Sashe 57
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
“Ee amman sai an fara bani wayar”
“Ba matsala zai baki”
“Na amince”
“Allah ya miki albarka”
One word Anty Ummi bata kara ba ta kashe wayar.
“Me zaki yi da waya?”
Ta shareshi tana tsaye a gurin har ya bude ledar ya fiddo kayan dake ciki.
“Ba tambayarki nake ba?”
“Wace yarinya ce za aje daukowa?”
Ya dago kai ya kalleta
“Ba a maida min tambaya da tambaya”
Ta dauke idonta daga kallon da yake mata ta juya ta nufi bandaki. Sai a yanzu ya lura da tafiyar da take.
“Kina jin ciwo ne har yanzu?”
Daf da zata shiga bathroom din ya furta nata haka. Sai ta juyo ta tsaka matsa tsawa.
“Ban sani ba”
Taso yai da sauri ya doso inda take fuskarsa a hade....
[3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *Masu karanta min novel basu biyaba da masu sharing Novel dina, Allah ya muku yadda kika min. Idan kina son biya ki turo 300 ta 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, sai ku turo da shaidar biyan ta wannan number 08036126660, ko kuma katin MTN na 300 ta wannan number 08036126660*
41
Wunin ranar a part din Dada ta wuni, duk yadda Dada ta so ta kaita asibiti sai ta ki, ta ci kuka sosai kamar ba gobe.
Tayi tunanin Zain zai tausaya mata ne, ga mamakinta sai ya tsallaketa yai tafiyarsa ga shi har dare yayi be sake lekowa ya ce ya jikinta ba. Duk irin tambayar da Dada Yalwa tai mata akan ta fada mata abunda suka tattauna da Zain lokacin da ta bar musu dakin Sai Hameeda tace babu komai, daga karshe ta taso ta baro mata dakin ta dawo dakinta.
Bakin gado ta zauna tana kallon kofar bandakinta.
“Wato duk irin hali da kalamin da nai masa be saduda ba ko? Bazarana ta ba zata yi aiki ba idan har banyi da gasken ba”
A fili tau maganar sai kuma wata zuciyar ta jefa mata tambaya.
‘Anya baki yi gaggawa ba? Ai ya kamata ki bashi lokaci dazun fa aka yi haka, ai sai ki dan bashi lokaci kiga idan be yi komai ba tukuna’
“Kai Zain ne fa, abu na be cika daukarsa serious ba, yanzu na san zuwa zai yi ya fadawa Ummi wata kila ma su dauki matakin da zai wargasa nawa shirin?”
Ta furta sai kuma ta tashi tsaye ta nufi karshen gadonta tana ta magana da kanta.
“Zai iya zuwa ya dawo da yarinyar nan fa, amman ko da ya dawo da ita ai ba zai ga mutanen ba, balle su tona min asiri, nima ba zan yi sakacin da asirina zai tonu ba, amman nasan matukar ya dauko yarinyar asirina zai iya tunuwa domin zata iya nuna ni, amman ba lallai ne kowa ya yarda ba, idan kuma Zain yai wasa nuna tonan min asiri a cikin masarautar nan sai na tona nasa”
Ta juyo.
“Be kamata na dorawa Abida sata a yanzu ba, duk ta ta tona min asiri akwai aikin daya kamata ta min, yarda ce kawai ba zan sake yi da ita ba, idan ta san wata ai bata san wata ba”
Ta nufi inda wayarta take ta dauka, missed calls ta tarar ciki har da na Fauziya da kuma na wata bakuwar number, contacts dinta ta shiga ta nemo wata number yan nijar da aka rubutawa Fulani mai +227 ta danna mata kira. Tayi mamakin da waya bata shiga har yanzu, rabon da tai waya da su tun lokacin da suka fada mata cewar sun siyarda Hafsatu manga a masarautar Damagaram. Komawa tai ga number Fauziya ta kira bugu daya ta daga.
“Kawata ga hotunan an wanko, na yi ta kiran wayarki baki daga ba”
“Bana kusa ina dakin Dada”
A nan ta kwashe labarin abunda ya faru ta fadawa kawarta.
“Kin san ni abunda na fi tunani? Ina ganin wannan bakar Yayar tasa ta shiga tsakaninku ne, saboda bata son ki ina ganin ta masa asirine ta dauke hankalinsa daga gareki shiyasa komai kika masa baya taba son ki”
“Ina tunanin haka, amman kuma ni miyasa idan nai masa asirin baya kama shi?”
“Wata kila har yanzu bamu dace da wanda zai kama shi din bane, amman kin fada masa Ikram da ni mun ganshi?”
“Ee na fada masa, amman kamar be damu ba”
“Anjima zan zo ma kawo miki hotunan ki nuna masa dan ya san da gaske muke”
“Hakan za ayi, amman yanzu ina son ki fara tuntubar matar nan da ta hada ki da su ko Allah zai sa a samu layinsu ko kuma wani line da suke amfanin da shi”
“Wallahi ko jiya na yi waya da ita tace itama bata samun layinsu a yanzu, amman ki kwantar da hankalinki babu yadda zai samesu domin su tuni suka bar garin, ko da yaje sai dai ya tararda yarinyar, kuma kin ga ita bata san inda zata zata samosu ba, dan haka babu wata hujja ta tona miki asiri”
“Amman yarinyar idan ta ganni zata iya shaidani ai”
“Ko ta shaideki Zain ne kawai zata fadawa shi kuma ya san komai, be kuma san inda zai same iyayen ba, abu na biyu bana jin zai kawo ta cikin fadar nan ma, ba ma lallaine yaje daukota ba tun da be san ta wace Siga zata shigo Masarautarku ba”
“Haka ne, ina jiran hotunan zan ga abunda iya yi”
Daga haka a kashe wayar ta nufi bandaki.
ZAIN POV.
Mai Martaba ya juyo ya kalleshi yana karantar abunda ke shimfide a fuskarsa.
“Me zaka je yi a Damagaram?”
“Lokacin da ina neman Farhat, na yi mata alkawarin idan na aureta zan dauke ta muje garin saboda wani kanen mahaifinta dake can, tun shekaranjiya take min maganar ni kuma bana son tafiya sai da amincewarka”
Mai Martaba yayi murmushi.
“Ka kyauta, na san kai ka matsayin da zaka iya tafiya duk kasar da kake so ba tare da ka tambaye ni ba, amman hakan da kake yana kara min sonka kuma ina jin na yi dacen da, duk da kasancewar kai kadai Allah ya bani namiji be sa ka lalace ce kamar sauran wasu yayanba, Allah ya maka albarka”
“Amin Mai Martaba na gode sosai, ina jin ba zan wuce kwana biyu ba, shine nake rokon idan da hali Mai Martaba yai min alfarmar kiran sarkin Damagaram ya sanar masa zuwa na, ina ganin kamar yafi kyau da kuma kyautuwa na sauka a masarautar”
“Ba dole ne, sai masarautar ta san da zuwanka ko saukarka ba, zaka iya shiga ka fito ba tare da sarkin ya sani ba”
“Na san da wannan, amman ina ganin kamar zan fi jindadi idan na sauka a masarautar, ko ba komai matata zata samu kyakkyawar kulawa kamin mu dawo”
“Mu da bama son a san da aurenka akan me zaka sauka masarautar, kuma tare da matarka”
Zain yayi shiru na wani dan lokaci kamin ya ce.
“Mai Martaba ina son matata, matata ba gurguwa bace ba musaka ba, tana kyau da duk wanda ya kalleta sai ya yaba da kyauta, kun yi mata suturar da zata iya shiga ko ina ta nuna kanta, bayayyiya ce kuma yar boko, talaucin gidan ne kawai matsalarta, kuna tsoron ace danku ya auro yar takalawa, bayan kuma talaucin da arzikin duk daya ne a gurin Allah, miye laifina dan na nunawa duniya matata? Yafi kyautuwa aji kunya kamin aure ba yan anyi ba, a gafarce idan maganganuna sun yi tsauri”
Yanayin yadda yake maganar ne ya karantar da Mai Martaba cewar Zain be jindadin yadda suke masa akan matarsa.
“Abunda baka gane ba, Masarautar Rishim masarautace mai kima da kwarjini, masarautace da babu irinta a fadin kasar nan, auren zumunci, kuma yayan fulani, ko yayan sarakuna abune da aka san masarautar nan da shi tun kaka da kakanni, kwatsan sai kuma aji kayi watsi da wadannan al'adun ka auro wata bare can dabam ba yar sarauta ba kuma ba tsatsonmu ba”
“Irin wadannan abubuwan sun fi tasiri a zamanin baya Mai Martaba, ban taba fadawa kowa ba, amman nasan labarin auren nan ba iya familynmu kawai ya tsaya ba, idan aka boye lamarin yayan da zan haifa da ita suka taso ba zasu so ayi musu wani kallon ba, nima kuma ba zan so a kirasu da wani sunan ba, idan har aka aiyanta Farhat ina jin kamar ni aka yi ma, idan kuma aka min kai an taba masarautar nan ne, na kuma san Mai Martaba ba zai jure ana kiran jikokinsa da wani suna ko kuma ayi musu wani kallo wanda be kamata ba”
“Lallai sarakuwarmu ta samu zama a zuciyar Yarima, yau shi da kansa yake mata kanfe”
Zain yayi murmushin daya bayyana fararen hakoransa, yana mai jin nauyin maganar da Mai Martaba yai duk da murmushin dake kan fuskarsa.
“A dawo lafiya, Masarautar Rishim zata sanarda zuwan Yarima da gimbiyarsa a gurin Sarkin Damagaram”
Zain ya daga masa hannu cike da jindadi.
“Godiya nake Mai Martaba Allah kara maka lafiya”
Cike da farinciki ya baro part din Mai Martaba ya nufo part dinsa, ba dan komai ya zabi sauka masarautar ba sai dan ya samu damar yin bincikensa hankalinsa kwance, ko da wani abun ya biyo baya ba zai bashi matsala ba tunda Mai Martaba ya san da zuwansa Masarauta.