Sashe 84
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Saman gadonta ta fada ta rushe da kuka mai karfi har jikinta yana jijjiga. Wayarta ce tai ringing sai tai saurin tashi ta nufi wayar ta dauka ba tare da ta share hawayen idonta ba, sai dai ta yi kokarin daidaita muryarta dan kar a gane kuka take.
“Hello Amal”
“Pretty ya kike?”
“Lafiya kalau, ina Anty Ummi”
“Tana lafiya, ki bude Instagram Uncle yana live”
“Da gaske?”
“Wallahi”
Tayi saurin kashe wayar ya share hawayenta, sai ta nufi inda system dinta take da sauri ta dauka ta dawo saman gado ta zauna tare da cire hijab din jikinta. Ta dora laptop din saman jikinta ta kunna. Kai tsaye taje page dinta na instagram. Ji tai ba zata iya jira news feed ya kawo mata shi ba, dan haka ta shiga search side ta rubuta sunan da ake kiransa da shi. *Craftsman* a take aka nuna mata su, na shi na ainishi wanda a kai ma mark da kuma na fake da sai foundation dinsa da kuma support groups kala kala. Wanda aka yi ma mark da sky blue tai saurin budewa daman ta san shi ne na shi na ainahi domin tana following dinsa. Kamar yadda Amal ta fada mata tana live saboda wani program da suke a can kasar paris, ya saje ta turawa har baka iya gane shi din bahaushe a fata sai dai a fuska, turanci yake watsara kamar daga bakinsa ya fito, ya saka suit blue wanda ya kara fito da kyau da kuma annurin fuskarsa, beard dinsa ya kwanta sosai ya yi baki har wani shining yake, like always he look very beautiful and attractive, you can't call him young sai dai kuma he is not that kind he look very gentle.
Bata san lokacin da murmushi ya subuce mata ba, zuciyarta na bugawa with each and every single word of his. bakinsa take kallo kamar wacce ke kirga fararen hakuransa. Idan yai dariya sai tai dariya idan kuma ya cigaba da magana sai ta maida hankali tana kallonsa, sai dai babu abunda ta haddace daga kalamansa, farincikinsa da walwalarsa kawai take lissafi, haka take a duk lokacin da take kallonsa, sai ta nemi bacin ranta ta rasa. Hannu ta kai ta shafa screen din laptop din hawaye na sauka daga idonta.
“For how long zan yi ta jiranka Zain? For how long zaka san I am still alive? Sai zuwa yaushe za ka zo ka nemi ajiyarka? Na kasa sabawa da rashinka, kai na ke ta yi ma ajiyar kaina, sai yaushe za ka fahimci irin halin da na ke ciki? Ka manta da kana da mata ko? Zan jiraka Zain ko da jiranka na nufin karshen rayuwata ne, ko da hakan na nufin shiga wata duniyar ne, zan jiraka Zain dan jiranka shine kadai farincikina a rayuwa...”
Tana gama fadar hakan ta daga kanta sama hawaye ya sauko ta gafen idonta...
[4/6, 2:43 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *58*
Wayarta ce ta sake ringing, sai ta bude idon ta kalli mai kiran. Ganin Amal yasa ta saurin dauka.
“Kina kallonshi ko?”
“Yeah, Amal ban san miyasa yake ta boye min kansa ba, ko maybe ya manta da ni ne ko kuma yana ganin matan turawa yana ganin kamar ni ban dace da shi ba?”
Ta yi maganar cikin muryar kuka.
“Bana tunanin haka pretty maybe dai akwai wani dalilin na dabam, amman ya gane ke ce da kika kira shi?”
“Ya gane, daga lokacin da ya gane sai yai blocking dina, babu ind bana fallowing dinsa Facebook twitter instagram amman da ya fahimci ni ce sai ya blocking dina, ina son ganinsa Amal ina son na tambayi shi wani abu, da zarar mun gama exam zan je har paris inda yake”
“Haba pretty ba ki bukatar yin hakan”
“Amal ba ki tunanin nima na cancanci farinciki? Iyayena suna tare da ni amman ina jin uncompleted, Amal i love him so much”
“I know, na ji Anty Ummi na fadin cewar jikin Hajiyarsu babu dadi sosai maybe ya zo dubata”
“When? A satin nan? Ina ganin zan dawo Gusau na zauna a gurin Anty Ummi so that idan ya dawo na samu ganinsa”
“No don't ba Exam zaku fara ba yanzu? Karki yi bar Exam dinki saboda ganin Uncle na miki alkawari idan ya zo duk yadda zan yi na hadaku zan hada ku”
“Okay Thank you Sis”
“Anything for Sis”
Tana aje wayar ta kwanta samman gadonta ta cigana da kallonsa, wani lokacin take tunawa ten years back, lokacin da take secondary school, a duka hutun da suka samu Anty Ummi tana aikowa a tafi ta ita, ita ce take yawan bata labari a kan Zain, how he sacrifice for her, irin wahalar da ya sha na rayuwa, da kuma irin kalubalen da ya fuskanta, daman bata manta wasu abubuwa da suka faru ba, amman Anty Ummi ce take tuna mata da komai bit by bit, har komai ya dawo mata fresh, sai duk hutun da take zuwa da maganarsa da Anty Ummi take mata, ko sau daya bata taba bata waya su gaisa ba, bata taba hada da shi idan ya zo garin duba iyayensa ba. From that day Hafsatu manga ta sawa kanta son ganinsa daman ta girma ta kaunarsa, domin bata san a alakarta da shi ba bayan fitar da yai, amman ya zauna a kwakwalwarta har zuwa girmanta, Anty Ummi ce ta fayyace mata komai, bata san zafin sonsa ba sai a yanzu da ta mallaki hankalin kanta. Tun daga 17 years ta fara shiga yanar gizo saboda shi, ta yi ta samun fake account kamin Amal da Anty Ummi su banbance mata na kwaran na shi da kuma fake. Daga ranar da tai masa magana ta sanar da shi ita ce sai yai blocking dinta, a duk wanda take binsa abunda ya daure mata kai kenan har yanzu take mamaki.
Bayan ta gama secondary school a Kaduna, sai Mahaifinta ya nema mata university Abuja, a gidan Hajiya Asma'u ta zauna wato yayar Rufaida Mahaifiyarta, daga lokacin da ta zo gidan dan Asma'u Raheem ya kwallafawa ransa sonta ita kuma tai ta nanata masa cewar ita matar Zain kamar yadda Anty Ummi take yawan fada mata. Ta nan maganar ta kai ga mahaifinta Alhaji Habib, already Hajiya Rufaida ta san komai domin ita ce best friend din yarta bata boye mata komai, Alhaji Habib yayi mamakin jin inda maganar ta fito domin ya dauka yarsa ta manta da Zain, ba shi da wani zabi bayan goyon bayan yarsa da kuma son abunda take so. Some people take it as a joke idan tana cewa shine mijinta domin bata boyewa kowa, more especially ma Raheem wanda ya kasance dan Hajiya Asma'u, yana tunanin tana yin haka ne kawai dan bata son sa, a yayinda mahaifiyarsa kuma take ganin kamar ta dasawa ranta sonsa ne saboda kawai ta ga he's billion, ga shi kyakkyawa kuma wanda duniya take ji da shi saboda kwariwar aikinsa da kuma irin taimakon da yake ma mutanen Africa especially Nigerians. Sai mahaliccinta ne kadai shaidar cewar son gaskiya take yi ma Zain, bata san dalilin son da take masa, saboda yayi sadaukarwa da yawa akanta ko kuma saboda yana daya daga cikin irin mazaje da take so ne? idan ta ga wasu suna crushing akansa a social media ko zahiri har ji take kamar ta hadiye zuciya ta mutu. On her First day a school ta hadu da kawayen kwarai yayan manyan mutane, wato Amina (Black bauty) Fatima (Diamond) Rabi'atu (Pearl) ita kuma suka saka mata Pretty da haka sunan ya bita har cikin familynsu, suka hada kansu komai za su yi a Scul din ko wajen scul a tare suke yinsa baka isa ka tana dayar ba sauran su kyaleka, idan dayan su ya samu abu kamar dukansu ne suka samu saboda hadin kai da kaunar junansu da suke.
Ziyar farko da Anty Ummi ta kai mata da yarta Amal (That little girl yar Anty Ummi remember?) ta yi ta mata nasiha da tunatarwa.
“Ki rika rufe jikinki, Zain mutum ne mai tsananin kishi akan abunda ya ke so, ba zai jidadi ba idan kina barin jikinki sake, karki kula kowa kin san ke matar aurece domin masarautar Damagaram ta mallaka masa ke a matsayin kuyanga (Saɗaka) shiyasa mahaifinki ko mahaifiyarki ba su taba miki maganar aure ba ko wani ba, sun maida hankali kan karatunki da kuma ingantacciyar rayuwar da za ki samu, duk wanda yai miki maganar aure ko so ki fada masa cewar ke matar aurece, ban ce ki yi ta tallata Zain ba amman ki tallata aurenki kuma ki kare mutumcin”