← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 93

Sashe 46

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Momy na fadar haka ta tashi ta nufi dakinta, Hafsat ta yi shiru tana kallon tea dake gabanta. Sapna ta kalleta

“Bloody please ki cire wannan tunanin a ranki, ni ban ga abun tada hankali ba, impact ni da za ki dauki shawarata ma ki fitar da wannan Ibrahim din ki yi aurenki, in yaso daga baya idan kina son aikin sai ya nema miki”

Fashewa tai da kuka.

“Shi ma fushi yake da ni”

Sapna ta bato kujerarta ta zo ta dafa Hafsat.

“Zai sauko kin san ai yadda yake son ki, so ki shareshi kawai ko bashi lokaci zai dauko dole ne yanzu yai fushi da ke saboda abunda ya faru yana ganin kamar da laifinki a ciki, kuma ina tunanin yarinyar tana da muhimmanci a gurinsu, waya sani ma ko yar daga cikinsu ne suke boye there's is something behind this issue”

“Zai iya zama haka ko?”

“Yes akwai abunda suke boyewa a tsakaninsu, kuma sun yarda da ke ke kuma kika kai failed dole zasu ji haushi”

“Amman Ibrahim yana da yara, ba zai boye wata yarinyar ba, sai dai ko in Zain din”

“It could be him ko kuma wanin abun dabam, dan haka ki bashi lokaci zai sauko”

Ta gyada kai sannan ta dauki tea gaba daya ta shanye ta tashi ta nufi dakinta, wayarta ta dauka ta shiga massage tana aikawa da Zain sako.

_Doc ka yarda da ni, Wallahi babu hannu a lamarin nan, amman akwai wata yar'uwarka tace min sunanta Hameeda ta zo nan tare da Doc Isma'il tana binciken yarinyar kamin hakan ya faru, ban san alakarka da ita ba, ba kuma ina nufin wani abun ba kawai dai na ga ya dace na fada maka ne_

Sai da ta gama tsara sakon kamar haka sannan ta tura masa.

*** *** ***

Babu irin cin mutunci da Momy ba tai ma Auwal ba, akan maganar har tana masa rantsuwa idan be fidda kansa cikin maganar ba, sai ta sanarwa Abbah kuma sai ta mugun tsaba masa.
Tun da take masa fadan be ce uffan ba har ta gama sannan ya bata hakuri tare da alkawarin ba zai sake faruwa ba.

“Ina ruwanka da yarinyar, uwa ka hada da ita ko uba? Akan me zaka tsaya kai da fata wai kai sai ka binciko abunda be shafe ka ba”

“Momy na ce ayi hakuri ba zan sake ba, i promise”

“Da ya fi maka”

“Allah ya huci zuciyarki”

Ta katse kiran, shi kuma ya sauke wayar yana jin mai haushin Hafsat. And ya ma kansa alkawari ba zai sake damun kansa da maganar ba. Amman ya tuna Zain yana jin zafinsa sosai, yana yawan auna yadda Zainab take tsaye a gabansa haka Farhat take tsaye a gaban Zain, yana morewa da ita dukan wani tanadi da buri da yake da shi akanta ya tafi a banza.

“Zainab bata cikin tsarin matan da na ke so,amman look at me ina zaune da ita by force gaskiya abunda su Momy suke min ya yi yawa, yana da wahala a samu yaro mai biyayya irina, sun rabani da wacce nake so a duk lokacin da na unkuro zan yi wani abu sai sun shiga sun fita sunga sun hanani sannan hankalinsu zai kwanta”

A fili yake zancen yana daga murya, kai kace ma ba a falo yake ba bayan kuma ya san Zainab tana cikin kitchen tana shirya musu abin karyawa. Lekowa tai daga kitchen din daman tun dazu tana jin hayaniyar yanayin wayar da yake da Momy.

“Lafiya kamar kana magana”

Be tanka ta ba, ya tashi ya wuce dakinsa cikin mugun jin haushi. Yana shiga ya wurgar da wayarsa saman gado.

“With his dirty hands zai taba jikinta, wani kazami da shi malam, yarinyar da na dade ina raino wani banza ya zo kawai ya dauketa ta could you imagine?”

Ya halbi wardrobe fa kafarsa.

“Ni gaskiya an cuce ni, Wallahi ina son Farhat nan kawai Abbah ya zo ya hada ni da wannan yarinyar, and i was planning na aureta a my second wife wannan banza ya zo ya aureta. What if all those things a plan? Miyasa be kai yarinyar nan wani guri ba sai gidanmu? And now aka kawo ta aiki a cikin gidana?”

Juyowa yai ya dawo falo, a lokacin Zainab na tsaye gurin dinning tana jera kayan abinci.

“Zainab wace tsohuwa ce ta kawo miki yarinyar nan?”

Juyowa tai ta kalleshi.

“Miyasa ka tambaya?”

“Just”

“Wai mi yarinyar tai yi ne? Ni ban gane maka ba, an kawo yar mutane ka zo ka dauketa ka bada ita ga wasu police yanzu kuma kana ta tambayar lamarin yarinyar?”

“Ba komai kawai ki amsa min”

“Nima ban san matar ba, kawai dai ina son na tabbatar da wani abun ne, matar data kawo ta ai tace ita kanwar mahaifinta ce ko? Yanzu kuma Dcp ya aiko a ka dauki yarinyar wai wani case suke can iyayen yarinyar suna nemanta”

“To ko wannan matar sato ta tai?”

“Shine abunda nake tunani, amman da ta sato ta miyasa bata kaita ko'ina ba sai gidana? Ina kika hadu da matar ne?”

“A nan kawai ta shigo ta tambaya wai ko ina son mai aiki, a lokacin tana tare da wata babbar yarinya nace mata ina so amman wannan ta mun girma sai ta za a kawo min karama, shine yanzu ta kawo ta”

“Ki yi hankali da irin mutanen nan masu shiga gida gida neman masu son yar aiki wasu macuta ne, ida....”

Tunawa da yai da magabar Momy yasa shi yin shiru be karasa ba.

“Minene?”

“Ba komai, abincin ya yi”

“Ee”

Ta fada ba dan ta gamsu babu komai din ba.

*** *** ***

He spent all night thinking of Yarinyar kauye, yana ta son hango wanda yai dalilin raba shi da ita, amman a duk inda ya duba sai Anty Ummi yake hangowa domin ita cw silar komai, but after ita fa? Waya san sirrin zaman Hafsatu manga a gidan? Just him and Ibrahim, Hafsat ta shiga ciki ne saboda Ibrahim ya sakata baya son kawowa zuciyarsa abunda ba shine ba, he started Suspecting something.
Yayi saurin tashi tsaye yana dafa kansa.

“No no no Ibrahim can't do this to me, i trust him?”

‘Amman kuma wa? He is the only one daya san sirrina duk wanda zai san wannan sirrin a inuwarsa ya fake, idan ma Hafsat din ce ai itama ta dalilinsa ta sani, but wait mai zai sa Hafsat tai masa haka? Ta san Anty Ummi ta ne? Amman ai da Anty Ummi bata bada yarinyar ba da duk haka be faru ba’

Sake sake yake ta yi a ransa, a duk inda ya zaga ya zagayo Anty Ummi ce matattarar faruwar komai. Lumshe idonsa yai y busar da iskar bakinsa a hankali.

“Ban san tararar dake tsakanin ganina da na ki ba, kin yi kankanta na ce son ki nake, kin yi yawa na iya mantawa da ke, motsi kike da tafiyar numfashina, ko wace dakika tana kara azabtar da zuciyarta da nisan da kika yi da ita”

Yaje gaban window ya tsaya yana cigaba da magana da kansa kamar sabon mahaukaci.

“Ke kadai ce abu mai rai daya naji ya tsaya min a rai bayan tafiyar Haleema, ke kadai ce abu mai motsi dake sani nishadi da jindadi, ina jindadi kusanci na ke ina jin natsuwa da kwanciyar hankali idan ina kusa da ni, ban san kilo mita nawa ne a tsakanin mu ba, amman kusanci yana nan kusa da ni a gefen zuciyata, hoton fuskarki da rayuwar da muka yi yana nan a zuciyata, ba zan taba mantawa da ke ba har a bada, ina miki fatar samu natsuwa da kwanciyar hankali a duk inda kike...”

Wayarsa ce dake kan gado yai kara alamar shigowar sako, juyo yai ya kalleta sai kuma ya dauke kansa ya jingina da gurin, it pain him idan ya tuna yadda ya bar bata, yadda take kallonsa da yadda hawaye suke zuba a idonta. Yana tsaye a gurin har rana ya hudo ya soma hasko dakin, sannan ya juya ya shiga bathroom yai wanka ya fito ya shirya cikin kananan kaya as usual ya feshe jikinsa da turare. Daf da zai wuce ya dauki wayar ya duba, yana ganin sunan Doc Hafsat a sms din yasa ransa ya bace, be bude sakon ba ya danna delete ya goge sakon, ya dawo contact dinsa ya goge number ya shiga block list yai blocking dinta sannan ya saka wayar aljihu ya fito, ya nufi dakin Farhat.
Be sameta a dakin ki ba, hakan yasa shi daukowa kasa, sai ya samu tana kitchen tana hada musu breakfast. A bakin kofa ya tsaya yana kallon kafafunta ta tsaya tsaf da alama sun mata sauki ko kuma sun daina ciwon. Kamshin turaresa ne ya sanar mata da zuwansa amman saboda karfin hali taki ta juyo ta kalleshi, juyo yai ya fito ya shiga motarsa, sai kuma ya fito ya shiga cikin gidan ya dauko wani akwati ya fito ya bude bayan mota zai saka shi, tsaye yai cak yana kallon kayan Hafsatu manga wanda ya siya mata a lokacin da tai zama asibitin, ya sasu bayan motarsa da da zimar idan ya fito ya zubar amman ya manta sai a yanzu da zai saka box din yaga kayan, hannu yasa ya dauko wata riga ya rike yana ta kallo sai kuma ya kai hancinsa ya shinshina.
Fasa saka box din yai ya rufe bayan motar ya dawo ya aje shi a front ya shiga gurin zamansa ya zauna yana rike da rigar, wayarsa ya dauko ya nemo number Dcp ya kirashi.

“Ina ka ce iyayen yarinyar suke?”

“Nijar, lafiya dai”

“Nijar a ina?”

“A damagaram”

“Basu baka adireshinsu ba”

“Mi zai sa su bani addireshinsu?”

“Amman ai kai dan sanda ne dan sanda ma Dcp miyasa baka yi abunda aikinku ya tanada ba kamin ka mika yarinyar ga mutanen? A yadda muka ta so da kai Faruk ba haka kake a makaranta ba, kai mutum ne mai gaskiya da kokarin fitar da ita miyasa ka canja”

“Har yanzu ina nan a yadda nake Zain, kai ne dai ka canja ka daina yarda da mutane, kana ganin kamar kowa kokarin cin amanarka yake”
Chapter 46 · 0% Book details