← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 93

Sashe 10

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cewar Zain yana kokarin tashi tsaye. Sannan ya taka a natse ya fice daga falon yana ta mamakin yadda suke kokarin yi masa abunda aka daina yayi tun kaka da kakanni, kuma a aure na biyu bama na daya ba.

“A shekarunan nawa”

Ya furta yana duba jikinsa, sai kuma yai murmushi, kamin murmushin dake fuskarsa ya gushe tunawa da makircin Hameeda. And now yayi alkwarin wa Mai Martaba ba zasu sake yin wani abu makamancin wannan ba. After that baya tunanin zaibiya ganin wata mace da har zai iya aurenta. Tunani kala kala a ransa har ya iso part dinsa wanda can kusa da part din Dada Yalwa. Sai da ya duba agogon hannunsa kamin ya tura kofar falon ya shiga.

Dare yayi yace zai fita a yanxu zuwa asibiti bayan ba aikin yake da shi ba, idan kuma har ya fita a yanxu be san yaushe zai dawo ba, beside yarinyar da zaije a akanta yasan yanxu ma bachi take, ya tabbatar Dr Ibrahim zai mata duk abunda ya bukata dan haka baya bukatar tada hankalinsa akai.

FARHAT POV.

Allahumma inni aj'aluka fee nuhurihim wa'a uzuu bika min shururihim. Ita ce addu'ar da take ta maimaitawa tunda suka kawo ta gurin, addu'ar mai muhimmanci da tasiri a halin yanxu, matukar ka karanta wannan addu'ar idan ka hadu da yan fashi ko masu satar mutane ko mai binka bashi ba zai tambaye ka insha-Allah sai dai ma ya kara maka, ko kuma wani mutum da kake tsoron sherinsa Allah xai kareka daga garesu, sai dai tun kana nesa da su ake karantawa.
Kadan kadan take maimaitawa har ta isa gaban wanda ya kirata din jikinta sai rawa yake kamar mazari.
Da yaren fulatanci yai mata magana ta sakar masa ido ta kasa amsawa balle ma har ta mayar masa da amsa, shikan a tunaninsa yaga yar'uwa ganinta fara kuma ga gashi har gadon baya, besan attachment ba ne.

“Kai ba fulani ba?”

“Fulani ce amman bana jin komai”

Ya kalli dan'uwansa sai suka yi fulatancin sannan ya sake kallonta ya ce

“Dige wane garee kake?”

“Gusau”

Ta amsa jiki na rawa sosai, a ranta kuma tana da maimaita addu'ar.

“Kana gane hanyan geeda kouu?”

“Ee ina ganewa”

Cikin barkatacciyar hausa yake mata maganar, irin hausar nan ta fulanin daji bakinsa cike da goro, kayan jikinsa sun yi datti sosai kamar wanda ya shekara be yi wanka ba, hasken fatarsa ma dishe kamar an shafa masa laka, ban da hasken fitila da wutar karar da suka kunna na haskashi ba kai kace ma wani dodo a cikin duhu.

“Amman kasan idan be ka san hanya ba zaka hadu da wani gungu kou? Dan haka in beka san hanya ba ka beri jauro shi kai ka, mun yi maka haka ne saboda hanyar fullanci”

Ta duka kasa da sauri tana masa godiya har da kukanta. Daya daga cikinsu ne ya tashi dauko AK47 dinsa ya rataya, ya dauki rawani ya nade fuskarsa da shi sannan ya hau babur dinsa mai kama da dan 50 ta kuma ta hau baya ya soma keta dajin da ita, tayi zaton wani gurin za a kara kaita ganin kasurgumin dajin da suke fitowa cikinsa wani gurin ma kamar ba daji ba, wani gurin kai kace dan adam ba zai iya rayuwa a ciki ba, sam ba ta lura da hakan ba sai yau, shigar da suka yi da su dazu da rana bata lura da hakan ba saboda hankalinta kwata kwata baya jikinta balle har ta iya gane ta inda suka biyo sai a yanxu ne take ganin ikon Allah gaba daji baya daji, duhu kam ya yi musu kamar mutum na cikin daki.

Be sauketa ko ina ba sai a bakin titi, a titi ma babu wasu motoci masu yawa, saboda dare ya yi sosai, gashi kuma kowa ya san hanyar ba mai binta a wannan lokacin sai wanda ya shirya saida ranshi.

“Karka kuskura shigga kauye a yanzu, ka koma inda ka fito”

“To na gode Allah ya saka da alheri Allah ya biyaku”

Be amsa ta ba ya juya ya koma, ita kuma ta fara gudu tana kuka kamar mahaukaciya, kanta babu dankwali daman bata zo dashi ba, Hijab din Anty Ummi data saka kuma tun a can suka rabata da shi, gashi sun karbe mata waya balle ta kira.
Haka ta rika sheka gudu kamar ance mata ga mutuwa nan bayanta, ba tai gudun minti arba'in ba ta hadu da wata motar data dauko katakai. Duka hannayenta biyu ta daga mai motar, amman yaki tsayawa, motoci kusan uku na wuce amman babu wanda ya tsaya sai wani mai motar haki, shima kuma dan an hasken safiya ya fara fitowa ne, har yayi kamar ba zai tsaya ba, sai kuma ya tsaya yana kare mata kallo.

“Baiwar Allah lafiya”

“Lafiya kalau, yan fashi ne suka tare mu suka shiga da mu daji, sai yanzu na samu dayan ya fitar ni, yace karna koma kauye, dan Allah ka taimaka min ka fitar da ni birni”

“Subhanallahi, to ai yanzu Gusau zan je, ke daga ina kike?”

“Daga gusau nake nima gada biyu”

“Shiga shiga muje”

Cikin sauri ta shiga bugubabbiyar motar a front seat. Bata daina addu'ar da take ba har suka isa cikin gusau, mai motar yai mata karanci ita take kwatanta masa ya kaita har kofar gida, dauke da hakinsa cikin mota. A lokacin bakwai saura na safe, tasan bata da inda yafi mata gidan Anty Rukaiya matukar tana cikin garin gusau, sai dai me zata ce mata bayan ta koreta? Anya ma zata karbeta kuwa? Idan ma ta karbeta Ya Bashir zai yarda ya zauna da ita? Cike da kwankwanto ta kai hannu ta buga gate din, bayan wasu yan mintuna mai gadin ya fito waje, ganin Farhat yasa shi sakin fuska da kuma mamaki.

“Aisha lafiya dai”

Bata amsa shi ya tsaya gaisawa da mai motar ita kuma ta tsaya a waje ta kasa shiga cikin gidan kamar bakonta, zuciyarta na raya mata taje gidan Anty Ummi kawai.

“Bari na kira Alhaji”

Cewar Mai gadin tare da komawa cikin gidan, Farhat kamar ta hana shi sai kuma wata zuciyarta ta dakatar da ita. Ba a dauki lokaci ba sai ga Ya Bashir da Ahmad a tare sun fito da sauri.

“Farhat Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un miya same ki”

Ya furta da cike da tashin hankali yana kallonta. Kasa amsawa tai ta noce kanta kasa sai ga Anty Rukaiya ta fito tana mata kallon uku saura kwata.

“Rukaiya ya akai ta fita? Ba kince Ummi tace ta taya ta bachi ba?”

“Korarta nai yi”

Ta amsa kai tsaye.

“Korarta kamar ya? Mi tai miki da zaki koreta? Wannan wace irin magana ce, yanzu baki san iya halin da kika sakata ba”

Farhat kam kuka kawai take, ta kasa daga ido ta kalli hararar da Anty Rukaiya take mata.

HAFSATU MANGA POV.

Ana kiran sallah asuba Hafsat ta farka, sai taji kanta kamar an dora mata dutse, kafarta kuma da zogi, ga idonta bata ganin daidai dasu dishe dishi take gani, sai dai hakan be hanata karema dakin kallon ba, komai na dakin fari ne tun daga kan labulayen har zuwa fentin dakin ga ac da freezer duka farare kamar dai silin, tashi tai zaune tana kallon ko'ina, hannayenta biyu tasa ta dafe kanta saboda jirin da take ji, ji tai kamar ana ja mata hamnunta na hagu sakamakon robar dake hannun nata. Wani uban ihu ta fasa ta fisge robar hannunta da sauri ta jefar, a take jini ya fara zuba da wanda ake mata karin da kuma na hannunta data fisge. Sauka tai saman gadon ta shige karkashi ta dafe hannun nata tana fadin.

“Na bani sun shanye min jini, wayyo.... wayyo...”

Idonta duk ya cicciko kamar zai fito waje tsabar tsoro.

*HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_

Wattpad @KhadeejaCandy

9⃣

HAMEEDA POV.

Ta tashi cikin farinciki sakamakon aabunda ya faru jiya, komai ya xo mata kamar mafarki, tasan Zain ba zai taba tsallake maganar mai martaba ba, hakan zai bata dama ta gina sabuwar soyayyarta a zuciyar Zain, hakan na nufin mafarkin ya kama hanyar tabbatuwa.

“Gimbiya kamar dai kina cikin fadinciki...”

Abida ta fada tana kallonta, kamin ta cigaba da gyara gadon da take. Hameeda ta kawarda idonta daga wayar dake hannunta tana Murmushi.

“Ba kiyi karya ba, a yau ina cikin farinciki da na dade ban samu kaina a ciki ba, kiran da Mai Martaba yai mana jiya, ya sasanta tsakanina da Zain”

Abida ta yaye bedsheet din da yake kan gadon Hameeda tana fadin.

“Ba ke kadai ba ce ake riko a gidan nan, amman mai martaba yafi baki muhimmanci fiye da komai, kin san dalili?”

Kai Hameeda ta girgiza cike da kasaita tana wani lumshe ido.

“Saboda ke marainiya ce, kuma ke kadaice kika tashi a gidan nan tun kina karama har girma a nan, bayan haka kuma kika yi aure kika sake dawowa, wannan kadai ya isa ya saka Mai Martaba ya rike ki da kima.
Gimbiya kin fi ko wace mace ta gidan nan tarbiya da gudun bacin ran Mai Martaba, mi xai hana ba zaki yi amfani da wannan damar ki cimma burinki ba”

“Ban gane ba”

Ta fada fuskarta dauke da rashin ganewar karara. Karasowa abida tai kusa da ita ta risina har kasa ta dafa kafafunta.

“Allah ya taimakeki ya kara miki lafiya, tun daga lokacin dana fahimci kina son Zain, sai na soma tausayinki saboda na fuskanci yanayinki da nasa ba daya ba ne”

“Kina nufin Zain baya so na?”

Da sauri ta hade hannayenta ta dukarda kanta kasa.

“Idan har bakina zai furta hakan, to ko na cancanci a zubar da kaina kasa jinina ya zama fansa ga kalamin da ya fito daga bakina, wane lafiyayyen Namiji ne zai kalli mace mai kyau da kima ga cikar zati yace be kyasa ba? Sai dai idan be samu ba”

“To me kike nufi?”
Chapter 10 · 0% Book details