Sashe 72
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“It could be her, waya sani ko mahaifiyar bata raye? Idan Abbah ya dawo da ita sai mahaifiyarmu ta tafi? Haba dai Hassana ki yi tunani mana”
Tsaki taja ta kashe wayar, a daidai lokacin da take parking a harabar gidan Alhaji Salisu Alhasan. Cike da bacin rai ta fito ta shiga cikin gidan, a tsakar gida ta tsaya tana gaisawa da kananinta sannan ta shiga cikin falon inda mahaifinta yake zaune tare da mahaifinsa da wasu kanensa. Yana ganinta sai ya tattaro dukan hankalinsa ya maida gurin har ta zauna tana gaishe da Alhaji Salisu. A nan ta soma yi musu bayanin kan case din har ma da fada musu cewar Husaina ta karbi case din, suna haka sai ga Anty Ummi shigo rike da takardar tana murmushi mai kamar kuka ta mikawa Alhaji Habib.
“Ga result din”
Kamim ya karba Hassana ta kai hannu ta karba ta bude tana karantawa, rufe baki tai idonta ya cika da hawaye sai ta mikawa mahaifinta. Cikin fargaba ya karba ya bude shi kam murmushi yai ya juya a gurin yai sujuda godiya ga Ubangijinsa. A ranar kasa hakuri yai har sai da ya saka yarsa a gaba suka koma gurin Hafsatu manga ba a hana su ganinta ba kasacewar Hassana ce lauyarta suna zaune a gurin da suka zauna da zu, suna gurin aka fito da ita. Ganin babu wanda ta sani a cikinsu yasa ta ki yarda ta karaso kusa da su, sai kawai tasa kuka. Alhaji Habib ya karasa inda take ta duka tana dafa kafadarta hawaye na zuba a idonsa.
“Ya ta...”
Ya furta yana murmushi mai cike da kunci. Ya shafa fuskarta sai kuma ya rumgumeta.
“Ina Zat?”
Shine abunda ta tambaya tana kokarin raba jikinta da na shi. Sai Hassana ta risino ta shafa bayanta tana kokarin yi mata bayani.
“Hafsat wannan mutumen da kike gani....”
Bata karasa ba ya daga mata hannu, yana share hawayensa.
“Shi ya kamata yai mata wannan bayanin, da alama ta shaku da shi sosai, dazun ma da muka zo gurinsa taje yanzu kuma shi take tambaya, ina ganin idan yai mata bayani zata fi fahimta, ko mahafiyarta bata tambaya yadda take tambayarsa wata kila ma bata raye, Ƴa ta fada min ina mahaifiyarki?”
Ya karasa yana tambayar Hafsatu Manga. Sai ta ɓata fuska.
“Nima ban sani ba”
“Yaushe rabon ki da ita?”
“Tun muna kauyen nan kamin gayu su koremu”
“Daman ta saɓa tafiya ta barki?”
“Ee amman tana dawawa yanzu ko ta dawo ba zata ganni ba, saboda ba na can”
Tasa hannu tana murza idonta.
“Mahaifiyarki tana da awarwaro?”
“Ee tana da shi”
“Miye sunan Mahifiyarki? Kin san inda take zuwa?”
Sai ta lake kafada.
“Kai ma sace ni za ka yi?”
“Aa zan nemo inda mahaifiyarki ta ke ne”
Bata sake cewa komai ba, duk irin tambayar da yai mata bata amsa masa ba, Hassana ta dauketa hoto a wayarta sannan aka maida ita tana kuka kamar ɗazu.
Washe garin ranar aka bada gawar Farhat kamar yadda Dpo Auwal ya alkawaranta, sosai iyayenta suka so su tafi da ita gida, amman Mai Martaba ya roki alfarma a yi mata wanka da sallah a nan, kuma aka rufe ta a nan, a ranar Zain ya sha kuka irin kukan da sam ba zaka za ci zai iya yinsa ba, a masarautar akai karbar gaisuwarta wadanda basu san da zamanta a gidan ba da wadanda basu san Zain ya aurota ba yanzu kan sun sani domin Mai Martaba ya bada sanarwar a fadawa kowa da kowa, a fadarsa akai zaman uku kamar yadda al'ada ta tanada, su kuma a can Anka Local Government suka yi na su, sai a yanzu Inna take nadamar abunda ta aikatawa Farhat irin furucin da tai mata da kuma nuna bata son auren, daman ba a son furuci ko fushin iyaye, ta yi nadamar da da bata da amfani dan ba zata dawo da ita ba, kuka take sosai kowa sai da tausaya mata.
HAMEEDA POV.
Tun daga ranar da aka dawo da ita gida, bata sake leka waje ko da part din Dada ne, ta kebe kanta a dakinta har aka yi karbar gaisuwar aka gama bata fito ba, Dada da kanta take shiga ta duba ta tana bata magana kamar dai sauran yan gidan, wandanda suke alakanta hakan da abunda Zain yai mata.
Daga ita sai Fauziya suka san gaskiyar lamarin da ya hana ta sakewa da sukuni, ta rasa natsuwa saboda abunda ta aikata, ko a lokacin da ta aikata makamancin wannan ga yar'uwarta bata ji rashin natsuwa kamar haka ba, duk ta bi ta rame kamar ma ciwo, ko iska ya kada sai ta zabura gashi zuciyarta na raya mata cewar asirinta zai tonu idan aka shiga kutu domin Dada ta fada mata Monday nan mai zuwa za a shiga kotun. Yau ma Fauziya ta ziyarce ta bayan gama karbar gaisuwa da aka yi shekaran jiya, ta lura da yanayin da Hameeda take ciki ta tsammaci zata canja saboda fadan da tai mata jiya.
“Haba Hameeda, idan fa baki sake kin zama kamar yadda kike a da ba, za ki iya tonawa kanki asiri, idan kika cigaba da wadannan dabi'un za a iya gane wani abu a tare da ke”
Ta daga kai ta kalli Fauziya da idonta dake nuna tsantsar rashin natsuwa da kwanciyar hankali.
“Fauziya kin taba kashe rai? Ta hanuna na daba mata wuka kuma ta mutu, yanzu idan anje kotu asirina tonuwa zai yi dole za a gane ni ce”
“Taya za a gane ke ce? Fitowa za ki yi ki fadawa duniya abunda kika aikata? Haba dai ki daina yin abu kamar wata marar ilmi da wayewa mana, ki bani wayar zan jefar da ita a wani guri inda ba babu wanda zai gani ba”
“Aa zan ajeta a gurina”
Ta fada tana girgiza mata kai, dan bata yarda da kowa ba a yanzu, tana ganin tun da har Abida ta ci amanarta, to kowa zai iya cin amanarta. Duk juyin duniyar nan da Fauziya tai na ta karbi wayar dan ta taimaka mata sai Hameeda ta ki yarda.
*** *** ***
In all those days yan'uwan Rufaida da iyayenta sun saka cigiyarta a duk inda suke sa ran za su sameta kuma sun dukufa akan addu'a ba dare ba rana, Alhaji Habib kam har kudi ya saka ga duk wanda ya ganota ko ya san inda take ko inda za a sameta. Amman shiru babu ita babu labarinta.
A haka Alhaji Habib yake yau yana Kaduna gobe yana Zamfara, be maida hankali kan ciwon Hajiya Safiya ba, tun daga lokacin da Hassana ta fada masa be sake leka asibitin da sunan ganinta ba, sai dai yana bada kudin kula da lafiyarta, ga ciwon kan ya ki sauka sai karuwa yake har ta fara fita hayyacinta saboda ya tsananta mata sosai. Babu irim rarrashin da Hassana da Husaina da yan'uwan Safiya ba su masa na ya hakura ba, amman yaki ya taka yaje dubata saboda baya kaunar sakata a idonsa. Gaba daya hankalinsa ya tattara ya koma gurin neman Rufaida.
*** *** ***
Yau dai kam yana jin komai yai masa tsauri, duniyar ta isheshi, kwakwalwarsa ta tushe yana jin kansa kamar babu komai a ciki, gidan duk ya fita ransa kuma be san wani gurinda zaije ya samu sakewa ba. Sai dai ya farka da tunanin Hafsatu manga kamar yadda yake a kullum, around nine o'clock ya kira Barrister Hassana yana son ta shige masa gaba dan ganin Hafsatu manga, he miss her so much, ya san yadda halinta yake bata da natsuwa idan bata ganshi ba, gashi maganar da yake son ya fada mata akan Alhaji Habib. A take ta amince duk kuwa da kasancewar yau assabar ce ba kasafai take son fita weekend ba.
Kamar kullum yau ma sai da Ibrahim ya kawo masa breakfast din da matarsa ke hada masa kullum. Ko da ya shigo ya tararda Zain ya shirya cikin riga da wando na shadda sky blue sai kamshi yake. Ibrahim ya kalleshi yana jin kamar ya zolayesa sai dai kuma be dace da wannan wasar ba a yanzu.
“Ina zaka je?”
“Mama zan je gani, ka zo a daidai zan je mata da indomie nan dan tana son indomie, sai na biya na siyo mata chocolate”
“Ai ka fada min da nasa Madam da girka mata wani abun dabam like nama na san ba zata ki so ba”
“Karka damu wani lokacin za ayi”
Suna maganar Barr ta kira Zain ta sanar masa tana gurin shi kawai take jira, a aggauce ya fita daga gidan ya bar Ibrahim nan, sai da ya biya ya siya mata kayan makulashe sannan ya isa gurin.
Ciki ya shiga dauke da kwandon abincin da Ibrahim ya kawo masa, dayan hannunsa kuma rike da ledar da yai mata siyayya. Ko da ya shiga ya samu Barr Hassana a zaune tare da ita tana zuba mata farfesun kayan ciki a plate, tana ganin Zain tai saurin mikewa tsaye zata je inda yake sai yai saurin karaso kusa da ita yana fadin.
“Zauna ni ma zaman zan yi”
“Zat baka zo ba, kullum baka zo ba”
Ta fada kamar tai kuka.
“Gani na zo ai yi hakuri, aiki ne ya rikeni kina lafiya ko?”
“Aa bana lafiya, jikina yana zafi kuma kaina na ciwo ina yin kuka kullum”
Hannu ya kai ya dago kanta yana kallon yadda fuskarta ta rame kamar shi.
“Zat yaushe zasu fitar da ni daga nan? Ka fada musu ba ni na kasheta ba”
“Zan fada musu, dole ne sai munje kotu kotu zata wanke ki”
Ta bude baki
“Kotu? Aa bana so ina tsoro”
“Babu wani abun tsoro ga yayarki nan zata tsaya miki a kotu har sai mun yi nasara”
Ta kalli Barr Hasaana wacce ke mika mata plate da spoon.
“Ba ni da Yaya”
“Ba ni da Yaya”
“Yayarki ce mana, wannan mutumen daya zo ai Babanki ki shine mahaifinki”
“Aa ni bani da Baba ban taba ganin babana ba”
“Babanki, ya shekara da yawa yana nemanki amman be ganki ba, yanzu mahaifiyarki ake nema idan an ganta zata fada miki gaskiya”
“Mama ta bata magana Sunana kawai take kira”