← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 93

Sashe 22

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duniya ta juya mata baya, rayuwa ta zo mata ta inda bata tsammaceta ba, komai ya canja mata daya bayan daya ita kanta a yanzu bata iya gane halin da take ciki.
    Sosai take jin kewar Anty Rukaiya da yayanta, wata daya kenan amman kullum jin take kamar jiya ta rasu, wani lokacin jin take kamar kanta empty ne saboda damuwa da tunanin dake ciki.
Kowa ganin laifinta yake saboda ta ki amincewa da auren Ya Bashir, wanda a ganinta be ma dace ayi mata wannan maganar ba, taya zata iya rayuwa a gidan da yar'uwata ta rayu? Idan kuma ta zauna a nan anya zata iya rayuwa kuwa?
Tun baya mutuwar Anty Rukaiya,Farhat ta dawo Anka local government da zama sai rayuwa tai mata kunci, kullum cikin kuka take na rashin yar'uwarta, a dayan bangaren kuma ta kan rasa wane tunani zata fara yi akan cin amanar da Auwal yai mata ko kuma Ya Bashir da yan'uwanta suke son ta aura? Kowa ya kasa fahimtarta ciki har da Mahaifiyarta.

Juyi take tayi saman gadon karfi mai rumfa irin na da din nan, kamar yadda ta sabawa kanta da wuni a daki kullum. Jin motsin shigowar mahaifiyarta yasa tai hanzarin tashi zaune ta share hawayenta.

“Amman dai kin ji kunya Aisha, Wallahi baki min adalci ba kuma baki yi ma kanki ba, kin tabbata butulu kuma dan kaza mai ci ya goge baki”

Dagowa tai ta kalli Inna idonta cike da hawaye.

“Inna taya zan rayu da mijin yar'uwarta? Taya zan aurin mijin da Anty Rukaiya ta aura? Ba kusan abunda bake ji ba, Wallahi zan iya kashe kaina idan na aureshi Inna”

Inna ta jinjina kai tana hade hannayenta.

“Lallai kuwa Aisha it bata ji zafin daukarki ta kaiki makaranta ba ta wayar da ke ki goge sai yanzu ke zaki ji kyamar auren mijinta da rike mata yayanta ko? Wato kin ci jar miya kin waye, kin bani mamai Aisha ba irin wannan tarbiyar nai miki ba, kuma ban tsammaci irin wannan sakamakon daga gareki, hakika da Rukaiya tana da rai data gwammace bata rika ki a gurinta ba”

Fashewa tai da kuka mai tsanani, sai ina ta hau ta da masifa.

“Ni ba kuka nace ki min ba munafuka, tashi kije dakin amo ga bakuwa can tana jiranki”

Daga haka Inna ta fice, Farhat kuma ta kwanta a gurin tana ta kukanta kamar bata ji abunda Inna tace mata ba, bayan dan lokacin sai ga Anty Ummi ta shigo dakin da sallama. Amman kukan da Farhat take ya hana ta amsa mata, cikin tashin hankali Anty Ummi ta zauna bakin gadon kusa da ita ta rumgumota tana tambayar dalilin kukan nata.

_________________________________________

Kun tuna waye Auwal kuwa?

Anya Zain zai yarda Hafsatu ta zauna a gidansu Doc Hafsat kanwar Auwal?

Da gaske Ya Bashir zai iya runtse ido ya auri Farhat?

Ya Zain zai yi da Anty Ummi, mi zai biyo baya?

Me Hameeda take shiryawa?

Shin Farhat zata iya yima Anty Rukaiya halacci ta auri mijinta domin kawai ta rike mata yayanta?
[2/19, 9:48 PM] خديجة أبو بكر القلوي😍: *HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_

Wattpad @KhadeejaCandy

1⃣8⃣

Dawowa tai ta zauna tana cigaba da masa kallon mamaki.

“Amman miyasa?”

“Saboda ke Anty, yau idan naje gida zan sanar da Dada da Mai Martaba cewar akwai wacce nake so”

Hannayenta biyu ta daga sama tana yi ma Allah godiya. Shi kuma ya tashi ya fice zuwa gurin motarsa, idan ya tuna saboda Anty Ummi zai yi sai yaji kuzari da son yin haka, ta dayan bangaren kuma yana tunanin irin zamantakewar da zasu yi. Daga Gada biyu zuwa kan wurin sarki tafiyar awa daya yai har da wani abu, saboda yanayin driving din da yake, yana faka motarsa kansa yai mugun sarawa har cikin zuciyarsa, cikin rashin kuzari ya fito daga motar ya nufi part dinsa.
Saman cushion ya zauna ya lumshe idonsa yana maida numfashi a hankali.

“Saboda ke ne kawai”

Ya fada yana bude idonsa. Sai kuma ya tashi ya shiga bedroom dinsa, kayan jikinsa ya cire ya bude drawer ya dauki tawul ya daura ya shiga bathroom, yana shiga ya raba jikinsa da tawul din ya kunna shower yai tsaye ruwan na dukan kansa, sai kuma ya juya ya jingina hannayensa jikin tile din ya rufe idonsa.
Ya samu kusan minti talati a haka, sai da yaji kiran sallah la'asar a masallacin dake cikin fadar sannan yai wanka ya fito a gagauce ya shirya ya fita domin baya son ya rasa jam'i. Bayan ya sauke farilla ne ya shiga part din Dada dan ci abinci duk kuwa a kasancewar an kai masa nasa a part dinsa.
A falo ya sameta zaune daya daga cikin bayin gidan tana matsa mata kafafunta, dayar kuma tana bare mata ayaba.
Yana shigowa dakin duk suka sanda kansu kasa domin su kansu sun san kallo na daya daga cikin abunda Yarima Zain ya tsana, kusa hada baki su kai gurin gaisheshi muryarsu har rawa take, ba azabtar da su yake ba, amman yana musu kwarjin da ko motsi yai sai sunji kamar numfashinsu zai dauke. A kujerar dake facing dinta ya zauna yana gaishe fuskarsa cike da annashuwa kamar da gaske farincikin ne har cikin ransa.

“Dada sannu da gida”

“Wannan farincikin na minene? Da har tasa kai mana dawowar rana a yau?”

Ya fadada fuskarsa da murmushi.

“Na wani albishir ne mai girma wanda kuka dade kuna jira, ke kawo min abinci”

Ya karasa yana kallon mai bare mata ayabar. Jiki na rawa ta tashi ta nufi inda dinning din Dada yake, Dada kuma tai dariyar daya bayyana hakoranta biyu na maka tace

“Labarta min naji, indai mai dadin ji ne kana da babba goro...”

Dagowa yai har zai yi magana sai Abida ta shigo fuskarta cike da damuwa sai da ta fara zubewa kasa ta gaishe da Zain sannan ta fadi gaban Dada ta kwashi gaisuwa, sai kuma ta zauna gaban Dada fuskarta kamar zata fasa kuka.

“Akwai wata magana ne...”

Dada ta tambaya tana kallon yanayinta. Murzar hannunta take kamin ta soma magana kamar da tsoro.

“Allah ya taimakeki, Gimbiya Hameeda tana daki tun jiya bata fito ba, ta kuma min gargadi da kar na kuskura na shiga dakinta har sai ta bukaci hakan”

“Bata da lafiya ne?”

Dada ta tambaya cike da kulawa.

“Allah ya kara miki nisan kwana, nima ban sani ba”

“Jeko bude dakin”

“Ta hanene ranki ya dade idan har na bude zata iya min mugun wulakanci...”

Tashi Zain yai ya fice daga falon, kai tsaye part din sisters dinsa ya nufa wanda a cikin dakunan ne Hameeda take da nata. Yana isa ya tura kofar dakinta ya shiga.
Tsaye yai cak sakamakon arba da idanuwansa suka yi da kayan mayen dake saman gadon Hameeda, ita kuma tana gefe daya ta makure guri daya ta hana ta sharar bachinta. Kallon kayan maye kawai yake yana mamakin inda ta samo su, yaushe ta fara shaye-shaye?
Karasawa yai kusa da gadon ya dauki kwalbar yana dubawa, fuskarsa cike da damuwa da kuma mamaki. Kara matsawa yai ya kai hannunsa yana tashinta, firgigit ta bude ido ta tashi zaune tana kallonsa idonta a juye kwalli duk ya bata ido ya dararo har saman kumatunta.
Zuwa can kuma ta zabura tana kokarin rufe bakinta, hakan ya tabbatar masa da cewar sai a yanzu ta gane shi kenan.

“Waya baki wannan?”

Tai shiru sai rabon ido take kamar munafuka.

“Answer me....!”

Tsawar daya daka mata ne yasa tai saurin sauka daga kan gadon ta koma can gefe, sai kuma ta nufo kofar ta kulle.

“Doc.. Doc... Ne... Ya bani.. Shi.. ”

Ta fada muryarta na gargada, ido Zain ya kura masa yana karantar gaskiyarta, ita kuma ta kasa daga kai ta kalleshi, sai wani munafukin numfashi take dan kawai ya jita.

“I and Doc Hashim ne kawai Mai Martaba ya yarda su duba iyalansa? Shi ya rubuta miki wannan? I will call him”

Yana juyawa, sai tai saurin faduwa kasa ta rike masa kafa tana kuka.

“Dan Allah karka kira shi, ka rufa min asiri karka fadawa kowa”

“Waya baki? Yaushe kika fara shaye-shaye?”

Dago kanta tai ta kalleshi.

“Ni na siya, bana samun bachi ne shine ya iya ina sha dan na riga bachi”

“Mi kika rasa da har zai sa ki rika shayeshaye? Kin san halin da Dada zata shiga idan taji wannan labarin? Mai kike tunani zai faru idan na sanar da Mai Martaba?”

Tashi tai tsaye ta nufin gurin window ta tana hawaye.

“Na rasa komai, da fari Mahaifiyata ,mahaifina, sai kuma yayata, daman tuntuni na dade da rasaka, ba ni da wanda zai saurareni ya bani shawara akan wasu abubuwan, ba ni da kowa na rasa kowa, ada kana saurarena kana bani shawara akan wasu abubuwan ina maka kallon dan'uwa kuma abokin fira, yayata ma tana nan tana fada min gaskiya, amman bana gani sai a yanzu dana rasata nake gani nayi rashin da ba zan taba maye gurbinsa ba har a bada,

Ba zan taba yafewa kaina ba, na musgunawa Haleema, tayi ta bani shawara amman ban dauka ba, yanzu na rasa ta na rasa kowa, Dada ba komai take fahimta ba, na koma ni kadai ba ni da kowa...”

Ta zube masa tana wani irin kuka mai taba zuciyata tare da zubewa kasa ta rike lalulayen window da karfin gaske. Zain ya hade yawun dake bakinsa zuciyarsa na sosuwa da kalamanta.

“Ki tattara duk wani abun maye nan ki dora saman gadon nan, otherwise na fadawa Mai Martaba... Lastly wash your face ki zo falo Dada na nemanki”

Yana kawai nan ya juya ya fice. Part din Dada ya dawo ya zauna inda a gurin daya zauna dazu.

“Lafiya take?”

“Kanta ke dan ciwo sai kuma jiri, amman zata fito yanzu”

Ya fada yana misalta irin yanayin da Dada zata shiga idan har taji Hameeda tana shaye-shaye.

“Bari naje na dubata”

Tana kokarin tashi tsaye sai yai saurin dakatarda ita.

“No Dada gata nan fitowa”

Sai kuma ya kalli Abida.

“Abida akwai abu a kan gadon Hameeda jeki kwashe min komai kisa a leda ki kai min dakina”

“An gama ranka ya dade”
Chapter 22 · 0% Book details