ke hadasu a waya ko kuma ta kawo mata shi har gida ya gaisheta, amman matsala zata iya fin haka dan zai iya saka son kai a ciki. Gurin zama ya nuna mata sai ta zauna jiki a sanyaye.

“Na kira wacan dpo ne sai ya ke fada min an canja shi”

“Eh shekara jiya aka dawo da ni, kin san yanayin aikin na mu, daga nan kuma za a iya kaimu wani garin matata na ma na can ban dauko ta ba”

“Daman na zo ne akan maganar yarinyar da aka kama Hafsatu manga, wacce ake zargi da kisan kai”

Ta fada idonta na cika da hawaye.

“Wacece yarinya ce?”

Ta tambaya da sauri.

“Yarinyar kauye wannan wacce kanene yake rikonta, wacce aka kai maka ita a matsayin mai aiki”

Ya tashi tsaye da sauri.

“Wata kashe?”

“Farhat”

Anty Ummi ta fada hawaye na zuba a idonta sosai. Koma yai ya zauna yana jin maganar tana masa yawo a kai. Wayar Anty Ummi ce tai ringing sai tai saurin dauka ganin number Ibrahim ta kara a kunne.

“Okay tau”

Shine kawai abunda ta fada ta kashe wayar. Sai ta kalli Auwal din ta ce

“Ba ita ta kashe ta ba, bana jin Hafsatu manga zata iya kashe ta ba taya ma za ayi ta iya kasheta ba zata iya ba, tarko ne aka hada ma”

Har ta gama wayar tai wannan maganar Auwal be ce komai ba, idonsa sun kada sun yi mugun ja.

“Farhat... Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un”

Ya furta, sai kuma ya kalli Anty Ummi ya ce

“Kun tabbatar da ta mutu ne?”

“Likitoci sun tabbatar da hakan, yanzu Ibrahim ya fada min wai Zain yasa an kama Hameeda saboda ita yake zargi”

“Ba zan iya miki komai ba a yanzu, idan ballin yarinyar kike son a baki ba zan iya baki ita ba a yanzu, dole ne sai munje koto”

Ya fada yana kokarin maida kwallah da suka cika masa ido.

“Kotun nake son aje, shiyasa nai saurin zuwa nan, saboda na san Dada Yalwa da Mai Martaba zasu iya bukatar a kashe maganar saboda gudun zubewar mutuncin masarautarsu, iyayenta kuma na san zasu iya cewa sun yafe, amman idan kungiyarmu ta shigo ciki, kuma kai tsaye dole gaskiya zata fito kuma dole a gane mai laifi, ina son a wanke Hafsatu manga ne kuma a kama Hameeda ta dandani kudar abunda ta aikata”

“Zamu komai, ba zaki iya ganinta ba, lauyanta ne kawai zai iya ganinta, kuma ba zamu shiga kotu ba doka ce under age ba a shiga kotu da su sai da lauyansu wanda sai yi magana a madadinsu”

“Zamu shirya komai, kungiyarmu zata shigo ciki, na san lauyar da zata tsaya mata kwararriyar lauya ce, goyon bayanka kawai nake bukata dan Allah kar a hada baki da kai a kashe maganar nan”

“Ba zan yi ba, Farhat kamar yar'uwa take a gurina ba jininta ba zai je a banza ba, ba kuma zan zuba ido Hameeda ta ci bulus akan Hafsatu Manga ba, zan yi duk abunda ya dace ina gawarta take?”

“Tana Zainuddeen Special Hospital”

Kai ya daga mata, sai ta tashi ta fice daga office din tana hawaye.

“Da ban yaudareki ba, dan yanzu baki mutu ba, da yanzu kina can gidana cikin kwanciyar hankali, amman ba zan bar wannan ba... ”

Ya fada yana share hawayen da suka zubo masa har cikin ransa yake jin mutuwar Farhat din. Telephone din dake gabansa ya dauka ya kira sai ga wani police ya shigo da sauri yana sare masa, fada yai masa sosai akan rashin sanar da shi kisan kan da basu yi, sai yace takardar ce yake cikewa shiyasa be kawo ba...
[3/22, 2:22 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *Masu karanta min novel basu biyaba da masu sharing Novel dina, Allah ya muku yadda kika min. Idan kina son biya ki turo 300 ta 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, sai ku turo da shaidar biyan ta wannan number 08036126660, ko kuma katin MTN na 300 ta wannan number 08036126660*

47.

Gaba daya masarauta Rishim tai tsit baka jin komai sai zancen kisan kan, a take maganar ta fara leka makota saboda yan aji a kara gaba. Mai Martaba na dakinsa yana sauraren korafin Dada dake kuka tan zayyana masa kama Hameeda da Zain yai, sai ga Hajiya Zarah ta shigo tana sanar masa cewar Farhat ta rasu, tun da ta fada masa maganar ya soke kansa kasa be dago ba har sai da Hajiya Maryam ta shigo ta zube a gabansa.

“Allah ya taimake ka, ya kamata kai wani abu saboda gudun zubewar kima da mutuncin masarautar nan, an kama Hameeda a motar yan sanda, abunda be taba faruwa ga wani dan sarautarta ba yau ya faru a gidan nan, maganar nan fa yada ta za ayi, idan har ba kai wani abun ba, yanzu kuma ga dpo can ya zo ya shiga part din Zain yana bincike, anjima kadan nasan wata maganar ce zata sake tasowa saboda Ummi ba zata kyale ba, dole za atayi abunda zai zubarsa mutuncin masarautar nan daman can ba son mu take ba”

“Shine abunda na gani, na san ai ita ce ta turo Zain din ya kamata saboda bata kaunar Hameeda in ba dan haka ba, mi zai sa Hameeda a cikin lamarin bayan kuma ga wacce tai abun an kama ta dumu dumu”

“Ku bar hukuma tai aikinta, idan kotu suke son zuwa sai a tafi a can za a bayyana mai gaskiya da marar gaskiya, za a sako Hameeda domin Zain be da hurumin rufeta domin ba ita aka gani a gurin ba”

Haka kawai abunda Mai Martaba ya fada. Sai kowa yai shiru, ita dai Dada an biyata tun da ya ce za a sako Hameeda.

Tun daga baki kofa wani dan sandabke daukar hoto har aka isa gurin da jini ya zuba, wato inda aka caka ma Farhat wukar. Anan wani police din ya debi jinin ya zuba a wani gurin, Auwal kuma ya karasa gurin da gorar rubutu da kulli magani suke ya saka safar hannu sannan ya dauka yana dubawa, a cikin wata farar leda aka saka gorar, dayar kuma aka saka kullin magani, haka ya bi cikin gidan ya duba komai ya dauki abubuwan da yake son dauka sannan yasa aka kira Abida yai mata tambaboyi, sannan ya kulle part din gaba daya ya tafi da makullin.

Daga gidan Asibiti suka nufo already an kai Farhat mutuware, da taimakon Doc Ibrahim aka bude musu gawar suka dauki hotonta ya basu wukar suka sakata a cikin wata ledar wacce aka rubutawa evidence, sannan suka fito, mahaifiyar Farhat ce da wasu tsofi biyu suka tare Auwal suna rokon a ba su ita wai su sun yafe.

“Idan kun yafe, govnati ba zata yafe ba, dole ne sai na hukunta mai laifin”

Shine kawai abunda dpo ya fada musu ya wuce ya barsu suna aikin kuka. Anty Ummi ce take bawa Mahaifiyarta hakuri ita tana kuka.

“Ba a baku gawarta amman yanzu kin ga kotu za a shiga, dole ne sai hukunar yan sanda sun yi bincike kamin a rufeta gudun kar a rufeta kuma wani abun ya taso, case yanzu a hannun yan sanda yake”

“Kaddarar rayuwace ta fada mata, daman can ban so auren nan ba, babu yadda ban yi ba akan ta auri mijin yar'uwarta amman ta ki, daman nasan wani abu sai ya faru tun da yayan manya basa daukar talaka da daraja, gashi yanxu sun kashe min ita sun huta”

Ta kara fashewa da kuka, sai kuma ta juyo tana rokon Anty Ummi.

“Na hada ki da girman Allah, ki taimaki ki sa baki a bamu yarinyar nan, saboda ayi mata sutura kamar yadda addinin musulumci ya tanada, wannan abun da kuke kokarin ne kamar kuna wulakanta gawarta ne, na bar banda ya kasheta da Allah lahira Allah yai masa hukunci ranar da komai baya boyuwa”

“Za a baku ita Inshallah amman ba yau ba, ban kuma miki alkawari gobe ba, amman da zarar an gama bincike za a bada gawarta”

Anty Ummi ta fada cikin wani irin kuka. Daga asibitin da taho da su gidanta, da yamma lis wasu yan 'uwanta suka ciko mata suka taho, tun da suka dawo gida Anty Ummi take ta zirga zirgar fadawa abokan aikinta abunda ya faru.
Chapter 66 · 0% Book details