← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 93

Sashe 4

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Sunana Anty Ummi, nan gidana ne ina da yara hudu amman duk sun tafi makaranta”

Ta karasa tana nuna mata gidan. Ta zaro ido waje.

“Kai gidan yankan kai?”

“Aa bama yankan Kai Allah ya tsare mu waya ce miki gidan yankan kai ne?”

Tai Shiru tana ta kallon Zain, sai Anty Ummi ta nuna shi.

“Wannan ne ya fada miki?”

Ta gyada kai, alamar ee. Zain ya kara kallonta da mamaki, ita kuma ta wani daure fuska kamar da gaske shi yace mata haka.

“Daga ina kike?”

“Daga gidanmu”

“Ina ne gidanku?”

“Can garinmu”

“Ina ne garinku?”

“Kufawa?”

Ta juyo ta kalli Zain.

“Kasan garin?”

“Aa shekaranjiya dai naji Mai Martaba yana maganar an kai musu hari...”

Tayi karaf ta karbe.

“Ee hari aka kai mana gayu suka kai mana hari da bindiga”

“Su waye gayu?”

“Barayi”

Ya fadi kadan kadan dan kar aji, daga nan sai abun ya koma labari, kamar ba ita ce take kuka ba.

“Idan aka ce musu barayi kashe mutum suke, da suka zo garinmu suna ta kashe mutane, sun kashe kakana da Baban abulle kuma ban san inda Inna larai take ba, ni kuma na gudu ina ta gudu har na hadu da mai mota ya kawo ni nan garin ya bani naira dari kuma darin ta fadi kuma yanxu yunwa nake ki kuma jiya ruwa duk akaina ya kare”

Anty Ummi ta kalli Zain.

“Yarinyar nan bata da hankali”

Ta fada kadan kadan, ashe yarinya taji sai kawai ta fashe da kuka.

“Wallahi ni ba mahaukaciya ba ce”

Anty Ummi tai saurin daga mata hannu.

“Tau ya isa, yanzu ki kwantar da hankalinki zan kira yan sanda na sanar da su saboda.... ”

“Dan Allah karki kira yan sanda ni tsoronku nake Wallahi”

Ta kara fashewa da kuka.

Zain ya raso ya matso kusa da ita.

“Kwantar da hankalinki, ba wani abun yan sanda zasu miki kawai za a sanar ne saboda tsaro”

“Aa ni bana so”

“Okay yanzu fada min miye sunanki?”

“Sunana Hafsat Hafsatu manga”

Daga Zain har Anty Ummi jikinsu sanyi yai jin sunan mahaifiyarsu.

“Allah sarki...”

Cewar Anty Ummi. Zain ya mika mata Hannu.

“Sunana Zainudden amman ana kirana Uncle Zain wannan yayata ce”

Ya nuna Anty Ummi. Sai ta saki baki.

“Ko dai matarka ce?”

“Aa yayata ce, baki ga mun yi kama ba”

Ta kalli Anty Ummi ta kalleshi.

“Ee zaka bani abinci na ci”

“Eh mana zo muje ciki gida”

Ya mika mata hannunshi. Sai ta lake kafada.

“Aa ka taba min No-no”

“Wallahi ba zan tana miki Nono ba, ba zan miki komai ba kinji na rantse”

Ya fada da sauri. Har Anty Ummi na dariya. Ta dade tana kallon hannunshi kamin ta mika masa nata wani irin sanyi yaji a hannunta yasan wannan baya rasa nasaba da sanyin da ta sha jiya, ya rikota suka fita.
A rayuwar Zain yana son yara fiye da kima, balle wannan da yaji ta da sunan mahaifiyarsa, ta kwanta masa sosai. Anty Ummi ce a gaba shi da ita suna baya, tasa duka hannayenta biyu ta rike hannunsa daya tana tafiya tana dingishi.

“Miya samu kafanki”

“Nima ban sani ba yanzu dai naji hana min ciwo”

Ta amsa tana ta lekon gidan.

“Ka rantse ba zaka min komai ba”

Ya tsaya yana kallonta, ita dago kai tana kallonshi.

“Idan baki yarda da ni ba, kiyi tafiyarki sai Anty Ummi ta kira miki yan sanda sai su kama ki”

Tai saurin girgirza kai.

“Aa na yarda da kai”

A tare suka shiga mai gadi ya bude masa sai kallonta yake. Anty Ummi ta tsaya tana masa bayani.

“Lallai tabbas naji an kai hari garin nan, dan garin bashi da nesa da damu a kauyen gindawa ne, dake karamar hukumar maru, I an ce an kashe mutane sosai Allah sarki nima na ganta jiya amman sai ta gudu”

“Ashe dai da gaske ne”

Cewar Anty Ummi tana kallon Hafsat cike da tausayawa. Hannunta Zain yaja suka karasa ciki bakin kofar falo ta tsaya tana kallon falon.

“Ni dai tsoro nake ji... ”

Ta fada kamar zata fashe da kuka. Risinawa yai ya rika duka hannayenta ya saka idonshi cikin nata.

“Mama ba zan miki komai ba, ba kuma zan bari kowa ya cutar da ke ba, kin ga idan kika zauna can bbu kowa kuma akwai maciji zai iya cutar da ke”

“Ai bana tsoron maciji...”

Ta fada tana hade girar dama da hagu, murmushi yai ya dan ja mata kunne kadan.

“Karya kike”

Ta kyalekyale da dariya kamar ta saba da shi.

“Amman ke daga ganinki baki jin magana ko?”

“Haka nan ake cewa a garinmu amman ni nasan ina jin magana, kuma suna cewa ba ni da hankali a wai dan sun ga mamana mahaukaciya ce”

Ta fada a shagwabe tana son yin kuka.

“Aa kina da hankali mana, ina mamanki take”

“Nima ban san inda take ba tayi hauka ta gudu, ta bar ni nan, maman bata da hankali, ita ta saka min wannan munduwar”

Ta nuna masa abun hannun dake sanye a hannunta mai sunanta. A hankali ya taba munduwar hannunta cike da tausayinta.

“Zo muje ki ci abinci”

Anty Ummi ta fisge hannunta daga rikon da yai mata. Mikewa yai tsaye ya bi bayansu sai ya sameta falo tsaye tana ta kallon falon. Abinci Anty Ummi ta zuba mata ta kawo a plate ta mika mata.

“Karki ce amman bari na kawo miki brush ki wanke bakinki kin ji?”

“Zan iya ci ko ban wanke bakin ba”

Tayi saurin zaunawa ta saka hannu a ciki ta fara ci, Zain ne yai saurin rike mata hannu sai Anty Ummi ta shiga dakin yara ta dauko mata sabon brush da toothpaste ta zuba mata ta mika mata tare da nuna mata bandakin dake falon.

“Wannan ki wanke bakinki ga ban daki can”

“Tau”

Ta nufi inda aka nuna mata da sauri tana dingishi. Tana shiga bathroom din ta tsaya tana kallon abubuwan da suke gurin daya bayan daya take tabawa har tana gogawa suna kara. Tsalle tai ta leka kanta a mirro ganin bata cin masa yasa ta dauki bokitin ta kife ta taka akai tai tsaye tana kallon kanta. Yatsanta tasa ta taba toothpaste din ta lasa, tana jin zaki sai ta lashe duka, ta dauki shaving cream ta zuba a yatsanta ta goga a hakora, sai ta sauko saman bokitin ta fito daga bandakin.

“Na wanke bakin amman ban ga ruwa ba”

“To da me kika wanke?”

“Wanda kika zuba min naji yana da zaki sai na shanye na zuba wani fari na wanke da shi, amman ban kuskure bakina ba”

Tana karasa fadar hakan ta kai hannunta ta fara cin abincin. Daga Anty Ummi har Zain kallon junansu suke.

Suna haka Farhat ta fado falon ba ko sallama, wani wawan kallo Zain ya watsa mata sai tai tsaye inda take tana kallon Anty Ummi.

“Anty Rukaiya bata nan kuma...”

Sai tai shiru bata karasa ba, Anty Ummi ta san me take nufi tunda tasan komai.

“Shiga ciki”

Ta wuce dakin da sauri har tana kokarin faduwa.

“Idan nace miki yarinyar nan bata da hankali sai ki karyata ni ji yadda ta shigo ba dankwali kuma da kayan bachi, haka ta fito tun daga gidansu har nan”

“Ina ruwanka da ita ko jiya ta fada min kayi kokarin kadeta, ba ruwanka da ita baka san damuwar da take ciki ba”

Ya tabe baki tare da mai da kallonsa gun Hafsat take kallon Anty Ummi.

“Mama ci abinci kinji bari na zo”

Anty Ummi ta fada ganin yadda ta bar cin abinci ta sako mata ido.

“Ni ba mama ne sunana ba Hafsat”

Tana fadar hakan ta maida hankalinta gun cin abincinta. Anty Ummi ta ce

“Na sani saboda kina da sunan Mamana nake ce miki ba zan iya fadar sunanki ba”

Bedroom Anty Ummi ta nufa gurin Farhat.
[2/19, 9:46 PM] خديجة أبو بكر القلوي😍: *HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_

Wattpad @KhadeejaCandy

3⃣

YARIMA ZAIN POV.
A hankali ya kai dayan hannunsa ya cire tsadadden agogon dake hannunsa ya bude drawer ya dauko box din agogon ya saka shi ciki ya mayar, sai kuma yai tsaye a gurin kamar wanda aka dasa a gurin, baya iya tantance yanayin da yake ciki a yanzu shi dai yasan ba farinciki yake ba, kuma ba bakinciki yake ba, indan sabo ya saba da kakkausar lafazi daga bakin Anty Ummi dan haka ko kadan kalaman basu sashi damuwa ba, duk kuwa da kasancewar basu masa dadi ba.

Amman yana jin kamar akwai abunda yake damunsa, yawun bakinsa ya hade ya nufi tagar dake bude yana kallon mutane da ke gudu suna fakewa daga ruwan saman daya fara sauka, hannayensa ya zuba cikin aljihu yana sauke ajiyar zuciya.
Haleema ce ta fado masa a rai, irin rayuwar da suke da zamantakewar aurensu yake tunawa, hakika ta nuna masa so kamar yadda yake nuna mata, bata taba musa masa akan wani abun ba ko da kuwa shine mai laifi, ta kanyi kokarin ganin ta gusar masa da duk wani bacin rai, ko da wasa bata taba daukaka muryarta akan tasa ba, idan yana gida kullum tana manne da shi.

“Ya Rabbi... ”

Ya furta yana busarda iskar bakinsa. Mafita yake nema mafitar da ba zai taba samu ba har abada!

‘Taya zai rayu da wata maccen wacce ba Haleema ba? Taya zai sabu da ita?’
Chapter 4 · 0% Book details