← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 93

Sashe 59

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk suka amsa da to suna mai bashi girma da nuna tsantsar biyayya, biyu suka tafi biyu suka tsaya suna cigaba da gadin kofar. Cikin ya dawo amman sai ya kasa zama zuciyarsa nata masa zillo kamar zata fito, gurin windows ya nufa ya tsaya, yana kallon yadda take kada gorar duman dake hannunta, be san lokacin da murmushi ya kubuce masa ba wanda ya bayyana fararen hakoransa, ba zai iya fadar dalili daya dake saka zuciyarsa son kasancewa da Hafsatu manga ba, baya iya auna yadda farinciki da annashuwa ke ziyartar zuciyarsa a duk lokacin daya ganta, be san dalilin dake hana shi sakewa da walwala idan bata kusa shi ba, sai dai yafi alakanta hakan da tausayinta da yake. Yana kallon yadda suka saka ta gaba sai kuma ya juyo yana kallon kofar ya gagara zama, kamin su shigo da ita duk yabi ya matsu. Ana taba kofar falon gabansa yai mugun faduwa, har ciki suka shigo da ita ya daga musu alamar sun gama nasu, sai suka juya da sauri suka fice.

Ita kan kanta na kasa bata daga ta kalli kowa ba, sai dai taji kamshin turaren data sani wanda bata iya shaidar wanene mai shi, tsoro duk ya kamata tana ta sauraren a a karanta mata laifin da tai da kuma irin hukuncinta. Karasa yai kusa da ita ya risina ya leko fuskarta sai yasa hannunsa ya daga kanta ta fuskance shi, hawayene ke sauka a idonta, hawayen da yake jin saukarsu har cikin zuciyarsa. Ya kasa ce mata komai, yana ta jiran tai magana ko da nuna masa wata alama ta sannaya amman ba ko daya. Ta rame sosai kamar ba ita ba, amman kuma ta ciro ta bangaren hallittarta fuskarta ma ta nasa girma aai dai ba sosai ba. Hannu ta kai ta shafa rigarsa, hannun ya kama ya rika sai yaji wani irin sanyi ya ratsa nasa hannun, saurin fisge hannun tai tana yarfawa saboda zafin data ji sakamakon raunin dake hannunta.

“Kin ganene Mama?”

Ta gyada kai, sai kuma ta fashe da kuka ta rumgume masa kafafu. Jikinaa yai sanye yaji wani abu marar dadi yana zaga zuciyarsa. Dago kanta tai sai ya zauna a gurin ya zaunar da ita kusa da shi ya sake rika hannunta yana dubawa.

“Miya samu hannun”

“Bulal... La”

Ta amsa cikin kuka. Kwanto da kanta yai jikinsa sai ka kara rushewa da kukan, shi kuma ya lumshe ido ya faga kansa sama yana daukar da aje Numfashi a hankali.

“Daman ita ce wacce ka zo nema? Yarinyar da aka kama Anty Ummi saboda ita? Ita kanta Anty Ummi na san baka fada mata gaskiya ba da ba zata barka kazo neman wannan annobar ba”

Hafsatu manga tayi saurin tashi, Zain kuma ya bude ido yana kallon Farhat dake tsaye kansa. Wata uwar harara Farhat ta watsawa Hafsatu manga sai ta juya da sauri zata fice Zain yai hanzarin rikota, jikinta har wani rawa yake kana ganinta kasan a firgice take.

“Shiiiiiiiiiiiiiiiiii”

Ya furta tare da saka hannunsa biyu ya rike fuskarta.

“Rufe idonki”

Ta rufe.

“Ja Numfashi a hankali...”

Taja

“Sauke”

Ta sauke. Haka yai ta fada mata tana yi har sai da ya tabbatar natsuwarta ta dawo jikinta sannan yace ta bude idon. A hankali ta bude babu Farhat a gurin daga ita sai shi ne.

“Zat Zat kaje da ni can inda kake kaji, bana son nan dukana suke sosai basa da imani”

Ya gyada mata kai.

“Saboda ke na zo garin nan Mama, dake zan koma ba zaki sake nisa da ni ba”

“Yanzu zamu tafi?”

“Aa sai Sarki ya bani ke tukuna”

“Ba zai bada ba, basa bari aje ko'ina”

Ta fashe da kuka, sai ya kai hannu ya shafa fuskarta.

“Zai bari, ni zan nemi haka, je ki cigaba da aikinki anjima za a kawo ki nan”

Ta share hawayen idonta sannan ta nufi kofar har ta bude sai kuma ta juyo ta kalleshi idonta na cika sa kwalla.

“Karka tafi ka barni”

“Da ke zanje”

Ba dan ta gamsu ba ta saka kai ta fice. Shi kuma ya sauke ajiyar zuciya yana jin babu dadin da be san dalili ba, dakinsu ya nufa sai ya samu Farhat zauna bakin gado tana sharar kwalla. A gabanta ya tsaya yana kallon fuskarta ita kuma ta gagara dagowa ta kalleshi sai wasa take da yatsunta, ba zata iya fadar abunda ta jike ji a yanzu ba, iyakar abunda ta sani taji babu dadin lokacin data ga Zain da Hafsatu Manga, rashin jindadin kuma bata san na minene ba, da gaske na bakincikin abunda ya faru da Anty Ummi ne ko kuma wani daban izuwa yanzu dai bata iya furta ko daya daga ciki, sai dai ranta ya sotsu da ganin yadda yake lallaba Hafsatu Manga abunda be taba mata ba tun da ta shigo gidansa.

“Kuka kike yi?”

Ta dago ta kalleshi da zimmar fada masa bakar magana sai kuma taji yai mata kwarjini sosai gashi ya tsareta da manyan idonsa. Dauke kai tai ta tashi tsaye ba dan tasan inda zata ba, sai ya riko hannunta ya janyota zuwa kirjinsa.

“Minene na kuka fada min? Wata maganar nai marar dadi ko me?”

Tana kokarin kwace kanta daga rumgumar da yai mata, sai duk taji kunyar kanta, kunyar hawayenta da ya gani hawayen da ita kanta bata san na minene ba.

“Ni gida nake so gurin Mamana”

“Idan na samu yadda nake so, zamu koma gida gobe inyaso idan kin hutu sai muje mu gansu haka ya miki?”

Ta kasa cewa komai, ba karya tai ba tayi mamarin mahaifiyarta sai dai kuma a yanzu ta furta hakan ne kawai saboda ta kwaci kanta, sai dai har cikin ranta tana jin zaman gurin da suka soma yanzu yanzu ya fitar mata a rai. Duk irin kukuwar da take na fisge kanta daga gareshi be saketa ba sai ma kara rumgumeta da yai a kirjinsa, hakan yasa ta fashe da kuka.

“Am sorry”

Ya furta zuciyarsa kuma tana ta sosuwa da yanayin da ya ga Hafsatu manga........

Taya zai Zain zai fita da Hafsatu manga? Anya zai samu nasara kuwa? Zamu ji a cikon page din anjima domin wannan rabin page din ne. Ku rika hakuri da typing error. 🙏
[3/17, 8:36 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 42b

Sun dade a gurin tsaye har sai da yaji ana kiran sallah magariba sannan ya saketa ya shiga bandakin yai wanka yai alwala. Cikin dakin yai sallah ita kuma ta fita falo ta yi nata sallah. Bayan ya gama ya fito cikin wasu kalar sufafin wadanda suka fito da kyauta da kuma kwarjin dake fuskarsa. Kusa da ita ya zauna yana kallonta.

“Ga abinci nan ana jera me kike so ki ci”

Sai kawai ta tashi ta nufi dakin daya fito ba tare da tace da shi komai ba. Be jin zai ci abincin shima dan haka ya tashi ya koma saman kujera ya zauna. Misalin tara saura Sarki Idrissa Abdourahmane Idrissa ya aiko kiran Zain, dole tasa Zain ya shiga ciki ya cire kananan tufafin dake jikinsa ya saka manya wato riga da wando na shadda sannan ya dauki hulla ya dora sama. Ko ba komai yasan zasu kara masa kalama Mai Martaba ma yana yawan fada masa ya rika saka manyan kaya saboda mutunsa da kuma na masarautarsa musamman idan wani gurin ya tafi.

Tunda ya fito daga gurin dogaran da suke gadin kofar suka rika take masa baya har suka isa wani kebantattacen guri da sarkin ke zama yana hutawa. An gyara gurin ya kawata shi da kayan kawa na gargajiya masu ban sha'awa da matukar burgewa. Zain ne akwai ya shiga ciki yayinda dogarawan suka tsaya a waje. A kujerar dake fuskarsa ta Sarkin Zain ya zauna suna sake gaisawa a karo na biyu. Bayan sun gama gaisawar ne Sarki yake gabatar masa da Yarima Hamma wato dan sarkin wanda yake tare da shi a yanzu. Shi da Zain aka rasa wanda zai bude baki yai ma wani magana a cikinsu, shi yana ganin kamar Zain yafi dacewa ya gaishe tun da shi ya shigo masarautarsu shi kuma Zain yana ganin kamar kankanci ne ya gaishe da dan wani sarkin yana dan Sarki. Kallo daya Zain ya masa ya dauke idonsa, shi ma kuma tun shigowar Zain na farko be sake kallonsa ba. Suna haka Wata babban mace ta shigo dattijowa Hafsatu manga na biye da ita dauke da tray mai cike da kayan marmari. Tun da shigo idonta ya sauka akan Zain sai ta kasa dauke idonta shi ma kuka yaki ya kawarda idonsa daga kallon hawayen da suke zuba a idonta. Bata kula ba har ta tashi tuntube.

“Ke mahaukaciyar ina ce? Baki ganine?”

Yarima Hamma ya katsa mata tsawa, ganin tana kokarin fado masa. Abunka da wacce ke jira sai kawai ta fashe da kuka ta aje tray a gaban shi yayinda Dattijowar ta aje dayan a tray a gaban Sarki. Tsaki Hamma yaja ya tashi ya fice daga gurin. Dattijowar ta katsa mata tsawa.

“Rufe baki”

Zain ya kalli Dattojiwar ya ce

“Tayi kankanta da aikin da kike sakata, gata kyakkyawa, da Mai Martaba zai min karamcin bani ita a matsayin Kuyanga da zan fi kowa farinciki”

Sarkin ya kalleshi yana dariya.

“Yarima kenan, wannan ai tayi maka kankanta da kuyanga, akwai su da yawa idan kana so, sai a dubo maka wacce tafi wannan gwari idan ma matasan kake so”

“Wannan din dai nake so ranka ya dade, Masarautar Rishim bata marhabun da bayi saboda tana ganin kamar zamanin haka ya wuce, duk bawan da ka gani a gidan to am dauke shi aiki ne ko kuma dan gado ne tun kaka da kakannin, wannan yasa nake son idan har an bani ita na shiga da ita a matsayim Kunyanga nasan Mai Martaba ba zai zargeni ba musamman idan yaji kai ne kai min kyautar ta”

Sarkin yayi murmushi irin nasu na manya, sannan ya kira sunan Dattijiwar dake jera masa kayan marmari a dan karamin tebur dake gurin.

“Jekadiya”

Ya fadi zauna tana daga nasa hannu.

“Allah ya taimaki sarki”

“A shiga da ita a anko masa ita a Kuyanga, zai yi kuzuri da ita a matsayin tsarabar mu”
Chapter 59 · 0% Book details