← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 93

Sashe 12

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wow, wannan talkative din fa? Kuma da gaske haka akai?”

Cewar Ibrahim yana kallon Zain dake Murmushi.

“Amman ba ni na kade ta ba”

“Kai ne... Kuma ka kawo nan kuke dibar min jini”

Ta fada tana gyara daidaituwar hannayenta a wuyansa, da sukan karfinta ta makure masa wuya dan kar ta fado har ya soma jin zafin rikon da tai masa.

“Saka miki akeyi, ni na saka miki shi”

Ta dago ta bude ido kadan ta kalleshi.

“Ba kai ba ne, wannan ne. Dan Allah kasan gidanmu ka kaini ko kuma gidan Sarki”

“Mu a nan bamu da gidan Sarki sai gidan yan sanda”

Zain ya amsa mata. Tayi shiru bata ce komai ba, Ibrahim zai yi magana wani mutum ya turo kofar dakin ya shigo sanye da uniform din police, daga Ibrahim har Zain kallonsa suke, ban da Hafsat da idonta yake rufe hannu ya mika musu suka gaisa sannan ya gabatar musu da kansa.

“Sunana Auwal Muhammad, ni ce wanda ya kade wannan yarinyar akan kuskure...”

“Kuma sai ka gudu ka barta ko?”

“No ba guduwa nai ba nina kawo ta asibitin ai, lokacin da na kadeta muna da meeting ne shiyasa dana kawo ta ban tsaya kuma da naje ban samu dawowa ba sai cikin dare”

“Amman abun kunya ne wannan maganar ta fito daga bakinka kana dan sanda, meeting yafi ran mutum kenan? A yanayin da ka barta tana bukatar jini amman ka taka kafa ka barta nan kai tafiyarka”

Auwal ya rasa abunda zai kara cewa, a iya tunaninsa Zain dan'uwanta ne, ganin yadda yake dauke da ita kuma sai masifa yake masa.

“Yanzu dai abunda ya faru ya faru, Zain ka yi hakuri”

Hafsat ta bude idonta ta dago ta kallin Auwal, ba shiri ta maida idon ta rufe ta kara kankame Zain da dukanin karfinta.

“Wayyo na bani wayyo Allah na dan Allah ka kaini gida ka ji...”

Kuka ta soma yi na gasken har hawaye na zuba a idonta, ganinsa da tai da kayan yan sanda ya tsoratata sosai, gaba daya ta rude dakin da ihu kamar za a cire mata rai.

“Zaka iya tafiya”

Ibrahim ya fada, dan yasan Zain ba zai sake ce masa komai ba.

“Amman ya jikinta?”

“Da sauki”

“An bada jinin ne? Kuma nawa aka kashe na magani”

Wani wawan kallo Zain ya watsa masa, kamin ya dauke kansa ya fice tare da Hafsat a kafadarsa. Sai da ya fito harabar ward din sannan ta bude idonsa shima kuma dan taji ana masa wani yare da bata gane kansa ba.
Lokaci daya ta daina kukan kamar ba ita ba, sai dai har yanxu bata daina ganin mutane biyu biyu ba. Hakan yasa ta maida idonta ta rufe bata sake budewa ba, sai da taji yana kokarin zaunar da ita cikin mota.
Badan tana cikin ciwo ba da tafi kowa son murnar ta shiga mota, dan ko babur ta hau farinciki take balle kuma babbar mota kamar wannan. A front seat ya zaunar da ita sannan ya zagayo ya shiga yai mata key.

“Amman kaji yadda mutanen can suke ce maka?”

Be amsa ta ba, ita bata jira ya amsa din ba tace

“Wai sa suna ta ce maka Sa, sun raina maka wayo suna nufi san saniya fa”

Murmushi yai be ce mata komai ba, ya soma tukin.

“Wannan motarka ce?”

Nan ma be amsa mata ba. Hakan kuma be hana ta kara tambayarsa ba

“Miyasa ka kade ne? Mi na maka?”

Nan ma shiru.

“Ina zaka kai ni?”

Still shiru.

“Kai miyasa kake yin shiru idan ina maka magana? Baka san ba kyau kyale mutum idan yana magana ba, mu a garinmu ba a kyale mutum idan yana magana, ba kyau har Sarki wai sarkin garinmu ba a kyale shi idan yana magana kuma har da dukan mutum ake, mu fa garinmu bayin sarki ne mu dukanmu ake idan muka yi laifi Inna Ladi kan kullum cikin aiki take bata ma gajiya kullum sai taje gidan sarki tayi aiki....”

Ya tari numfashinta, dan ba zai iya da dagon magana irin nata ba.

“Rufe idonki”

Ta rufe.

“Miyasa ka ce na rufe ido saboda ka sake kadeni ko? Ai na san kai na kade ni, kuma ka kira min yan sanda, kuma yanxu ban sna inda zaka kaini ba kila ma sai da ni zaka yi”

“Yi shiru....”

Ya furta ba tare daya kalleta ba, kamar umarninsa take jira sai ko tai shiru. Bata kuma bude idon ba har suka shiga gidan Anty Ummi.

*HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_

Wattpad @KhadeejaCandy

1⃣1⃣

Kamar ta hadiye zuciya ta mutu haka take ji, bata tuna komai na rayuwarta, kokari taje ta manta da Auwal da Ya Bashir da kuma abunda ya faru da ita jiya amman ta kasa, abubuwa uku sun hade mata a lokaci daya.
Idan tai unkurin kuka sai yaki zo mata, tana zaune dakinta har Anty Rukaiya ta fita ta dawo, bata motsa daga kwancen da take ruf da ciki ba har Anty Rukaiya tai shirin office ta fita. Sannan ta taso ta fito falo kamar marar lafiya haka take tafiya idanuwanta a sun yi ja sosai jiri na dibanta kadan. Saman cushion ta zauna tana matsar jiki kamar mai jin sanyi. Ji tai tana son waya da Auwal tana son ji daga gareshi tana son da tabbatar gaskiyar daga bakinsa, amman kuma a yanxu bata da waya a hannunta. Tashi tai ta koma dakin ta dauko hijab dinta ta saka ta fito cikin saurinta mai kamada zata fadi ta fita harabar gidan.
Sai da ta kusa karasa gidan Anty Ummi sai kuma wani tunanin ya fado mata, zuciyarta ta soma ganin laifin Anty Ummi, da ace bata fadawa Anty Rukaiya ba da bata yi mata wulakancin daya sakata cikin halin data kasance a jiya ba. Ajiyar zuciya ta sauke yafi a kirga tana ta kwankwanton shiga. Can dai ta tura kofar gate din ta shiga cikin yanayin damuwa. Tunda ta hango motar Babansu Amal ta san yana nan, a ka'ida bata shiga idan Abban su Amal yana gida musamman da safe, saboda baya sake mata fuska ita kuma tana ganin kamar shigowarta gidan ne baya so.
Da kanta ta tura kofar falon ta shiga, ba tare da ta tayi sallama ba. Anty Ummi dake tsaye gaban dinning ta juyo ta kalli kofa, ganin Farhat yasa ta sakin fuska tare da murmushi.

“Yar halak tun jiya nake zancenki a raina”

Shirun da taji Farhat tayi ne yasa ta aje kofin hannunta ya nufata tana kallonta cike da mamaki.

“Ke miya sameki?”

Farhat ta kalleta ido cikin ido ta ce

“Yadda ce tasa na fada miki sirrina Anty Ummi, kallon uwa nake miki saboda tawa uwar bata kusa da ni, har abunda be kamata ki sani ba, kin sani a kaina, miyasa zaki je ki samu Anty Rukaiya da magabar bayan kuma na fada miki karki yi mata maganar?”

“Ban yi mata maganar ba sai ta sigar da ta fahimta, idan har zan iya saka yata Amal a cikin matsala zan iya sakaki Farhat, kokarin cire ki nake a damuwa ina kokarin sama miki mafita ne, saboda bana son rayuwarki ta lalace”

“Da baki fada mata ba, da bata mareni ba, da bata kore na bar gidan ba, har na hadu da barayi....”

“Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un”

Anty Ummi ta rikata ta zaunar. Farhat kuma ta fada mata komai daya faru ciki har da boye gaskiyar da Anty Rukaiya tayi ma Ya Bashir ba.

“Anty ji nake kamar na sha wani abu na mutu, na shiga tsakanin yar'uwata da mijinta, yanxu rashin yarda zai shiga tsakaninsu, a kullum zata rika ganina da abun ne, a macuciya take kallona tana kallon na ci amanarta, tana min kallon wacce zata rabata da gidan aurenta.
Da ace ban zo birni na waye ba da Ya Bashir be kwadaitu da ni ba har na shiga tsakaninsa da matarsa, da Auwal be ganni ba balle har ya yaudareni”

Anty Ummi kallonta take cike da tausayawa ba dan ta fahimci inda furucin na karshe ya dosa ba.

“Anty Ummi Auwal ya yaudareni wata zai aura, satin nan za a daura masa aure da wata macen ba ni ba, shekara hudu da muka yi a tare ya tashi a banza, soyayyar da yake nuna min ashe duk yaudara ce, yana yawan fadamin buri daya ya rage masa a duniya shine na aurena ashe karya yake, Anty naga iv aurensa da wata naga pre-wedding picture dinsa da wata, shiyasa a duk lokacin da nai masa zancen turowa sai ya canja min magana ko ya kawo min wani uzuri, shiyasa yake ta min yawo da hankali, ya san ba zai aureni ba ya bata min lokaci yasa na kori kowa nawa...”

Maganar kawai take kanta na rawa kamar ba ita ba, sai a yanzu hawaye masu zafin gaske suka soma sauko mata. Anty Ummi ta kama hannayenta ta rike gam tana kallonta ta yadda zata tabbatar cikin hayyacinta take.

“Da gaske kike Auwal ya yaudareki Farhat? Da gaske Auwal wata zai aura ba ke ba?”

Ta daga mata kai.

“Jawahir ta fara kirana ta fada min, na hau whatsapp naga hotunan da idona, Anty wannan shekarar ta zame min bakar shekara, bakin wata kuma bakar rana, ina ma ban zo duniya ba”

“Amman Rukaiyah taji wannan abun?”

“A lokacin data dawo da fushi ta dawo, ni kaina ban san mi nake ba a lokacin kamin na labarta mata komai ta sauke min mare biyu ta koreni, yanxu ma nasan ba zata barni ba korata zata yi, ni kaina ina son tafiya, ina son nayi nisa da mutane ina son na tafi duniyar da babu wanda ya san ni”

“Farhat ba zaki iya rayuwar kauye ba, idan kuma kika je mi zaki fadawa Ummanki?”

“Bana son kauyen wani gurin zanje inda zan manta kowa, ina jin kaina kamar babu komai a ciki, Anty ina son nai magana da Auwal ina son naji daga gareshi, yau zan bar garin tafiyata zan yi bana son kowa....”
Chapter 12 · 0% Book details