← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 93

Sashe 86

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Zain na i know you have done a lot akan Hafsat, ta shaku da kai kusan ko da yaushe labarinka take, na san kai ma ka shaku da ita, amman Zain Hafsat karamar yarinya ce batai girman da zaka bata irin wannan kulawarba, idan har soyayya ta shige a yanzu da take karamar yarinya ba mu san me gaba zata haifar ba, ina son yata t samu ingantacciyar rayuwa mai kyau, kulawar da bata samu a gurinmu da iyayenta ba, a yanzu ina son na bata ita ni da mahaifiyarta, alfarma na ke nema a gurinka Zain, na san Hafsat tana matsayin kuyangar ka ne, amman ta yi kankanta da wannan idan ma na tuna abun yana bata min rai, domin a yanzu bata san komai ba, ina neman alfarmar ka fadi abunda zan baka na muƙataba, sai ka barranta ta daga kuyanga, idan har ta girma ta mallaki hankalin kanta, kuma ta ji tana kaunarka ita da kanta zata nemeka, ban yi hakan da wata manufa ba, sai dan inganta rayuwarta, domin akwai kalubane mai yawa a rayuwarta ta nan gaba matukar ka tayu a zuciyarta daga yanzu zuwa girmanta.”

Shiru Zain yai kamar baya cikin wayar, ya rasa abunda zai fada tunaninsa ya tsaya cak har ya rasa abun tunani a kwakwalwarsa.

“Zain kana jina Allah yasa ka fahimta”

Jin shirun yayi yawa yasa Alhaji Habib cewa haka. Wani dogon numfashi yaja ya sauke sannan ya ce

“Na fahimta, zan turo maka account dina ka saka min dubu talatin na muƙataba daga yau ƴarka ta tashi daga kuyanga na yanta ta kamar ko wace ya mai yanci da walwala”

“Na jidadin hakan kuma na gode sosai, amman dubu talatin be yi kadan ba?”

“Ba kudin ne abun dubawa ba, muhimmancin abun ne, abun dubawa”

“Haka ne na gode sosai Allah ya saka maka da alheri”

Alhaji Habib ya fada cike da jindadi. Zain kuma ya kashe wayar ba tare da sake cewa komai ba. A take ya tura masa sakon number account dinsa, in few minutes 30,000 suka shigo account din. Sai kuma ya ji babu dadi, ya san gaskiya mahaifinta ya fada, shi kanshi zai so ta samu rayuwa mai kyau fiye da kima, amman yana ganin kamar mahaifinta be fahimce ba ne da yake masa kallon sonta yake, shi har mamakin yadda mutane basa iya banbance so da soyayya yake, Ibrahim kawai ya fadawa abunda ya faru bayan ya gargade shi akan karya fadawa kowa dan yasan Anty Ummi ba zata jidadi ba idan ta ji. Amman yasan gaskiya mahaifinta ya fada idan tana kaunarsa wata rana ita da kanta zata nemeshi, sai dai be sa ran haka ba, dan a tunaninsa zata manta da komai ne. Daga lokacin ya rika kokarin cireta a ransa, a duk lokacin da Anty Ummi tai masa magana sai ya nuna baya so, shi yasa ko da dai rana be taba tambayarta a gurin Anty Ummi ba, har rokonta yai akan ta daina masa maganarta, abunda yayita bata mamaki amman be fada mata ba, babu wanda ya san da sirrin sai Ibrahim. After six months ya je gida ganin Mai Martaba da Dada Yalwa, be jidadin yadda ya samu Dada ba, duk ta rame kamar ba ita ba, kana ganinta ka san tana cikin damuwa, duk da yawan wayar da yake da ita a can be fahimci hakan ba sai da ya sakata a idonsa. A dakinta ya ci abinci a ranar yana kallon yadda ya kasa cin komai sai furau furau, da yai mata magana sai ta saka kuka irin na su na tsofi wai da wannen zata ji rashinsa ko na Hameeda, kara ma shi tana waya da shi kuma tana ganinsa, amman Hameeda tun da ya tafi bata sake waya da ita ba, idan kuma tai ma Mai Martaba maganar a kira mata ita a waya sai yace tana nan lafiya, idan ta kira numbar ta bata samu, a iya kokarin da tai ma zuwa kaduna kuma sai Mai Martaba ya hanata. Zain yayi mamaki da ba a fada mata gaskiya ba har yanzu, wata kila ma fada mata gaskiyar zai rage mata radadin rashin Hameeda da take ji, kuma a yanzu tana kallom an zalunci Hameeda ne.

“Dada Hameeda tana wani gurin inda ba zai yi ta fito ba”

“Kamar ya?”

Ta tambaya tana tashi zaune, zuciyarsa nata raya masa karya fada mata gaskiya, sai dai yana jin fadin gaskiyar shine kawai mafita.

“Dada Hameeda kisan kai ta aikata, ta amsa laifinta ne a lokacin da muka je kutu da sunan ta bada shaidar abunda ta sani akan Farhat, hakan yasa alkalin ya yanke mata hukuncin zama gidan kaso har na tsowon rayuwarta”

Dada ta yi murmushi tare da hawaye.

“Daman na sani, tun da ka dora mata kwaha za'ayi haka Zain”

“Ba ni bane Wallahi Dada, ita da kanta ta fada ba tare da an matseta ba, kuma sai ta fitarta da wayar Farhat a hannunta wanda babu wanda yasan da wayar a hannunta, bayan haka kuma Dada ta fada mana cewar ita ta kashe Haleema ta hanyar sanya mata magani a cikin abinci, kamar yadda tai ma Farhat, daya daga cikin dalilin daya sa kika bar ganin Abida, domin ita ma tana can gidan yari alkalin ya yanke masu hukucin shekara ashiri da biyar a gidan kaso, ita da wata kawarta Fauziya”

“Miyasa ba a fada min gaskiya ba? Taya zan gasgata ku ba zan yarda ba har sai na ga Hameeda na yi magana da ita da kaina”

Ta fada cikin kuka.

“Ban fada miki dan ki gasgata ni ba, sai dan ganin boyewar da ake miki bashi da amfani, dukan mu muna tsoron rasaki ne kawai shiyasa Mai Martaba ya hana kowa yai miki jaye ko ya fada miki gaskiya, ya canja miki layin waya ba tare da kin sani ba duk dan kar kiji hankalinki ya tashi, idan kina bukata zan kaiki gurin Hameeda yanzu kinyi magana da ita, duk wayar da kike da ita a baya tana gidan yarin ne, ita kanta ta bukaci a boye miki dan kar hankalinki ya tashi”

Ta yi saurin sauka saman gadon.

“Ina son na ganta ina son nai magana da ita, ita kadai ce zata fada min haka na yarda”

Mayafinta ta dauko, Zain ya sakata a motarshi ya fita da ita ba tare da kowa ya sani ba a gidan, kamin su isa duk ta matsu babu kalar hawayen da bata yi ba, basu bata lokaci a zaune ba sai gata an fito da ita, cikin wani irin yanayi marar misaltuwa. Tana ganin Dada sai ta fashe da kuka, Dada Yalwa ma kukan take tai saurin tashi tsaye tana kallonta sai Hameeda ta zo da gudu ta rumgume Dada.

“Dada ki taimaka min na fita daga nan, ba zan iya rayuwa a cikin nan ba, dana rayu a nan kara a kashe ni kawai na hutu, rayuwa a nan kunci Dada”

Dada Yalwa ta dago kan Hameeda tana hawaye.

“Da gaske ke kika kashe Farhat ko kazafi suke miki? Ke kika kashe Haleema da gaske”

Jikinta ne yai sanyi, sai ta rasa abunda zata fadawa Dada Yalwa, ee ko aa. Kallon Zain tai sai kuma ta kalli Dada da wata kalar fuska tana tausayi da nadama.

“Ba da gangan na kashe Farhat ba Dada, kurkure ne, Haleema kuma shairin shaidan ne, na yi tunanin kamar hakan mafita ne a gareni, dan Allah Dada ki yafe min”

Lokaci daya Dada ta dauke hannayenta daga jikin Hameeda, hawayen da ke mata zuba suka tsaya, a take ta ji tsana da kuma mamakin yadda Hameeda zata iya kashe rai har biyu.

“Da aka fada min ban yarda ba Hameeda, shiyasa na ce sai na zo naji da bakinki, ashe da gaske ne, a yadda na ke ganinki ban yi zaton ko a mafarki za ki iya kashe rai ba, ashe duk daukar da nake miki kin wuce nan, ina ta ganin Zain yana cin amanarki yana miki kage saboda baya son ki, ashe yana da gaskiya, a hannuna kika tashi amman ban miki irin wannan tarbiyar ba, wannan halin ba na ahlinmu ba ne, ba ki kyautawa rayuwarki ba, kuma ba ki burge ni ba, wannan ba so bane Hameeda hauka ne bakar zuciya marar lissafi irin ta kafirai marasa imani”

Tana kaiwa nan ta juya da nufin barin gurin sai Hameeda ta rikota tana kuka.

“Dada dan Allah karki barni, ba ni da kowa a yanzu sai ke...”

Dada na ta tureta daga jikinta ta wanke mata fuska da mari.

“Ban yi zaton rashin imaninki ya kai na ki kashe rai ba, ban san da irinki na ke zaune ba tuntuni, dacan baki san da ni ba kika aikata kisan kan, rai biyu? Kuma kika dawo kina nuna bake kika yi ba, kara Farhat baki hada komai da ita ba, amman Haleema fa yar'uwarki ce uwa daya uba daya, Allah ya waddaranki Hameeda...”

Dada ta fada cikin kuka, sannan ta wuce Zain ya rufa mata baya, suka bar Hameeda a gurin tana kuka kamar na fitar rai.
Tun daga lokacin Dada bata sake tanbayar Hameeda ba, duk wani bacin rai da tunani da suke tunanin zata shiga, sai abun ya zo mata da sauki, a duk lokacin da ta tuna da girma laifin data aikata sai ta ji ta fitar mata a rai, sai dai hakan be hanata tunani ko kuka wani lokacin. Sai da yai shekara daya da komawa paris sannan ta fara kaiwa Hameeda ziyara a gidan kaso, lokaci zuwa lokaci.
Chapter 86 · 0% Book details