← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 93

Sashe 88

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwananta uku a asibitin suka sallameta, sosai Abbah ya so ta zauna tare da su a gidansa na abuja ta kara samun sauki sannan ta koma gidan Hajiya Asma'u amman Momy ta hana tana ganin kamar Yayarta zata ga ba a mata daidai ba, zata ga kamar sun raina kulawar da take bata ne. Ga Raheem da ke ta kai kawo tun da aka kawota asibitin Momy ta lura da rawar kansa, already ta san manufarsa tun da Hajiya Asma'u ta taba mata maganar. Sai dai har a sallamota ko gaisuwar kirki bata shiga tsakaninsu da Hafsat ba, tana kula MB sosai amman bata kula Raheem saboda ya nuna yana sonta.

A gidan aka dawo da ita, sai kukan shagwaba take yi ma Momy. A gidansu da ke Abuja suka kara kwana sannan wuce Kaduna. On her first day a gidan bayan an sallameta daga asibitin, tana zaune dakinta ita kadai feeling so boring. Beauty ta kirata.

“Dear kina gida ko?”

“Ee”

“Ki shirya gani nan zuwa, zan ki rakani wani gurin”

“Okay but bana jin karfi sosai maybe ba zan iya tafiya mai nisa ba”

“Karki damu ba nesa zanje da ke ba”

Daga haka ta aje wayar tana tunanin ina zasu kaita kuma. Daman sun saba haka idan dayansu yana cikin damuwa sun kan fita da shi dan rage kewa da yin walwala, sai dai nata is different tun ciwo ne. Like by force taje tai wanka ta shirya cikin godon riga domin gown, abaya suna cikin tufafin da tafi kauna kuma ta fi jindadin sakawa. Shiru shiru basu zo ba har aka kira sallah azahar, ganin hakan yasa ta fito falo daman can ba son fitar take ba. Sai kuma fitowar ma tai mata babu dadin ganin Raheem zaune. Tana zaunawa sai ya tattara dukanin hankalinsa ya mika gurinta kamar wanda aka cewa wani abun zata ce masa, kallonta yake sosai yana ayyana irin dadin da zaiji idan yau ta aminta da shi ta so shi kamar yadda yake sonta. Tana da kyau sosai irin kyaun nan mai daukar hankalin maza ga dan karamin bakinta da manyan idanuwa, when she smile her right side dimple will appear abunda yake kara mata kyau a duk lokacin da tai dariya, she's so slim just the way da yake son matarsa ta takasance.
Jikinta ne ya bata yana nan yana kallonta kamar yadda ya saba, har ta unkura zata tashi sai ga Beauty ta turo kofar falon ta shigo fuskarta da murmushi.

“Assalamu Alaikum”

Ita kadai ta amsa mata, yayinda Raheem ya jingina fa kujera kamar be ga shigowarta ba.

“Dear let go”

“Yanzu? I tot ma kin fasa”

“Ya za'ayi na fasa kin ga duka suna can suna jirana fa, daga ni sai ke ne babu”

“Ina ne zamu je?”

“Yafa veil dinki za ki gani ai”

A tare suka shiga dakin, Beauty na rike da hannunta ta dauko mayafin ta sake janyota suka fita dan taga jikinta da sanya. A bakin kofa ta tsaya tana kallon Beauty.

“Ban fadawa Hajiya ba, kuma bata son ina fita bam fada mata ba”

“Fine kirata a waya yanzu, tell her za ki raka ni wani gurin yanzu mu dawo”

A gurin ta kira Hajiya Asma'u a waya ta fada mata sannan taje ta shiga motar, ta window dake bude ta hango yadda Raheem ke kallonsa abunda ya kara bata mata rai dan ta tsanai yadda yake tsareta da kallo.
Beauty ce ke driving, while ita kuma tana front seat. Bata wani gurin da bata sani va Beauty ta nufa da ita, kamar ta tambaya sai kuma tambayar tai mata wahala haka ta zuba hanya ido har suka karaso gaban wata katafariyar Hotel, wacce bata taba zuwa ba, sai dai tana jin labarinta.

“Beauty me za mu yi a nan?”

“You know ba mu saba zuwa hotel ba sai da wani dalili, so ya kamata mu zaga cikin wannan mu bawa idonmu abinci, muna ta jin labarin hotel din nan yau dai na ce musu ya kamata mu zo”

“Amman ba irin wannan lokacin ya dace ba beauty, bana cikin yanayin da zan sake sosai a yanzu”

“Kar wannan ya dameki”

“Amman idan wani ya gamsu fa”

“To miye a ciki? Ba fa rooms kawai ke cikin hotel din nan ba, akwai guraren da yawa, like garden restaurant, suya spot and many more, ke dai fita muje”

Ba dan ta so ba, ta fita daga cikin motar suka nufi wani bangare na hotel din, kama shiga ciki zaka rantse da Allah dare ne domin babu inda hasken rana yake shigowa sai dai na lantarki, da sanyin ac. Jere suke suna tafiya Beauty na mata hirar Hotel din, tafiya suka yi mai dan nisa, tun tana jurewa har ta soma jin gajiya, wani gurin suka iso mai kamar garden sai dai ba shi da fadi sosai and akwai irinsa kusan guda ashiri a gurin, she has no idea yadda akai saman yai hudu kamar dare bayan kuma ta san rana ce suka baro a can waje. A wanda suka nufa an kawata shi da blue wuta and flowers, kyallin da ke jikin fulawar sai blinking yake. Saman gurin an kawata shi da taurarin da zaka rantse da Allah na gaske ne. Yar dogowar hanya ce da zata sada su da inda suka nufa an kawata hanyar da kyandir.
Sai ta rike Beauty tana dan jin tsoro dan babu hansken wuta sai na kyandir.

“Beauty kin san inda kika kawo mu kuma”

“Na sani mana, ke dai biyoni kawai”

Beauty ta fada tana yar dariya, she trust her friend ta san ba zata cutar da ita ba, hakan yasa ta bita amman ba dan hankalinta ya kwanta ba. Lokacin da suka isa gurin sai kamshi turaren da take sakawa da sanyin ac ya fara musu marhabun. Wani kyakkyawan dinning table ne mai zanen heart a gurin da kujera biyu, tsakiyar table din an dora kyandir mai zanen heart, kasan gurin kuma an zagaye ko ina da kyandir din, and duk abunda yake gurin was decorated in red color. Flowers da ke gurin tana da tsawo sosai ta tare su basa ganin kowa kamar yadda kowa baya ganinsu.

“Beauty I'm scared, kin ce min sauran suna nan amman ban ga kowa ba, and why all this?”

“You shouldn't be, zauna a nan bari na je na kira su”

Ta rika ta zaunar zaman kujerar da ke facing din kofar shigowa gurin.

“Ko dai muje tare”

“No ki zauna yanzu zan duba su, bari ma na kira su, aro min wayarki tawa ba kati”

Ya mika mata wayar hankalinta ya dauko da tsoron da take ji a gurin dan haka bata kawowa ranta tunanin taya za'ace wayar Beauty babu cati ba. Tana kallon Beauty ta tafi da sunan kiran Pearl, ita dai tana ta mamakin kawo su irin gurin nan bayan they are not lovers, and gurin ma ya tsorata, dan tasan halin friends dinta zasu iya tsoratata da sunan sakata farinciki. Shiru shiru bata dawo ba yasa ta fara counting in ta kai goma bata dawo ba zata bita, so she decided to close her eyes kar ta ga wani abun marar kyau.

“1...2...3...4...5...”

After courting ten ta bude idonta, abunda ta gani ta dauka tsarawa take kamar yadda take yi idan tana tunanin Zain, tafowa take inda take da wani irin taku na kasaita da burgewa. Tana ta kallonaa har ya karaso sai tai murmushi ta runtse idonta tana murza su.

“I'm such fool”

After seconds ta bude, and he was still there wearing a beautiful smile. Saurin tashi tai tsaye baki sake ta kai hannu ta taba fuskarsa. Ta ji alamar mutum ta taba but bat yarda shi din ne ba.

“Maybe I'm blind har na fara ganin mutane da fuskarsa”

Ta fada with emotional tears in her eyes.

“No you're not PureHeart”

Maganar da yai ta maimaita kanta sau ba adadi a kwalwalarwa kamin ta sadata da tunaninta har ta maye ilahirin jikinta. His sound, his face, his smile, his everything was there near her. Jikinta ne ya fara rawa hawaye na sauko mata, sai ya kara matsowa ya rika hannunta ya dora saitin zuciyarsa.

“Feel it”

Wani irin bugawa zuciyarsa take kamar yadda take tata, a lokaci daya suke sauke numfashi da dauka, just like their hearts da suke bugawa a tare.

“I feel it”

Ta fada in a cool way, with her very calm voice. Sai ta fashe da kuka tasa dayan hannunta ta rufe bakinta ta rumtse ido gam...
[4/10, 9:45 AM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *61*

Jin tai kamar kafafunta ba zasu dauketa ta saboda rawar da suke, and her right hand was still on his chest har yanzu bugun zuciyarsa take ji. Ganin zata fadi din yasa yai saurin rikota ya zaunar da ita har lokacin idonta a rufe suke. Hannunsa ya kai ya rika tafin hannunta, wani irin sanyi suka ji tare da wani irin abu mai kamar shocking a lokaci daya. Tai saurin bude idonsa sai ta sauke su cikin nasa, sai kwalla ta biyo baya, shi ma kallonta yake ido cikin ido, wani boyayen sako idanuwansa suke aikawa nata idanuwan, daga inda yake zaune yana jin bugun zuciyarta yayinda ita kuma take ganin motsawar kirjinsa.

“You... You... ”

Magana take so tai amman ta kasa muryarta sai tawa take da alamar akwai kuka a tare da ita.

“Ba za ki iya magana ba, har sai wannan kukan ya fita daga cikinki, so let's cry”

Sai kawai ta fashe da kuka tana ta kuka yana kallonta zuciyarsa na sosuwa da hawayen da ke zuba daga idonta. Handkerchief ya ciro a alijihunsa ya mika mata, sai ta karba ta share hawayenta.

“Zain...”

Ta kira sunansa, sai ya katseta tare da dora hannunsa saman bakinsa.

“Shiiiiiiiiii”

Sai ta lumshe ido. Tashi yai daga inda yake zaune ya zaga ta bayan kujerarta ya dora hannayensa saman kan kujerar ya risino da bakinsa daidai kunnenta.

“Zat za ki ce”

Bude idon tai tana murmushi da hawaye at the same time.

“I hate you i hate you so much”

“I know”

Ta mike tsaye sai ta juyo ta kalleshi. Zata yi magana ya rigata.

“Tell me one good reason da yasa kike boye kan ki a gareni?”

Kai ta girgiza.
Chapter 88 · 0% Book details