← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 93

Sashe 87

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan shekara daya da dawowar, ya samu aiki a babban asibitin paris, kuma ya fara a sa'a domin kuwa sun yaba da kwarewarsa da kuma jajircewarsa, a dalilinsa na son manta da komai da kowa yasa ya maida hankali kam aikinsa, wanda hakan ya kara masa girma da farinjini a gurin turawan, har ta kai babu kamarsa a fadin asibitin, indai kwararen likitan zuciya ne to shine dai a fadin kasar wanda yafi kowa kwarewa da sanin aikinsa, duk abunda yake tarawa yana aiko da shi ne a naija ta hanyar Ibrahim ana taimakon mabukata da gajiyayyu, daga nan Ibrahim ya bude masa foundation.
Ya sake zuwa naija ne bukin Ibrahim da Hafsat, wanda akai a a shekararsa ta hudu da kowa paris, bayan bikin ya kwashe wata daya a gida shi ma kuma daker suka bar shi yai su a naija, bayan ya koma ne kamar shekara biyu Hafsatu manga tai matsa tsaye a rai, sanadin hakan yasa abokinsa ibrahim ya bincika masa ita, sai aka kawo nasa labarin cewar tana cikin Koshin lafiya tana gudunarda rayuwarta yadda ya dace.
Tun daga lokacin Ibrahim yake bibiyar rayuwarta, duk wani abu daya shafeta yana fadawa Zain ba tare da Anty Ummi ta san komai a kai ba.
A ten years da yai a paris sunansa ya zaga ko'ina inda turawan da kansu suke masa lakani da *Craftsman*. Ya jidadi lokacin da ya samu labarin Hafsat bata manta da shi ba wanda hakan ya kara masa sonta fiye da da, ba tare da sanin cewar Anty Ummi ce take tuna mata komai ba, a tunaninsa ta haddace komai a kanta ne, a lokacin da tai masa request a facebook, yayi mamakin ganin girmanta, amman hakan be sa ya amsa mata ba dan a tunaninsa har yanzu tana da sauran lokacin domin yana ganin har yanzu bata san ciwon kanta ba, daga lokacin yai blocking dinta, sai ta koma instagram a can din ma haka yai mata kamar dai sauran account dinsa da take bibiya, ta hanyar Ibrahim ya samu labari lokacin da ta shiga university a Abuja. A lokacin ne ta bude sabon account ta canja sunanta, shi kuma ya kyaleta ba dan komai ba sai dan ya bata damar kallonsa wanda ya san zata so haka. Shi kuma ya bude wani account din yana following dinta, duk wani abu da take yana gani. Ta nan ya samu magana da daya daga cikin kawayenta wato Pearl, shi ya dauki kwangilarta tana fada masa komai akan Hafsat, lokuta da dama tana daukar hotonta ta tura masa ba tare da ita din ta sani ba, kusan dukansu sun sani dan ta fada musu amman ban da Hafsat dan ya bukaci a boye mata ne wanda hakan zai bata damar focusing akan karatunta. And he's happy tana final year babu abunda ya sameta, yaji kishi sosai lokacin daya samu labarin tana abota da MB, sai dai ba shi wani yan cin hana ta, kamar yadda be isa ya cire son ta a zuciyar Raheem ba, ya san tana da kyau da haiba irinta ya mace wacce ko wane namiji zai so ta kasance matarsa sai idan be samu ba.

*** *** ***

Tashi yai tsaye ya bayan ya gama tunane tunanensa ya shiga kitchen ya dafawa kansa Indomie, yana jin nishadi da kwanciyar hankali idan yana cin irin abincin da hafsat ta fi so fiye da komai, wani lokacin yana tuna lokacin da take jera indomie tana cewa gashi nan ga Mamanta ga wane da wane. He used to jerawa kamar yadda take yana fadin gata nan ga shi nan.

He so much worry about her condition amman ya kasa nuna mata kansa duk da yana son ganinta a fili, sai dai kuma yana ganin kamar lokacin yin hakan be yi ba. As he said Misalin goma na safe ya baro kasar zuwa Nigeria, they spend hours a jirgi har yai bachi ya tashi sannan suka iso, at that time isha'i a ake a naija. A Abuja ya sauka, tun a airport ya kira one of her friends ya pearl ya tambayeta ko akwai yadda za'ayi ya Hafsat ba tare da kowa ya ganshi ba.

“Akwai yadda za'ayi na ga PureHeart”

“Gaskiya ba dama, saboda mahaifinta da Momy tun jiya suka zo, kuma Hajiya Asma'u ma tana tare da ita”

“Okay, ki shafa min kanta dan Allah”

“Inshallah”

Sai da yai minti arba'in a garin Abuja yana hutawa, sannan ya hau jirgi zuwa garin Gusau. He feel Nigeria kamar ba ita ba, duk kuwa da kasancewar yana zuwa yana koma a duk lokacin da ya zo yana jin wani yanayi na dabam. Babu abunda ya karu a kasarsa sai ma raguwar cigaba da aka samu, ga zalinci irin na shugabani da karuwar cin hanci da rashawa. Sai dai hakan be taba sashi ya ji baya son kasarsa ba, domin mahaifarsa ce har gobe ba shi da kamarta tun da Familynsa da Sahibarsa suna ciki suna rayuwa.
[4/8, 11:58 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *60*

Yana farincikin zuwansa Gusau bayan tsawon lokacin da ya dauka baya garin, ba sa abunda yasa yake jin wannan zuwa kamar ya fi ko wanne muhimmanci ba. Kowa a masarautar yana farinciki da ganinsa kama daga Mai Martaba da iyalansa har Dada Yalwa wacce bata da ishasshiyar lafiya a yanzu. After spending the night with Hajiya Hadiza suna ta fira ya dawo part din Dada Yalwa.
A dakinta ya sameta tana cin tuwo miyar yakuwa da manshanu, kusa da ita ya zauna yana murmushi ya nasa hannunsa cikin robar wanke hannu ya wanke hannunsa sannan ya kasa cikin tuwo.

“Ya dai kamata na ci abincin kasata kuma tare da babbar mata”

“Babbar matar da ka gudu ka bari?”

“To ba gani nan yanzu na dawo ba”

“Dawowarka tana da amfani Muhammad, ina son nai magana mai muhimmanci da kai”

“Kamar ta me fa Dada?”

Ya tambaya yana aikin auna loma a bakinsa.

“Zain ni da mahaifinka duka muna son ganin aurenka, bamu san ta rai ba, musamman ni da tsufa ya ci ya cinye, Mai Martaba yana son ganin jikansa daga gareka, duba kaga gidan nan duk an kwashe yan mata an aurar da su sai jikoki da ita da kananan kannenka, amman kai ace har yanzu babu jika ko daya kuma babu mata, da kana da mata na san ai dole ka rika dawowa kana ganinmu, yanzu da wannan ciwon ya tafi da ni ai da yanzu sai dai kawai ka tararda gawa”

“Rayuwa da mutuwa duka na Allah ne, ciwo baya nufin mutuwa Dada”

Ya fada cikin rashin jindadin maganarta.

“Na sani, amman indai idan kana kusa zai fi, na san na takura maka a zaman da kai a matanka na baya, a farko Hameeda tana yawan kawo min karar Haleema tana ce min tayi abu sai na dauka gaskiya ne, daga baya kuma sai nai tunanin ko makircin Ummi ne ta aura maka Farhat kuma nai tunanin Farhat din magani tai maka, ashe duk ba haka ba ne, Zain ina son kai aure na sake saka matarka a ido, na karanta mata ko sau daya ne, ina son farincikinka kai da Hameeda, sai dai yanzu na fitar da rai daga na Hameeda, sai dai na ka kawai bani da wani buri a yanzu wanda ya wuce na ga kaima ka kafa taka zuri'ar tlkana rayuwa mai kyau kamar kowa”

Ya kalleta da irin kallon na tausayinsata, ya san gaskiya take fada shi kanshi yanzu yana bukatar auren, kamar yadda ya san Mai Martaba ma yana son yai aure, a tattaunarwa da Hajiya Hadiza a dazu ta fada masa a yanzu Mai Martaba ba shi da wani abu daya wuce na aurensa.

“Dada zan yi aure, indai wannan ne kawai burinki da na Mai Martaba ku kwantar da hankalinku komai zai wuce, zan yi aure inshallah”

Ta zare hannunta daga tuwo tana kallonsa da idonta na tsufi zuciyarta cike da farinciki.

“Yaushe? Allah yasa nan kusa ne ba nesa ba”

“Yarinyar da na ke so, nan da wata bakwai zata gama makaranta, so idan ta gama na ke tunanin zan fara wani motsi a kanta”

“Har nan da wata bakwai Zain? Anya zan kai har lokacin kuwa? Tana ta jin kamar ina kusada kabarina”

“Haba Dada kowama yana kusa da kabarinsa dan Allah ki bar wannan maganar”

“To kan san ita mutuwa ba ka sani ba, ba a sanar maka ba, rayuwa bata da tabbas ko ga yaro balle babba irina”

“Zaki ga aurena har yayana zaki gani da yardar Allah”

“To Allah yasa”

“Amin”

Daga ranar ya saka kansa a tunanin yadda zai showa kan lamarin jikinsa yayi sanyi da maganar Dada, domin Mai Martabaa irinra ya nanata masa bayan kuma Ibrahim ya dade yana masa maganar kusan ya fi kowa matsa nasa shi da Anty Ummi. ga shi kuma baya son ya fitowa Hafsat a yanzu har sai ta kammala makarantarta, sai dai a maganar da Anty Ummi tai masa a yau ma ta kara sashi cikin wani, cox ta fada masa halin da Hafsat take ciki na damuwa da rashinsa.

“Zain ina ganin kamar cutar yarinyar, duk ta bi ta haukace akanka, zuwan nan da kai sai na gargadi Amal akan karta fada mata, saboda bata da lafiya zata iya daga hankalinta”

“Karatun kawai nake jiran ta karasa, i will Surprise her”

“A yanzun ya kama ka bata mamakin, ta yadda zata kare karatunta cikin kwanciyar hankali da natsuwa ba a cikin tunani da damuwa ba”

“Bana son wani abu ya samu karatunta ne”

“Me zai samu karatunta bayan tana final year, kuma tana tare da kai, haba Zain ko dan maganar Dada da Mai Martaba ya kamata kai wani ai”

“Zan yi tunani akai, you know somtimes ina mamakin yadda yarinyar nan ta aje ni cikin ranta na tsawon lokaci haka, ina jindadin hakan da ace a halin da ake yanzu Hafsat ta manta da ni ba san wane hali zan shiga ba”

“Ai be kamata ta manta da kai ba, Zain indai har zaka sadaukarda farincikinka akan wasu to kai ma ka cancanci farincikin na har abada”

Ya dan yi murmushi yana tuna wasu abubuwan da suka faru a baya.

*ONE WEEK LATER...*
Chapter 87 · 0% Book details