Sashe 33
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Allah ya taimakeka, dukan dan Adam ajizine, bana cikin daya daga cikin iyalanka amman wanda ya aje ni agidan nan yana da muhimmanci a gareka, dukan abunda Yarima ya aikata jiya laifinane domin ban fada masa cewar ina da ulcer ba, sai yai zato ko wani abun ne, hakan yasa ya kira ta ya tambaya ko akwai abunda ya faru, hakan yasa ta fasa kuka ta juye masa magana, amman bayan wannan babu abunda ya faru, Zain mai tsananin biyayya ne a gareka kuma mai jin nauyinka wannan ya hana shi yin musu maka abunda aka fada akansa, idan kuma Mai Martaba be yarda da magana ta ba, ina son ya bani alkur'ne na rantse masa da shi ko kuma ita Hameeda ta rantse akan anyi haka.
Mai Martaba kai shugaba ne mai adalci da sanin ya kamata karka yanke hukunci bisa ga fushi, idan har zaka yanke hukuncin ka yanke min duk hukuncin daya dace da ni amman ban da na saki, karka cilastawa danka yin abunda Allah baya maraba da shi, na hadaka da girman Allah Mai Martaba ka tausaya mana.
Ina neman afuwarka akan abunda ya faru, ko wane adam ajizine dukanmu masu laifi ne, kai ubane a gareni sakancewar kao shugaba ne mai adalci da sanin ya kamata, kuma ina mai maka alkawari hakan ba zai sake faruwa ba”
Idon kowa yana kanta, bama kamar Hameeda da bakinta ke sake tana kallon ikon Allah, Zain kuma yana kallon tana yin abunda ba zai iya ba, domin indai shi zai kare kansa sai dai Mai Martaba yai masa abunda duk zai masa amman ba zai iya ba, abu na biyu kuma kowa na mamakin yadda ta tsoma baki ba tare da Mai Martaba ya bata umarnin hakan ba.
Kallonta Mai Martaba yake, tun da ta fara magana ya yaba da hankalinta, a natse take fitar da duk wani kalamin dake fita daga bakinta tana kokarin fahimtar da shi abunda sauran suka kasa, gata sai hawaye take gwanin tausayi.
“Karya take wacan wacan yarinyar munafuka ce au laiye zaki yi ki karyatata”
Cewar Dada tana jin kamar ta taso tazo ta daketa
“Zai iya zama gaskiya mana, ai kin san Zain ba zai iya musa abunda aka cewa Mai Martaba ba, kuma kullum Hameeda ce take kawo kararsa akan ya mata abu, amman shi be taba kawo kararta ba, kuma be taba musa maka ba”
Dada ta kalli Hajiya Hadiza wacce ta gama maganar yanzu.
“Ee daman can son Hameeda kike ba ni na sani, duk da goyon bayanki ya auro wannan tsitattaciyar magen, to Wallahi ta Allah ba taku ba”
. Mai Martaba yai gyaran murya a karo na biyu sannan ya ce
“Dukan abunda zai tashi hankalin iyalaina bana sonsa, babu ta inda mata ta fi yar'uwa, dan haka bana son ka bar zuciyarka ta yaudare ka fifita matarka akan yar'uwarka, abu na biyu kuma ban jidadin abunda Hameeda tai ba, dan bana son auren ba shi ke nuna duk abunda kika yi ko kika ce na cilasta masa abunda ba zai kawo kwanciyar hankali ba, fushi gaba zargi zargi duk ina son a aje shi a cikin iyalin nan, Matar Muhammad Yayarki domin ta auri yayanki dan haka kar na kuskura na ji kin mata rashin kunya, ba ke ba kuma kowa a cikinku ya ce zai nuna rashin tarbiya a gareta zai tsaba masa, ita kuma ina son ta kama mutunci da girmanta karta kuskura shiga sha'anin da bana nata ba, kowa ya rike girmansa da matsayinsa. Zain ya girme ki Hameeda be kamata ki masa karya ba, karya tana daya daga cikin abunda na tsana, karya tana zubarda mutumcin mutum da kimarsa, karya kuma ba abu ne da akasan wanda ya girma a cikin gidan nan da yinsa ba, dan haka ki bashi hakuri da matarsa.
Zain..”
Mai Martaba ya kirashi a natse sai ya dago ya kalleshi tare da amsawa.
“Kai mai yanke hukunci, ina fatar nan gaba idan haka ya faru kai zaka yi hukunci ba ni ba, ka kai matsayin da zaka yanke hukunci ko bana nan ko kuwa akan abunda ya shafi masarautar nan ne balle kuma abunda a shafi iyalina, Allah ya maka albarka”
Wannan furuci da Mai Martaba yai ga Zain be yi ma Hajiya Maryam da Hajiya Zarah dadi ba, Dada kan kasa cewa komai tai ba dan komai ba sai dan hukuncin da Mai Martaba ya yanke be mata dadi ba, ba ta son cilasta masa ya cilasta ma Zain sakin Farhat nan, amman tana nan haushinta. Dan haka sai ta tashi ta bar falon.
Hameeda bata da damar musa masa tace ba haka bane, hakan kuma da Mai Martaba yai ya nuna ya aminta da kalaman Farhat saman da nata. Sai da tana jin kamar akwai kaskanci a tare da ita idan har ta bawa Farhat hakuri, amman ya zatayi umarnin mai martaba ba bata da wata dabara bace ta bi.
“Dan Allah Yarima kai hakuri”
Be amsa mata ba, sam be ma kalli inda take ba, sai ta kalli Farhat tana wani irin dauke numfashi kamar zata mutu, saboda bakincikin bawa Farhat hakuri.
“Ki... Yi... Ki... Yi haku...ri...”
Farhat ta dago ta kalleta.
“Ba komai na yafe miki”
Hajiya Hadiza tayi murmushi.
“Mun gode Mai Martaba Allah ya kara girma da lafiya, daman ni nasan Zain ba zai ce haka ba, Allah ya tsare gaba”
Da hannu Mai Martaba yai musu alama da su tashi su bashi guri sai kowa ya tashi ya fice, ban da Hajiya Hadiza wacce ta dauko masa sabuwar fira daman yau a dakinta ya wayi gari.
Suna shigowa part dinsu Zain ya maida kofar falon ya rufe yana kallon Farhat data hade fuska kamar bata taba murmushi ba.
“Da ya baki qur'an ki rantsen fa?”
“Ai ba zai bani ba, domin manyan mutane basa daukar irin wannan hukunci sai ya zama dole, so kaga Mai Martaba ya yarda da ni sama da Hameeda”
“Yarda da yai dake a yanzu ba shi yake nuna ki sake yin haka a gaba ba”
Ya fada as he command her.
“Shi kadai ka iya, ni kazo nan kana min fada amman yanzu kanwarka take kokarin cin zarafinka a gaban Mai Martaba”
“Ban iya munafurci ba”
“To ni na iya sa ido kai kallo”
Ta fada tana harararsa, har tayi gaba sai ua rikota ya dawo da ita da karfi ya matse gashin kanta.
“This will be the last time da zaki harareni”
Wani irin kara tai tana kokarin kwatar kanta amman ta kasa, har sai da yaga dama ya jefar da ita saman kujera.
*** *** ***
Bayan ta gama hada breakfast su Amal suka ci suka wuce islamiya, ita kuma ta shiga ta shirya cikin bakar abaya ta dauko jakarta ta fito falo inda Hafsatu manga take zaune tana jiranta, duk ta bata fuska kamar ba ita ba. Zaunawa Anty Ummi tai saman kujera ta kama hannun Hafsatu manga tana sauke ajiyar zuciya.
“Baki son zuwa gidanku ne? Zan kaiki ne saboda ki samu kwanciyar hankali, nima na samu Zain ma ya samu, bana son fadan da kike da Amal kuma bana jindadin yadda Zain yake shige miki komai zai iya faruwa, sannan na kasa natsuwa da ke a gidan nan, ke kanki nasan kina son iyayenki...”
Ta tsayarda maganar sakamakon ringing din da wayarta ke yi, picking tai ta kara a kunne.
“Hello Ummu, Subhanallahi gani nan zuwa”
Tana aje wayar ta kama hannun Hafsatu manga suka fice, bata zame ko ina ba sai gidansu, wato family house dinsu, gabanta sai faduwa yake saboda tasan ciwon Abbansu a duk lokacin da asmarsa ta tashi bata masa da kyau.
Sai dai a yadda ta tararda yan'uwata da kuma Abbansu yasa hankalinta ya kwanta, domin ta sameshi zaune har ana dan taba fira da shi, zubewa tai kasa tana gaisheshi Hafsatu manga kuma ta tada kai sama tana kallon falon da aka narkawa dukiya, da dai dai take kallon hotunan dake manne a falon har ta kai kan hoton mutumen data taba gani a Jafatu Mall har ta dauko masa takardarsa data fadi.
Wayarsa Anty Ummi ce tai ringing sai ta dauka tai yar magana, sai kuma ta tashi ta kama hannun Hafsatu manga.
“Waccece wannan?”
Hajiyarsu ta tambaya.
“Yar makociyarmu ce”
“Allah sarki”
Daga haka Anty Ummi taja hannunta suka fice, motarta ta shiga suka kama hanyar samaru suna isa ta fito mota wani saurayi ya fito, bayan sun gaisa ta mika masa Hafsatu manga.
“Ka tabbatar a hannun sarkin garinsu ka kaita, idan kuma baka samu kowa ba ka dawo da ita, kar wani abu ya same ta”
“Karki samu matsala, za'ayi yadda kika ce”
Yana fadar hakan yaja hannunta sai ta fashe da kuka.
“Anty na daina bana son zuwa ba zan sake biki miki Amal ba”
Tsaye Anty Ummi tai tana kallonsu zuciyarta na sosuwa da tafiyar da Hafsatu manga zata yi, sai dai bata yi komai ba har ya sakata motar ya kama hanya. Sannan ta bude motarta ta shiga ta kamo hanyar gida.
**** ***** ****
FLASH BACK...
Tana jin motarsa ta yi saurin jera kulolin abinci a dinning, ta shiga bedroom da sauri ta dauko dankwalinta ta daura ta fito tana dariya ta daukin dawowar mijinta. A bakin kofar falo suka ci karo da shi yana kokarin shigowa ita kuma tana kokarin fita.
"Sannu da zuwa"
Ta furta tana dariya kamar yadda shima yake dariyar yana kallonta.
"Yauwa ya gidan?"
"Lafiya kalau"
Ta karbi jakar kayan da ke hannunsa, tare suka karasa cikin falon, ya cire hular kansa ya mika mata ya bude aninin rigar shaddar da ke jikinsa ya zauna saman cushion yana sauke gajiya.
"Kai Al-hamdulillah babu inda ya fi gida dadi, duk inda nake bana jin sakewa sai na dawo gida"
"Al-hamdulillah dai an dawo lafiya ya ka baro Lagos?"
"Lagos lafiya kalau"
"Ka huta ka yi wanka ga abinci can yana jiranka"