Sashe 42
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin sauri ya koma cikin Napep din matar dake bayan Napep din ta matsa mata ta shiga ko ba komai Zain zai je ya dauketa a gidan kuma ba zata iya tsayawa a hanya ta na aman jini ba, impact bata san abunda ke damunta ba, this is the second time da tai aman jinin bayan wanda tai a darenta na farko, tana bukatar zuwa asibiti. Kamin su isa kofar gidan Anty Ummi Farhat duk ta bata masa Napep da jini ta wahala sosai kamar a darenta na farko, duk wanda ya ganta a haka sai ya tausaya mata, har cikin gidan ya shiga da ita bayan Malam Adamu ya bude masa gate ganin halin da take ciki, a harabar gidan ya tsaya da Napep, matar dake baya ta rika Farhat tana ta fito da Farhat da tufafin jikinta suka gama lalacewa, tafiyar take tana rangaji matar na rike da ita har ta zaunar da ita bakin kofar tana mata sannu.
Malam Adamu yazo yana tambayar ba'asi sai mai Napep din ya fada masa, suna tsaye gurin motar Zain ta kunno kai cikin gidan. Kusa da inda suke tsaye ya faka motar ya fito yana kallonta, ita kuma taki ta daga kai ta kalleshi.
“Miya faru”
Mai napep din ya fada masa a halin daya sameta da kuma inda ya dauko ta, Malam Adamu ya kara da nasa yana fadar lafiya kalau ta bar gidan.
Hannunsa yasa ya rikota
“Taso muje”
Cikin gidan ya shiga da ita, mai napep din ya wuce. Baba Asabe suka samu zaune a kasa tana kuka.
“Lafiya Baba Assabe?”
“Hajiya aka kama yanzu nan polisawa suka shigo suka kamashi”
“Saboda mi?”
“Naji dai suna cewa wai ana zarginta da satar yarinya”
Hafsatu manga ce ta fado masa a rai, domin ita kadai ce yarinyar da Anty Ummi ta rika, amman su wa suka saka a kamata?
Hannunsa daya yasa ya sake rikata ya shiga da ita bedroom din Anty Ummi har cikin toilet ya sakata.
“Cire kayan jikinki”
Yaja mata kofar toilet din, wardrobe Anty Ummi ya nufa ya bude ya dauko mata gown, ta kusan minti talati a bandaki har sai da ya unkura zai shiga sannan ta bude ta dauko leko kanta.
“Bani riga”
Dauka yai ya jefa mata, ta koma ciki ta saka sannan ya fito ta dauki mayafin Anty Ummi ta saka, sannan suka fito tare. Tun da suka kamo hanya be ce mata komai ba, itama bata kalli inda yake ba.
A kofar gate din gidansu ya faka motarsa, sai ta bude ta fita sai gata ta zube kasa ba karfi. Bude gefensa yai ya fito ya rikata ya shiga da ita ciki falon ya zaunar da ita saman kujera. Tayi expecting zai yi mata nagabar dalilin fitarta ba tare da izininsa, sai taga kawai ya juya ya fita ba tare daya ce da ita komai ba.
HAFSATU MANGA POV.
“Miye alakarku da wannan yarinyar?”
Ya tambayi matar dake tare da Hafsatu manga,
“Ni ba kowa ba ce a gareta, amman kanwar mahaifinta ta bani ita akan a sama mata aiki, kwanaki na kawo Hindatu sai Hajiya ta ce ta mata girma shine aka ce bari a kawo mata wannan, amman tukuna bata balaga ba an dai mata allura?”
“Allurar mai?”
Wannan karon Zainab ce ta tambaya.
“Idan an kawo mana wadanda basu balaga ba, Hajiya tana sa ayi musu allura da zaisa jikinsu ya inganta suyi saurin girma saboda Mutane suna fada cewar yara idan sun balaga a gidansu suna musu kazanta wasu ma basu san yadda zasu kula da kansu ba”
“Amman baya cutar da su?”
Tayi yar dariya.
“Baya musu komai, ai likita ne ma yake musu alluran, sai dai ita Manga daya aka mata, sai an kwana biyu sai a kara mata wata”
“Okay”
Dsp Auwal ya fada sannan ya tashi yana amsa waya. Zainab kuma ta tashi ta shiga ciki ta dauko mata two thousand ta bata na hawan Napep matar ta karba tana da murna da godiya. Tana tashi tsaye Hafsatu manga ta tashi tsaye zata bita sai ta daka mata tsawa.
“Ke zauna, ba aiki aka kawo ki ba, Hajiya nuna mata aikin da zata yi”
Komawa tai ta zauna tana kuka.
“Je ki gyara Kitchen kamin na tashi sai ki zo ki gyara falon”
“Tashi aka ce”
Matar ta sake daka mata tsawa, da sauri Hafsatu manga ta tashi da sauri ta nufi inda Zainab ta nuna mata tana kuka. Tana shiga ta zauna jikin freezer ta kara fashewa da kuka.
Sai da matar ta wuce sannan Zainab ta tashi ta nufi dakinta ta bar Dsp a dayan bangaren yana amsa waya, bayan ya gama ya nufi kitchen domin ya lura da lokacin da aka wuce da Hafsatu manga.
“Hafsat”
Sai ta dago ta kalleshi cikin kukan.
“Minene? Kin ganeni?”
Ta gyada masa kai tana sharar kwalla. Zaunawa yai kasa kusa da ita ya dauketa ta dora saman kafafunsa.
“Fada min ya aka yi kika zo nan?”
“Wannan Anty Ummi ce ta dauke ni ta ba wani ni, ya saka ni cikin mota ya tafi da wani can wani gari ya bani wani abu na sha nai bachi, da na farka ya sake bani na sake bachi, sai ya kawo ni gurin wata mata katuwa mai gilashi tasa aka min allura, sai kuma suka kawo ni nan”
Ta fada cikin muryar kuka tana murza idon, hannunsa yasa yana share mata hawaye.
“Wannan matar kin santa?”
“Aa ni ban santa ba, kuma karya take da tace kanwar Baba ta bada ni karya take, wannan Anty Ummi ce ta bata ni”
“Wacece Anty Ummi?”
“Wannan muguwar matar, yayar Uncle”
“Wane Uncle?”
“Zat”
“Hafsat ba baki magana ba? Ya akai yanzu kike magana”
Ya fada yana saka hannunsa cikin bakinta yana duba halshenta.
“Nima dai kawai naga ina magana”
A yadda take maganar yanzu kamar ba ita ce ke kukan ba. Yayi dariya yana jan kumatunta.
“Zaki iya gane iyayen?”
Ta gyada kai
“Kin san garinku?”
“Kufawa, amman bana ganewa amman garin an kashe kowa, kuma mutanen suna nan”
“Sato ki Zain yai ko?”
Tayi shiru kamar mai tunani.
“Aa ni ina sonsa wannan matar ce bana so”
Murmushi yai ya tasheta tsaye.
“Tashi mu gyara kitchen”
“Ni ban iya ba”
“Zan koya miki”
Ya fada with smile on his face.
“Dauko ga tsinsiya can ki share sai nai mopping”
“In mun gama zaka kai ni gida?”
Yayi kamar be jita ba, ya fiddo wayarsa daga aljihu ya nemo number Hafsat tare da danna mata kira.
“Hello Dsp”
“Doc kina lafiya”
“Kalau ya Anty Zee”
“Lafiya kalau, kina da wani labari akan yarinyar nan da aka taba kawo miki wacce mata magana mai sunanki?”
“Aa gaskiya tun da ya dauketa ban sake ganinta, kwanaki dai akwai wata cousin dinsa data zo gidan tana ta tambaya labarinta, kuma naji ance ta bata”
“A gurin wa kika ji”
“Gurin aminsa, kasan she's my fiance, to kwanaki da hankalinsa ba kwance ba na masa nagana sai ya fada min”
“Amman miyasa cousin din take neman yarinyar?”
“Nima ban sani ba, amman ta zo tana ta min bincike a nan naji yarinyar ma a hannun yayarsa take”
“Sai da yarinyar nan suka yi”
“Saidawa kuma? How do you know?”
“Gata nan a tare da ni, an kawo ta ga aiki”
“What”
“Yes lokacin da na ce zan yi bincike akan maganar ai ke da Momy hana ni kuka yi”
“Yeah kaga ai be dace ba, ni zai ga laifina kuma babban gida kamar wannan be kamata ace ka shiga ciki bincike ba”
“Ya ci arziki bana garin gusau a yanzu, amman haka ba zai hana na bincike shi ba”
“Amman dan Allah kar sunana ya fito ciki”
“Idan babu hannunki a ciki ai sunanki ba zai fito ba”
“Babu hannuna a ciki, amman Dps ka san Farhat tayi aure?”
“What? How do you know”
“Ni ma dazu naga tayi posting a fb, kasan tana cikin friendslist dina”
Wani irin sarawa kansa yai, har ga Allah be ji dadin maganar ba.
“Amman kin tabbata?”
“Wallahi ita tai posting, bana tunanin kuma hacking din account dinta akai”
“Wata aura?”
“Allah ya mata sakamako, a yadda ta rubuta inda ba karya take ba, Doc Zain ne kasan kuma ya fika komai, kai baka ga post din ba?”
“Ban hau fb ba yau, Doc Zain da muke magana akansa yanzu?”
“Yes shi, amman ni kaina ban san da yayi wani auren ba bayan rasuwar matarsa, sai dai kuma bana tunanin ita zata yi karya da shi”
“Bad news”
Ya kashe wayar, zuwa yai ya dafa kitchen cabinet yana maida numfashi da karfi, sam sam sam maganar bata masa dadi ba, har ga Allah yana son Farhat kuma yana da kudirin aurenta, he was planning idan sun yi one year da Zainab zai gabatar da Farhat da mahaifinsa ya san a lokacin ba zai ki karba masa bukatarsa. But jin wannan labarin ya karyar masa da zuciya. A take ya kunna datarsa ya shiga Fb, sunanta yai searching ta shiga duba timeline dinta, post din ya fara yin karo da shi.
_May the love we express to each other on 10th, always be the first thoughts during any trying times in the future. Finally I'm Mrs Zain Ibrahim Tukur Dan-maliki_
*Got married today*
Haka facebook suka rubuta bayan dan guduntun rubutun da Farhat tai, he feel so hopeless, so shame, so disgrace. Sai a yanzu ya tabbatar da abunda yai mata rashin kyautawa ne, he remember all the good memories they spent together.
“Na gama sharar”
Kallon Hafsatu manga yai amman ba fuskarta yake gani ba, jinsa ne kawai a tare da shi amman tunanisa yana can wata uwa duniyar. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya sake kallonta da kyau.
“Minene?”
“Na gama sharar”
“Okay je ki dauko mopper gata can”
Zuwa tai ta dauko mopper ta mika masa.
“Amman zaka maidani gurin Uncle ko?”
“Baki son zama nan ne?”
“Ka san kai dan sanda ne, kuma ni nafi son Uncle na ji yace zai kaini inda Mamana”
“Karya yake miki, gashi ya siyar da ke an kai masa kudi”
Sai ta bata fuska kamar zata yi kuka.
“Ina mamana?”
“Nima ban san inda take ba, amman zan bincika ta, karki yi kuka kinji?”