← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 93

Sashe 53

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kuka tai sosai har sai da ta gode Allah bata taba jin zafin rabuwa da yar'uwarta irin yau ba, tashi tai ta maida hotuna sannan ta shiga bandaki tai wanka ta fito ya shirya cikin wani koren yadi mai kyali, ta nufi freezer dake dakin ta bude ta dauko grapes ta zauna bakin gado tana ci, sai kuma ta jefar da plate din ta fashe da kuka. Tana jin wayarta na ringing taki ta duba har ta gaji da ringing ta katse a haka aka jera mata missed calls sai da taga dama sannan ta nufi inda wayar take ta dauka, ganin Zain ne yasa ta share hawayenta ta dauki wayar ta kara a kunnenta....

Yana katse kiran sai ga text ya shigo wayarta.

*Ki same ni GRA Ali Gusau road yanzu*

Ta gumde baki kamar mai tunani, sai kuma tai saurin waje wayar ta bude wardrobe ta dauko wasu kayan ta saka, sannan ta kira Fauziya.

“Yanzu Zain yace na same shi a gidansa da ke gra”

“To kije mana, amman miyasa ya nemeki?”

“Nima ban sani ba, amman zan je da turaren nan, da na kiraki kawai ki zo please”

“Amman kina ganin ya dace a yanzu?”

“Yes shi kadai yake zama a gidan be cika zuwa ba ma, sai idan wani abun ne mai muhimmanci saboda yana kai takardunsa, can da wasu abubuwa, idan kuma naga ba shi kadai ba ne sai na fasa”

“Eh to haka yayi Allah bamu sa'a, daman tuntuni ai sai nace ki gwada turaren kika ki”

Bata kara ce mata komai ba, ta kashe wayar ta saka a jakarta ta dauki makullin dazu ta bude drawer ta dauko wani turaren kwalba mai tsananin kamshi, dake cikin kwalbar magani ta saka a jakarta sannan ta rufe gurin ta dauki mayafinta ta yafa ta fito rike da keys din mota, ta nufi part din Dada. Wannan karon a falo ta sameta zaune ana matsa mata kafafu, da far'a ta shiga tana gyara handbag din dake rataye a kafadarta.

“Dada zan fita”

Dada ta waigo ta kalleta

“Ina zaki je?”

“Zain ya kirani yanzu yace yana nemana, wai na sameshi a gidansa a Gra”

“Lafiya?”

“Nima ban sani ba, wai wata magana yake son mu yi”

“Amman ba za ayi a gida ba sai kinje can?”

“Ina ganin maganar tana da muhimmanci sosai dan ya fada min baya son kowa yaji, karna fadawa kowa idan zan fita, kema dan karki nemeni baki ganni ba ne”

“To Allah ya tsare a kula kin ga ana kusan magariba”

Dada ta yi murmushi tana jindadi a ranta duk da bata san dalilin kiran ba amman tana jindadin da har shi ya nemi Hameeda ta zo da kanta. Hameeda ta juyo ta fito tana Murmushi.
Da kanta take driving tana jindadi kamar an mata kyauta, ba dadin kiran da Zain yai mata take ji ba, mission din da take da shi akansa take ganin kamar ta kama hanyar nasara. Tun da ta hango gate din gidan abude ta tabbatar da ya rigata isa kenan, gidane plate mai kyau, ko ina tsab kamar ana zaune a cikinsa babu inda yake da datti ko kazabta kasancewar ya dauki mai gyara masa gidan kullum, a gidan yai kudurin zama da Haleema amman Mai Martaba ya hana shi yin nisa da shi, a dole tasa ya zauna a cikin gidan sarautar. A kusa da inda ya aje motarsa ta aje tata, ganin motarsa dai ya tabbatar mata da shi kadai ya zo kenan, it can be possible ya zo tare da Ibrahim suka shigo mota daya, tissue box ta dauko ta ciri guda uku ta bude turaren ta zuba a jiki ta saka a jakarka. Sannan ta fito ta nufi main door.

A falo ta same shi zaune yana jiranta, be dago ya kalleta ba, har ta gama kallon falon wanda hakan ya tabbatar mata da shi kadai din ne, daga inda take kokarin zaunawa ta fahimci bacin da ke fuskarsa, sai gabanta ya soma faduwa, wani nisan zango numfashinta yai ya dawo lokacin daya dago ya kalleta fuska kamar ance masa Mai Martaba ya mutu.

“Hameeda ke kika shirya duk wannan ko?”

Ta masa kallon rashin fahimta, tana saka hannunta a jaka. Sai ya taso ya nufo inda take.

“Kika nemi Fake parents suka tsaya akan sune iyayen yarinyar kauye nan ko? Saboda kawai ki saka Anty Ummi cikin matsala”

Kamar an zuba mata ruwan zafi haka taji saukar maganarsa a kunnenta, sai tai hanzarin cirs hannunta daga jaka ta tashi tsaye tana kallonsa.

“Ban gane ba? Wace yarinya?”

“Kin san komai don't you dare pay a game here, idan kina son kwanciyar hankali da zama lafiya ki fada min inda yarinyar nan take, idan kuma ba kiji ba duk abunda zai biyo baya ba zai miki dadi ba”

Ta fara hawaye gumi na karye mata.

“Ni ban san komai akai ba, ban san mi kake magana, mi aka ce na yi wannan karon?”

“Ba cewa akai kin yi ba, kin aikata din ne wannan karon”

Tayi baya baya shi kuma yana nufar inda take, sai tai saurin juyawa, ganin hakan yasashi hanzarin rikota ya juyo da ita, sai akwai ta dursuna masa tissue din a hannacin da gefen fuska, kwace fuskarta yai ya rokota da mugun karfi ya jefarda da ita jikin center table, kanta ya bugu da glass table din dake gurin nan take sai jini.

Wani irin nauyi yaji kansa yayi hancinsa kuma da mugun yaji, girgiza kan yai sai yaji jiri na dibanshi, baya baya yai ya zauna saman kujera yana fashe hancinsa, sai kuma taji abu ya sauko masa har tsikar jikinsa sai da ta tashi, biyu biyu yake ganin duk abunda ke falo kamin wani irin desires mai karfi ya sauko masa wacce be taba jin irinta ba a rayuwarsa.
Rumtse idonsa yai gam ya matse kafafunsa sosai, ji yai he can't control himself hakan yasa shi saurin tashi ya nufi bedroom dinsa ya turo kofar duhu na rufe masa ido.
[3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *Masu karanta min novel basu biyaba da masu sharing Novel dina, Allah ya muku yadda kika min. Idan kina son biya ki turo 300 ta 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, sai ku turo da shaidar biyan ta wannan number 08036126660, ko kuma katin MTN na 300 ta wannan number 08036126660*

39

Tana jin lokacin da ya fita sannna ta sauko daga kan gadon ta shiga bathroom ta wanke fuskarta ta sauko kasa.
Daidai inda ya aje indomie be ci ba, ta tsaya tana kallonta, kamin ta tabe baki ta dauke plate din ta nufi kitchen da shi, kayan data bata da wandanda ya bata ta hada guri daya ta wanke, bayan ta gama ta gyara kitchen ta fito ta sake gyara falon, ta saka air freshener. Sannan ta zauna a falon for a while sai kuma ta tashi ta koma dakinta, a ciki tai magariba da isha'i sannan ta saka kayan bachi ta kwanta saman gadon zuciyarta cike da kunci da kuma tunani kala kala.

*** *** ***
Can cikin bachinsa mai kama da suma ya rika jiyo kukan wayar da be tantance na wace wayar ba ne, yana kokarin bude idonsa yaji sun masa mugun nauyi, hakan yasa shi relaxing yaja numfashi ya sauke a hankali sannan ya bude ido. Yes dakinsa yake but he can't remember abunda ya kawo shi nan ba, yana kallon kansa ya ganshi naked.

“Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un”

Ya furta da sauri tare da tashi zaune, sai a yanzu ya lura da inda yake zaune, kasan carpet yake zaune, amman an turmuza komai na dakin kamar anyi fada, Especially ma bed din. Kukan da yake ji dazun na waya yaji ya karu, saurin tashi yai ya bude bathroom ya dauko bathrobe ya saka sannan ya nufo hanyar falon. A nan ma an bata wasu abubuwan, a lokacin ya tuna da abunda ya faru tun farkon shigarsa gidan. Dafe kansa yai ya ya jingina da kofar.

“Hameeda, yarinyar nan duk yadda aka yi kuskuren haihuwa akai ba zuri'ar gidanmu ba ce”

Ya fada a hankali yana mamakin yadda lamarinta keta ta azzara.

“Me kike so kuma wannan karon? Saboda na gano gaskiyarki ne kika min haka ko kuma you up to something?”
Chapter 53 · 0% Book details