← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 93

Sashe 26

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Thank you so much”

Kai ya gyada mata, sannan ta juya ta fice tana jan kofar.
[2/26, 10:39 AM] Ayusher P: *HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_

Wattpad @KhadeejaCandy

2⃣0⃣

YARIMA ZAIN POV.

Sai da ya gama karyarwa ya bata lokaci sannan ya fito ya shiga motar, dereban Anty  Ummi ya kama hanyar Anka da shi, tafiya kawai suke yana mamakin kansa, but daya tuna saboda Anty Ummi zai yi sai ya kawarda komai a ransa.
  Har suka isa be da natuwar jiki balle ta zuciyata, babu komai a cikin ransa sai tsanar Farhat, yadda zai iya daga ido ya kalleta yake tunani har suka isa garin.
   Kusa da gidan direban ya faka motarsa,  sannan ya fita daga motar ya karasa da kafa kofar gidan yai musu sallama, sai da wani saurayi ya fito ya tambaya wanene direban ya amsa masa.

“Daga Gusau muke, ita ai tasan da zuwanmu”

Saurayin yana komawa cikin gida, sai gashi ya fito da kwanon fura da kuma tabarma. Direban ya karba ya karasa gurin motar ya shimfida, ya budewa Zain motar.

“Ranka ya dade ka fito ga tabarma nan an shimfida”

Wani banzan kallo Zain yai ma tabarma.

“Bata da darajar da zanzo gidansu a shimfida min tabarma na zauna, kaje ce tai sauri ta fito ga mai siyenta ya fito”

“An gama Allah ya taimakeka”

Direban ya juya da sauri ya koma kofar gidan ya sake sallama da ita, yana mamakin furcin Zain. Bude motar Zain yai ya fito ya tsaya kan tabarma da takalminsa. Ba a kara minti biyu ba sai gata ta fito sanye da abaya green color, ta rame sosai kamar ba ita ba. Har ta karaso gurin Zain be kalli inda take ba sai kallon gonakin dake can yamma da su yake. Zuwa tai ta matsa ta rumgume hannayenta tana watsa masa harara kasa kasa.

“Da ace kin min sallama, na nace kin baro wani hali daga tarbiyar gidanku”

Ta kalleshi da kyau zuciyarta na sosuwa da kalaman.

“Ban ga mutane ba, shiyasa ban yi sallama ba”

“Haka ne, daman irinku marasa daraja basa kallonmu a mutane, saboda muna da matsayi na musamman”

“Masara dajara suna a inda suke, mukan matakinmu ya wuce haka, tunda ka baro masarautarku ka baro aikinka ka kawo kanka gurina, ba tare da da fargaba ko tsoron abunda zai faru ba”

Yayi murmushin takaici still be kalleta ba ya ce

“Yana da kyau idan mutum zai siye abu yana da kyau kaje ka dubashi gudun cinikin kifi ruwa, fada min nawa ne farashinki domin ina jin nan da sati daya zan taimaka na siyeki”

“Idan har siyena zaka yi, to abunda masarautarku take da shi, har ma a hada na masarautar kano da zazzau be siye ni ba, sai dai na taimaka na zama ya kamar kowa na yanka maka farashi mai sauki biyan, gudun saka masarautar Rishim a kunya”

“Baiwar masarautar Rishim tafi karfin shiga kunya balle masarautar, ina ji miki tsoron ranar da bakinki zai ja miki a binneki da ranki, idan kin gama kallona ga abun sadaka nan a bayan mota ki shiga gidashi a kurkinku...”

“Na fi karfin na shigar da abu da kai, sai dai a shigarmin dan nima surukar sarki ce a yanzu....”

Tana kawai nan ta juya ta nufi kofar gidansu. Sai a lokacin Zain ya juyo ya kalli bayanta.

“Kama damisa sa'a ne wasa da ita rashin kunya ne....”

Komawa yai cikin motar ya zauna sai direban ya zo da sauri ya shiga gidan direba ya tashi motar.

“Ranka ya dade ba a fitar da kayan da suke bayan motar ba”

Zain be tanka masa ba, shi ma kuma be sake cewa komai ba, yaja motar suka kama hanyar gida.

*** *** ***

Bayan Zain ya wuce Doc ta dawo tare da Hafsatu manga cikin gida, daya daga cikin gowns din ta dauka ta saka mata.

“Wow kin yi kyau Mama kin fito kamar balaraba”

Murmushin jindadi Hafsatu manga tai tana shafa kayan, doc tai dariya tare da tashi tana amsa kiran da Sapna ke mata.

“Ya akayi?”

Sapna ta nuna mata hanyar kitchen tana cin soyayen dankalin turawa.

“Abunda kika dora zai kone”

“Amman shine ba zaki duba min sai kin kirani”

“Ina laifi nama kiraki? Wai ku yan nigeria miyasa ba a muku daidai a rayuwar nan ne?”

“Mtssw”

Hafsat taja tsaki sannan ta nufi kitchen. Dariya Sapna tai mata tana kallon Momy data fito daga dakinta.

“Momy ina kwana?”

“Lafiya kalau yau ba zaki aiki ba?”

“Sai na gama karyawa, kin san Abbah yace na daina zuwa da yunwa”

“Hakan yana da kyau, daga nan sai a koreki ai”

“Muke da gwannati ai waya isa ya koremu?”

“Abun wani ai be taba zama naka ba, dan haka ba Alhaji Salis ne akan milkin ba, kanensa ya kamata ki san wannan”

“Whatever ni dai nasan ina da alaka mai karfi da wani be isa ya koreni akan aikina ba”

Momy ta tabe baki, kamin ta dauke kanta ta maida gurin tv. Doc ce ta fito rike da plate tana kwalama Hafsatu manga kira, da gudu ta fito.

“Wow yarinya kin yi kyau kamar na sace ki”

Sapna ta fada tana kallon yadda kalar rigar ta karbi fatar jikinta. Kallon rashin yadda Hafsatu manga tai mata jin tace ta sace ta.

“Ungo zauna ki ci bari na hado miki tea”

Hannu biyu tasa ta karbi plate din. Suna haka Auwal ya shigo sanye da kayansa na yan sanda hullar na rike a hannun. Wata uwar kara Hafsatu manga ta saki tare da sakin plate din dake hannunta ta nufi Doc Hafsat da sauri ta kankameta tana wani irin numfashi kamar zata shide.

“Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un”

Cewar Momy tana kallon Hafsatu manga kamar yadda duk suke kallonta.

“Minene Mama minene?”

Doc Hafsat ta tambaya. Bata iya amsawa sai kuka take ta rufe idonta gam, Sapna ta nuna Auwal.

“Maybe uniform dinsa take tsoro kin san ba kowa ke son police ba”

“Yan sanda kike tsoro?”

Ta gyada kai da sauri jikinta sai rawa yake kamar mazari.

“I told you”

Cewar Sapna tana daga kafadunta sama, Auwal ya kallin uniform din yana murmushi.

“Yanzu fa Mamata cewa tai na yi kyau, amman ina zuwa nan yarinya ta rika ihu kamar taga dodo?”

“Miye marabinka da dodon? Ni dai dan Allah ka fita karka haukatata”

Dariya yai ya juya ya fice. Babu irin lallabar da ba a mata ba amman taki yin shiru, haka Doc ta jata ta kaita dakinta ta kwanta ba dan tayi shirun ba sai dan ta gaji da rarrashinta.
Ita kuma ta koma falo ta karya sannan ta dawo ta shirya ta wuce office.
Around uku na yamma ta dawo daga aikin, ko da ta shigo Momy kawai ta samu a gidan, Sapna da Auwal duk suna gurin aiki. A gajiye ta shiga falon ta zauna saman kujera na wani dan lokaci sannan ta tashi ta shiga bedroom dinta. Can karshen gado ta hango Hafsatu manga na zaune har lokacin tana kuka idonta duk ya kumbura ga shi ko abincin safe bata ci ba, domin dazu kin kula komai tai. Zaunawa bakin gado Doc tai tana fadin

“Wannan wace iri rayuwa ce haka Hafsa? Dan sanda kika gani a gabanki ko me? Tun kamin na fita babu kalar rarrashin da ban miki ba amman kin ki hakura, dubi yadda idonki ya kumbura kamar wacce aka yi ma wani abu haba dai... ”

Wayarta ta fiddo ta dannawa Zain kira, sai da tai ta ringing kamar zata katse sannan ya dauka.

“Hello Doc barka da wuni, Yarinyar nan ce tun dazu take kuka har yanzu taki ta daina”

“Me aka mata?”

“Ba'a mata komai ba, kawai saboda taga Auwal da uniform din police, tun safe take kuka har yanzu”

“Gani nan zuwa”

Ya katse kiran. Ita kuma ta kara matsawa kusa da Hafsatu manga tana mika mata hannu.

“Zo nan dansanda bazai miki komai ba”

Lake kafada Hafsatu manga tai alamar ba zata zo ba, har Doc ta gaji ta tashi dan canja tufafin dake jikinta.
Cikin yan mintuna Zain ya iso gidan, ita kanta Doc tayi mamakin saurinsa sai kace wanda yake kusa da unguwar, text ya aika mata cewar gashi harabar gidan. Sai ta dauki Hijab dinta ta saka.

“Zo muje ga Doc Zain can yazo”

Sai a lokacin Hafsatu ta sauko daga kan gadon ta rika hannunta suka fita tare. Waige waige kawai take kamar ance mata dan sanda bullowa zaiyi ta wani wajen, daga cikin motar Zain ke kallonta har suka karaso, bude mata gidan gaba yai ta shiga tana ta shasshekar kuka.

“Daman kuna da yan sanda gidanku?”

Ya tambaya yana kallon yadda idon manga suka kumbura.

“Ee Dsp Auwal Salis yayana ne”

Jimmm Zain yai kamar mai tunani, ba zai ce be san dsp ba saboda yawan nunashi da ake a labarai idan wani abun ya faru, sai dai be taba sanin familynsu daya da Hafsat ba sai yau, impact be ma dauka dan garin nan ne ba.

“Rufe mana motar”

Haka kawai ya fada, ba musu ta matsa baya ta rufe masa ganbun motar, shi kuma yai ribas ya fice daga gidan, sai da ya kama hanya sannan ya kalli inda Manga take.

“Mama fada min sun miki wani abun?”

Ta girgirza kai.

“Dan sanda kawai kike tsoro?”

Ta daga kai.

“Shikenan daga yau ba zaki sake ganinsa ba, zan kaiki gurin Anty Ummi kina so ko?”

Ta lake kafada alamar bata yarda ba, sai sabbin hawaye take, yanzu kam hankalinta ya fara komawa gida.

“Fine kina son chocolate na siya miki?”

Ta daga kai.

“Share hawayenki”

Tasa hannu ta share. Hanyar da zata kaishi Jafatu ya kama zuciyarsa cike da tunani kala kala. A harabar gurin ya faka motarsa sannan ya bude mata ganbun motar

“Ki tsaya nan bari na siyo miki na dawo”
Chapter 26 · 0% Book details