← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 93

Sashe 71

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Idan kina son mu fitar da ke daga nan gurin dole ne sai kin ba mu hadin kai, ki fada mana komai yadda ya faru karki ji tsoro ko fargaba”

“Ba ni ba ce wannan matar ce”

Da kadan kadan Hassana take mata tambaboyi tana bata amsarsu har ta gama yi mata duk tambayar da zata mata, sannan ta kalli mutumen da suka zo tare da shi ta ce

“Doctor Bismillah”

Safar hannu likitan ya saka ya dauko wani karamin almakashi da yar roba ya nufo inda Hafsatu manga take.

“Me za ku mata?”

Zain ya tambaya a tsawace.

“Gashin kanta zamu kira ina son ayi mata gwaji ne?”

“Gwajin me?”

“DNA TEST”

Anty Ummi ta bashi amsa.

“Why?”

“Ta nan kadai zamu iya tabbatarwa da gaske Abbah mahaifinta ne ko kuma a a? Ta yadda kowa zai samu gamsuwa, ni, shi, Anty Ummi, kai, da kuma Hafsat din gab daya”

Zain ya dauke kansa daga barin kallon Hassana ya kalli mutumen dake tsaye a gurin daya je tarbon Hafsatu manga kamar an dasashi.

“Miye alakarki da wacan mutumen?”

“Mahaifina ne, kuma mahaifin Hafsat”

Zain be sake cewa komai ba, har likitan ya kiri gashin kanta. Sannan ya ce

“Ibrahim zai yi gwajin shi ma likita ne”

Har Anty Ummi ta bude baki zata yi magana sai Alhaji Habib ya rigata.

“Ba shi ya yi”

Sai likitan ya mikawa Ibrahim robar da ya zuba gashin, sannan ya je ya sake deban gashin Alhaji Habib ya saka a cikin wani kwankwan ya mika masa, ya cire fice yana kokarin cire hand gloves din da ke hannunsa. Lokacin da za a maida Hafsatu manga tayi kukan tana ta kiran sunan Zat.

Cikin bacin rai duk suka fito ba ma kamar Zain da idanuwansa suka gama rinewa suka kai ja sosai. A mota daya Zain ya shigo da Anty Ummi, Alhaji Habib kuma yana cikin tashi motar tare da direbansa suka kama hanyar Family house din su Anty Ummi. Ita kuma ta dawo gidan Anty tare da Zain yayinda Barr Hasana ta nufi gidansu Zain dan yi wani binceken, Ibrahim kuma ya wuce asibitin.

Da suka shigo gida ne Anty Ummi take masa bayanin komai ciki har da zancen Mahaifin Hafsat da yadda Rufaida ta bar gidan, kuma yadda aka yi case din ya dawo hannun Hassana yar'uwata saboda sun san Husaina ba zata yi abun kirki ba tun da ta zabi mahaifiyarta, kuma cigiyar Rufaida da Alhaji Habib ya bada a gidanje redio da tv, bayan kuma yasa a abincika masa a gidan mahaukata da asibitoci.

“Ya fada min wai kannenta za su zo gobe suna son ganin Mama, kuma suna son au bincika mahaifiyarta da kansu”

Zain yayi shiru yana nazari kamin ya kalli Anty Ummi ya ce.

“Idan ta tabbata haka ne, ya za kiji da tsanar da kika nunawa yarinyar nan”

Ta kawar da fuskarta dake hawaye sai ta dauko masa wani zancen.

“Auwal ya fada min, gobe za a bada gawar Farhat, iyayenta za su zo gobe maybe ba za su yarda a yi mata sallah nan ba”

Zain ya yi sauri Mikewa tsaye yana hade wani abu daya tsaya masa a wuya.
[3/26, 6:28 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 50.

Anty Ummi ta tashi tsaye tana kallonsa.

“Zain ina zaka je?”

“Ban sani ba, maybe gida zan koma amman ina jin kamar bana son zama a ko'ina”

Ya fada hawaye na saukowa daga idonsa.

“Dan Allah ka kwantar da hankalinka,kuma ya yarda da wannan kadarar”

“Da ban yarda da wannan kaddararba, da Allah kadai yasan halin da zan shiga, kwanciyar hankali kan babu shi a tare da ni har abada, ba ni natsuwar ruhi balle kuma ta jiki, tunani ma ban san wanne zan yi ba, i lost Haleema three years ago, and now na rasa Farhat, i was just thinking of what would happen next”

“Hameeda will go to jail akan abunda ta aikata babu abunda zai kara faruwa inshallah gaskiya zata fito komai zai bayyana”

“Even if she go to jail bana tunanin damuwa ta zata wanke, domin na rasa su har abada ba zasu taba dawowa ba”

“Ba zasu dawo ba, amman Allah zai iya musanya maka da mafi alheri, baka san abunda Allah ya tsara maka a gaba ba”

Ya hade hawun bakinsa tare da saka hannu ya share hawayensa.

“Bari naje gida ina bukatar hutu”

“Ka zauna nan har zuwa dare, maybe zai kawo mana results din da wuri, maybe kuma sai gobe”

Komawa yai ya zauna ya jingina kansada kujerar ya rumtse ido. Kitchen Anty Ummi ta shiga ta hada masa tea ta kawo masa, sai a karba ya aje be sha ba, ita kuma ta koma kitchen din ta dafa masa pepper soup, ta kawo masa har lokacin be sha tea ba. Karamin tebur ta janyo ta dora masa plate din tana kallonsa.

“Ba za ka ci ba? Haba Zain damuwarka fa tana damuna, bayan wuya sai dadi idan ka yi hakuri komai zai wuce kamar ba ayi ba”

“Haka ne, amman ba zan iya cin pepper soup din nan ba”

Ya fada yana daidaita zamansa.

“Ko kadan? Ba zan jidadi ba idan baka ci ba”

“Dazu na tsammaci zaki je wa Mama da wani abun dadi, kin san ba abun dadi za su bata ba, and ta yi spending three days there she miss us kuma ya kamata mu kai mata wani abun dadi ko?”

“Mantawa nai ban yi hakan ba, amman next time zan yi mata i promise”

Ya kai hannu ya dauki plate din tare da spoon yana juya pepper soup din, sai yai murmushi.

“Tana ta kirana tana ganin kamar zan iya yi mata wani abun? But I'm helpless”

“You're not helpless ko yanzu zamu yi duk abunda za mu iya a tsaya mata”

Ya gyara kai, ita kuma ta tashi ta nufi dayar kujerar inda wayarta ke ringing. Ganin number Auwal yasa tai saurin dauka ta kara a kunne tana amsa gaisuwar da yake mata.

“Lafiya Kalau Al-hamdulillah”

“Mashallah, daman na kiraki ne na sanar miki cewar Mun samu wata kwarriyar lauya mai zaman kanta zata tsayawa Farhat”

“Kamar ya zata tsaya ma Farhat? Ban gane ba”

“Ita zata shigarda da karar a madadina, ta fada min iyayenta suna da rauni kuma za a iya cin amana a cikin shari'ar”

“Mu zamu ci amanar ko kuma wasu?”

“Ban sani ba, amman dai hakan da zata yi yana da kyau domin za a kwatowa Farhat hakkinta, Hameeda zata iya komai na ganin ta fitar da kanta, ku kuma abunda kuke kokari ku fitar da Hafsat daga ciki, so na sanar miki ne kawai dan ki sani”

“To yayi kyau Allah ya taimaka, amman wacece?”

“Sunanta Barrister Husaina Habib Alhasan”

“To ya yi kyau Allah ya ba mu sa'a”

Daga haka ta aje wayar ta kalli Zain.

“Kaji wani murdadden lamari, wai yar'uwar wannan lauyar zata tsayawa Farhat”

Ya mata kallon rashin fahimta. Sai ta cigaba

“Twins sis dinta ce fa wacce akakarbe case din daga hannunta aka bawa Hassana, abunda na gama fada maka dazun kenan, so take kar Mama ta fito saboda kar wani abu ya samu mahaifiyarsu”

“Amman ba hadin kai bane kuwa? Idan har ta tabbata Mama yar wannan mutumen ce kin ga ai kanwarsu ce ko?”

“Yes amman ita Husaina tana kokarin kare mahaifiyarta ne, saboda bokan ya fada musu duk lokacin da Rufaida ta dawo abun zai koma kanta, ita kuma Hassana tana ganin laifin mahaifiyarta ne shiyasa ta tsaya kai ta fata tana son ta wanke Mama saboda ta farantawa Mahaifinsu”

Zain be kara cewa komai ba, farfesun ma kadan ya sha. Da yamma lis Ibrahim ya kawo masa gwajin DNA din. Daya karba sai ya kasa budewa yana gudun ganin sakamakon ba tare da wani dalili ba. Sai kawai ya aje takardar yana tambayar Ibrahim.

“Ya zo daya”

“Kama yai ka bude ka gani”

“Ganin ba shi amfani, just tell me”

Ya mike tsaye ya nufi gurin plasma ya tsaya ba dan xai yi komai ba, sai dan kuma baya son jin abunda Ibrahim din zai fada masa, Ibrahim ya kai hannu ya dauki takardar yana kiran Anty Ummi wacce ke ta dawainiya da yara da suka dawo daga makaranta yanzu.

“Anty Ummi ki zo ga result din”

A take ta baro dakin yaran ta fito falo ta karba gabanta na dan faduwa.

“Ai na dauka sai gobe”

“No ai daman gwaji ya danganta da kayan aikin da asibiti take da su, balle kuma asibitin kin san ta mu ce”

“Allahu Akbar, Allah mai yadda ya so a sadda ya so, jinina ce Zain ashe Mama jinina ce Wallahi mahaifinta ne”

Anty Ummi ta fada idonta cike da kwalla tana nufar inda Zain yake tsaye da takarda, shi kuma ya kasa juyowa ya kalleta balle kuma ya sake ce mata wani abu. Tsaya tai tana kallon bayan kansa tana auna yadda yake ji a zuciyarsa.

“Na san baka farinciki sabo...”

Sai yai saurin juyowa ya kalleta.

“No you're wrong, na fi kowa farinciki, and i will be the first one da zai mata wannan albishir din”

Yana kaiwa nan ya zagaya gefenta ya wuce. Sai Ibrahim ya tashi ya rufa masa.

Dukan wani bincike da ya kamata Hassana tai sai da tai sannan ta baro fadar, a hanya Dpo Auwal ya kirata ya sanar mata cewar an samu lauyar da zata tsayawa Farhat, batai mamakin jin Husaina ba, daman tun ta tsammaci haka saboda ganin ba ta jidadin yadda aka karbe case din a hannunta ba, kuma ta fada mata zata yi duk abunda ya dace na ganin Hafsat bata fito ba, so wannan ba abun mamaki ba ne dan ta saka kanta akan case din. Tana gama waya da da Dpo ta kira Husaina bugu daya ta dauka.

“Yar'uwarta”

“Husaina abunda kike yi ba shi da kyau, akam me zaki karbi case din mu tsaya a gaban kotu akan mutun daya? Bayan kuma kin san gaskiyar komai”

“Sanin gaskiya ba damuwata ba ce, mahaifiyata na ke karewa, ni kina ba ni mamaki wlh ke Yanzu kin fi son Yarinyar ta fito ita mahaifiyarmu wani abun ya sameta? Wace irin Ƴa ce ke?”

“Mahaifiyar yarinyar aka ce ba ita ba”
Chapter 71 · 0% Book details