Sashe 61
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ta bude idonta sakamakon kira sallah ta taji na asuba, ji tai kamar mutum a bayanta tana dubawa ta ga hannnunta cikin na Zain, sai tai saurin ture masa hannu ta tashi zaune. Hannu ta kai ta kunna bedside lamp sannan ta sauke kafafunta kasa. Sauka yai saman gado ya nufi inda makunnin wutar yake na dakin ya kunna. Sannan ya juyo ya kalleta.
“Ya jikinki?”
Uffan bata ce masa ba, sai ta tashi cikin rashi kuzuri ta shiga bathroom. Shi kuma ya juya ya fice daga dakin.
Cikin karfi hali tai alwala ta fito tai sallah, sannan ta sake komawa saman gadon ta kwanta, bata farka ba sai takwas da rabi na safe, sai da ta shiga bandaki ta wanke bakinta da fuskarta sannan ta fito ta saka Hijab dinta ta sauko downstairs. Kofar fita ta nufa tana jin motsin Zain a kitchen tare da Hafsatu manga tana masa fira, har Part din Dada Yalwa taje ta gaisheta sannan ta dawo part din a lokacin Zain yana zaune saman dinning Hafsatu Manga kuma na zauna kasa tana karyawa.
“Je ki ce Anty Farhat ina kwana”
Zain ya fada yana mata Farhat wacce ta nufi upstairs. Sai ta lake kafada ita ba zata ba.
“Je mana”
“Uh aa”
Ta sake lake kafadar tana aikin auna abinci a baki. Dauke kansa yai daga barin kallonta ya maida kan wayarsa dake kara alamar sako. Sunan Hameeda ne shimfide a jikin sakon, sai dai yai kamar zai goge sai kuma ya bude.
_Akwai yiyuwar ina da ciki fa, ka yi wani abu kamin komai ya bayyana ni kadai bani tabbas akwai ko baba, amman idan har ya girma kaine a cikin matsala, domin zan yi amfani da wadannan hotunan na matsayin shaidar kan min fyade da gaske, kaga babu ta inda zaka iya wanke kanka, kuma san dole a yarda da ni._
Yana gama karanta sakon ya aje wayar, ya dauki abincin Farhat ya nufi dakinta, kwance ya sameta tana ta hawaye. Sai yanyo karamin tebur ya dora mata abincin a kai, sannan ya zauna kusa da ita.
“Wai Minene na wannan kukan ne? Wani abun nake miki wanda baya miki dadi ko me?”
“Bana jindadin zaman gidan ni kadai”
Yayi shiru kamin ya ce
“I can invite your friends here, ko kuma yan 'uwanki”
“Amman Dada ba zata bari ba, na san bata so na ko gaisheta nai bata amsa min da kyau”
“Ni kike aure ba Dada ba, zaki iya farincikin matukar hakan ne abunda kike so, Dada Yalwa Hameeda kawai take son na aura shiyasa ba zata taba maraba da duk wata mace da na aura ba, kuma ina tunanin Anty Ummi ta fada miki haka”
Ta tashi zaune ta share hawayenta.
“Da gaske zan iya kiran kawaye a nan”
“Na taba miki karya?”
Ya fada yana kallonta fuskarsa ba yabo ba fallasa. Har ya tashi tsaye sai kuma ya dawo ya zauna ya fuskanceta.
“About this girl, karki daga hankalinki dan Allah, you know marainiyar ce bata da kowa a yanzu sai mu, ba san yadda zaki kalli abun ba, amman Hameeda ce ta shirya komai....”
A nan ya kwashe abunda ya faru ya fada mata, ciki har da zancen abunda ya faru tsakaninsa da Hameeda.
Ta rufe baki
“So ka kusanci Hameeda kenan?”
Ya kalleta
“Im not sure, amman idan har na yi miyasa zaisa na kusance ki, na yi iya kokarin da zan yi na hana kaina zuwa gareki amman na kasa, hutunna data bani basu isa su zama shaida ba, zai iya yiyuwa ta kwanta ne a jikina kawai ta dauka ko kuma ta yi wani abun da zai sa ta a dauki hoto kamar ina kusantar ne, amman ina jin kamar na aikata”
Ta sauko da kafafunta kasa tana fuskantarsa.
“Amman Zain indai Hameeda zata iya aikata wannan, zamanta a tare da mu hadari ne domin zata iya unkurin kasheka wata rana”
Ya kalleta.
“Idan ta kasheni zaki ji wani abu?”
Bata ce komai ba sai kallon kwayar idonsa take can kuma ta sauke idonta.
“Maybe”
Yayi murmushi tare da kamo hannunta ya rike.
“Idan har ni zata kashe abu ne mai sauki, as long as ba zata cutar wandanda suke kusa da ni ba, like you as my wife, Anty Ummi as my sister, And Mama...”
Sai kuma yai shiru.
“Ban san matsayin a gareni ba yanzu, zata iya haduwa da iyayenta anjima ko gobe, but i promise myself this i will try my possible best to take good care of her ko da tana gurin iyayenta ne, ban san yadda zaki dauki maganar ba, but ina jin Mama kamar yar da na haifa da cikina ina sonta sosai”
Ya yi shiru sai kuma ya kara matse hannunta cikin nasa.
“I know kina kallona as wicked person, na san ban kyauta abunda nai miki ba from first place, amman ke kika bani damar hakan kin sani ko?”
“Amman ai baka taba ganina da wani namijin ba, balle ka min shaidar iskanci”
“Ido abunda yake gani yake iya yanke hukunci da shi, yanayin shigar da kike ba zata taba burge namiji mai mutumci ba, idan kuma dan iska ne idan ya ganki zai yi zaton ke ma haka kike. Yanzu na yarda ba ko wace mai shigar banza ba ce yar iska, wasu nayi ne just for fashion, and I'm sorry for that”
Ya kai hannunsa saitin fuskarta.
“It's very difficult for me na zauna da wata macen a matsayin matar aure, halayentar fuskarta yanayin mu'amalarta ba daya ba ne da naki, ba zan taba nadamar fadawa kowa ina son Haleema ba, saboda macece mai tsananin biyayya da gudun zuciyata, duk abunda ta san yana faranta min tana kokarin aikatawa, idan kuma na ce bana so ba zata sake yi ba, wannan ne dalilin daya kara min son a zuciyata, amman duk da haka ina kokarin ganin na zauna dake na baki hakkinki yadda ya kamata, kina karkashina a yanzu komai naki yana kaina, na yarda da hadin da Allah yai tsakanina da ke shiyasa na watsar komai....”
Ya saketa ya tashi tsaye.
“Amman zama da ni akwai wahala Zain”
Juyowa ya kalleta.
“Zan jure har zuwa lokacin da zaki fahimci minene aure, maybe a lokacin kin shirya zama da ni as your Husband, ki shirya jibi zamu je ki gai mahaifiyarki kuma ki yi mata bankwana na tafiya”
“Gaskiya ni ba zan sake rakaka sha'anin wannan yarinyar kauyen ba”
Ta fada tana dan turo baki.
“Ni ne zan rakaki India a duba lafiyarki, and Mama zata bi mu”
Yana fadar hakan ya fice daga dakin. Hannu ta kai ta dauki mug din dake cike da tea ta kai bakinta tana ta tunanin maganganunsa. Sai gata cikin wani kurbi a zuciyarta dake dauke da tusayinsa...
Ko da ya sauko ya samu Hafsatu Manga ta gama cin abinci tana jera soyayen dankwalin turawa a dinning. Tana ganinsa sai tasa dariya. Zuwa yai ya tsaya a gurin fuskarsa da murmushi.
“Me kike?”
“Na gama cin abinci na cinye hadda naka, kaga na jera mutane”
Ta shiga fada nasa.
“Wannan Inna Ladi wannan Zat, wannan Mamana, wannan Yarima Hamma, nan ma wane gari ne? Can kuma ina ne?”
“Gusau, can kuma Nijar”
Ya fada yana zama kan kujerar dinning, sai ya dauketa ya dorata saman kafafunsa.
“Kina son Hamman nan ko Mama?”
“Shima yana zuba min abinci kuma idan za dakeni yana hanawa, shine ya siyeni a gurin mutanen nan”
“Ba kince iyayenki ba ne?”
“Aa wannan dan sanda yace idan na fadi gaskiya sai ya dakeni sosai sai ya halbeni shiyasa ban fada ba”
“Amman Anty Ummi ina tace a kaiki?”
“Nima ban sani ba, wani gurin kawai wannan mutumen ya kaini kuma yana ta min fada har da wani abu ya bani ina sha nai ta bachi, ya kaini gurin wata mata tasa aka min allura wai nai sauri na girma, sai suka kaini gurin wannan matar mai bakin rai sai ta min tsawa wai tashi ki yi shara”
Ya kwatantata yadda Zainab ke mata Matar Auwal..
“Shi kuma sai yana tayani aikin, sai a daukoni aka bada ni gurin yan sanda suka zo da ni suka kaini gurin wani dan sanda da wata mata suka ce nace wadannan sune iyayena kuma ba sune ba, suka tafi dani can kauye had cikina yana ciwo suka rika sani ina bin wasu suna kiwon shanu, sai kuma suka saida ni ga Yarima Hamma...”
Tun da ta fara bata tsaya ba, sai da ta kai aya. Shi kuma yai murmushi yana nazartar bayananta daya bayan daya. Sannan ya shafa kanta ya sauke ta ya tashi tsaye.
“Bari naje nai wanka kema sai kiyi ko?”
“Fita zamu yi?”
“Yes zan kaiki gurin Anty Ummi ta ganki da idonta”
“Aa ni bana sonta, ita da wacan matar”
Ta fada tana nuna dakin da Farhat take.
“Ba can zan baroki ba, tare zamu dawo kin yarda?”
“Ee”
“Good”
“Minene gaud din?”
Yayi murmushi ba tare daya fada mata ma'anarsa ba.
HAMEEDA POV.
Sun dade suna tattaunar maganar Kuyangar da Zain ya ce ambashi ita da Dada Yalwa, sai dai bata yarda ta nuna ma Dada cewar ta san wani abu a kai ba, Dada kuma tana ta mamakin zuwan nasa ne, ko da yake ta ji uzurinsa gurin Mai Martaba.
“Yarinyar ta mallake shi mal, da ada ne ba zai iya tafiya ba tare daya fada min ba, amman yanzu Mai Martaba kawai ya fadawa gudun karya hana shi tafiya”
“Uhm ai daga gani ba banza ta shigo gidan nan ba”
Hameeda ta fada bayan ta turawa Zain sako. Sannan ta tashi tare da kofin shayinta da dawo part dinsu ta shige dinta, gurin window taje ta tsaya tana kallon harabar Part din Zain, so take ta ga fitowarsa akwai maganar da take son ta fada masa ta yadda zai tabbatar da gaskene tana kan bakanta. Ta kusan awa daya tsaye bata ga fitowarsa ba, sai ta dawo ta zauna tana kiranshi a wayarta, sai ta ta gaji da jera masa missed calls sannan ya daga wayar ba tare da yace da ita komai ba.
“Ka dauka da wasa nake ko? Na baka sati biyu ka yi wani abu a kai, ko kuma na fito na fallasa sirrin gaba daya”