← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 93

Sashe 48

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hannayensa yasa ya dauketa ya fito da ita falo ya kwantar saman kujera, sannan ya haye sama, kayan jikinsa ya cire ya sanya short and vest ya dauko kasa ya shiga kitchen din, tayi tunanin gas din zai kashe ya dawo, amman be fito ba har bachi ya dauketa, he use to cook tare da Haleema sometimes ma shi zai girka musu dinner, ko su yi tare, so he is very good when it comes to cook dukan wani kalar abinci da Haleema take so ya iya girkawa.
Duk wani motsi da yake a kitchen din yana tuna masa da rayuwarsa ta baya ne, he can't remember when last ya girka wani abu mai nauyi sosai a kitchen dinsun bayan rasuwar Haleema. Tuwo ya dafa mata tuwon shimkafa, yadda ya dage yana murza tuwon sai ka rantse mace ce ba namiji ba, ko da ya gama ya kwashe ta yi bachi, yadda ya fito kitchen din ya hada gumi kamar wanda yai karamin yaki. Center table ya janyo ya dora mata tuwon sama sannan ya koma ciki ya dauki plate ya debo miyar ya kawo mata sannan ya shiga tashinta.

“Farhat Farhat tashi ki ci abinci”

Cikin maggin bachi ta ce

“Ba zan ci ba, bachi zan yi”

“Wallahi sai kin ci shi”

Hannunsa yasa ya tasheta zaune ya zaunar da karfi ya bude mata ido.

“Wake-up”

Ta kalli tuwon da kyau ta ga tuwo ne, ba dan tasan miyar kubewa tai ba da tace siyo ta yai, agogon falon ta kalla. Goma da rabi ya nuna sai kuma ta kalli Zain da har yanzu gumi yake.

“Waya girka?”

Ya mata banza ya tashi yaje ya dauki wani plate ya zuba na shi ya dawo ya zauna. Komawa tai zata kwanta ya katsa mata tsawa.

“Farhat, tashi ki tuwon nan Wallahi ko na mugun tsaba miki”

“To kawo min roba na wanke hannuna”

Kallonta yai da kyau sai kuma ya aje abincin ya tashi yaje ya dauko mata ruwa da ruwa ciki ta saka hannunta ta wanke sannan ya aje robar kasa. Har ta soma cin abinco ta gama be yi loma hudu ba, ya rike plate din kawi yana kallon tv ya kasa ci, ta yi mamakim yadda ya hada tuwo haka yai kyau kamar mace ta dafa, kamar ta tambaye shi sai kuma tai shiru ta mika hannu ta dauko robar ta wanke hannunta, da gangan ta karkarta robar ruwan suka zube. Juyo yai ya kalleta sai ya aje plate din ya tashi ya shiga dakinsa.
Bathroom ya shiga ya wanke hannunsa sai ya tsaya gaban madubi yana kallonsa kansa, a zahiri kansa yake kallo zuciyarsa kuma Hafsatu manga take kallo, rayuwarta yake tunani ina mutane da suka dauke zasu kaita mi zasu mata? Su waye su kuma waya saka su? Kallon da tai masa dazun ya tsaya masa a rai, sai kuma Anty Ummi wacce ita ce silar komai, da ace bata kai Hafsatu manga wani gurin ba da duk haka be faru ba. Ya dade yana ta bautawa abunda ba zai bauta masa ba, sannan ya fito ya kunna shower yai wanka. Ko da ya sake dawowa falon karfe biyu da kwata, Farhat na kwance a inda ya aje ta tana ta sharar bachinta. Tsaye yayi bayan kujerarta yana kallon fuskarta, she looks so cute and so innocent, Hafsatu manga ce ta fado masa a rai yadda yake watching fita da shigar numfashinta rayuwar da yai da ita a asibiti yake ta gani.

“Ya Rabb, ko wane numfashi yana tuna min da ke, hawayen da na gani a idonki sun hanani samun natsuwa”

Ya furta yana shafa fuskarsa. Zuwa yai ya dauke kayan da ta ci abinci da su ya kai kitchen ya gyara gurin, sannan ya dauketa ya kaita dakinta ya kwantar da ita saman gadon yaja blanket ya lullube ya kashe mata wuta ya fito daga dakin ya dawo falo ya zauna.

AUWAL POV.

“Ni ban gane wannan abun ba, ka dauki yarinyar mutane ka bada ita wani guri, yanzu kuma ka zauna kana da fushi da ni kamar na maka wani abu”

Ya daga mata hannu.

“Karki dame ni, tunda kika ga ban fada miki komai ba ai sai ki kyale ni ko?”

Ya tashi yaje gurin window falon ya tsaya yana danna wayarsa. Sai kuma ya kara ta a kunne.

“Wai minene alakarsa da ita?”

Hafsat ta amsa masa cikin kuka.

“Basu da alakar komai, yaya yace sai ya kulleni idan wani abu ya samu yarinyar, kuma ya koreni daga aiki”

“Ai kadan kika fara gani, nima sai na miki nawa wulakanci, uban waye ya aikeki fada masa tana hannuna?”

Fashewa tai da kuka sai Momy ta karbi wayar.

“Auwal dan Allah dan girman Allah ka kyale maganar nan, Hafsat zata iya samun aiki a wani gurin, babu ruwanka da alakarsa da ita”

“To Momy ba zan sake ba”

Daga haka ya kashe wayar, yaja juyowa yaga Zainab bayansa.

“Wata kake so ne?”

Ya dora hannayensa saman wuyanta yana murmushi.

“Ni babu ruwana, da karin aure wani sha'anin ne da be shafe ki ba, karki wani tashi hankalinki kinji?”

“Akan yarinyar ne?”

“Yes”

Ya mata kiss a goshi kamar ba shine yake fushi da ita ba. Sai kuma ya rumgume kankam a kirjinsa yana murmushi.

‘I will teach you a lesson Zain, indai akan yarinyar nan ne ka kori kanwata sai na koya maka hankali sai ka yi kuka da idonka’

A zuciyarsa yake wannan maganar a fili kuma kissing din matarsa yake suna kokarin lulawa wata duniyar.
Washe gari bayan sun gama breakfast ya fito harabar gidan ya kira, Hafsat bugu daya ta dauka.

“Doc ya kike”

“Lafiya kalau”

Ta amsa masa cikin rashin jindadi.

“Fada min inda zan samu yarinyar nan wacce ta zo gurinki tana bincikar labarin yarinyar kauye”

“Ni ban san inda zaka same ta ba, ba Momy ta ce ka daina maganar ba”

“Wannan tsakanina da ke ne please, ki nemo min inda zan samu number karki bari Momy ta ji”

“Ban san inda zaka samu ba”

“Haba ki yi tunani mana, ya aka yi ta san yarinyar tana gidan? Ita da wa ta zo?”

“Ita da Isma'il shi ya fada mata saboda shi kadai na taba firar da shi, sai kuma Ibrahim”

“Ta hanyar Isma'il din zaki samo min number ta”

“Amman Dsp...”

“Please mana Sis...”

“Okay”

Daga haka ya sauke wayar, ya juyo ya dawo falon yana saka hannayensa aljihu.

*** *** ***

Tun jiya da suka baro garin gusau Hafsatu bata daina kuka ba, kukan hada ta da mutanen da bata sani ba kuma bata san inda zasu kaita ba, gashi ta kara nisa da garinsu, ga kuma wani dan banzan ciwo da mararta ke yi, bata san ciwon maraba dan haka sai ta dauka ko cikinta ne ke ciwo.
Bata san garin da suka zo ba, iya kar abunda ta sani ana ta wuce garuruwa da yawa kamin su iso wannan kauyen da babu komai sai gidajen kara da shanu, ko ina fulani ne sun yi tunga tunga.
Ciki dakin kara mutumen da suka zo tare ya sakata ya gargadeta akan ta daina masa kuka haka kar yan'uwansa fulani su gane cewar daukota yai ko kuma wani abun yai mata. Sai kai tas hannu a baki ta toshe bakinta amman bata daina kukan ba.

“Wallahi in ba kai shiru ba sai na sa bulala na saneka da ita”

A dole ta hade kukan ta zauna a gurin tana ta soshe soshe, nan da nan bachin wahala yai gaba da ita.

36

A hankali Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya, ya juyo ya fuskanci Zain da kyau ta yadda zai fahimci zancensa.

“Look duk wannan abun be taso ba, at first daman can baka san da yarinyar a rayuwarka ba, so ka saka a ranka a yanzu ma baka santa ba, idan har Allah yana nufin sake haduwarku ba zaka sake haduwa da ita no matter ya shiga tsakaninku and no matter how far, ban sani ba ko zaka yarda da ni, amman Zain son yarinyar nan kake... ”

“No no, karamar yarinya ce ba sonta nake so ma soyayya ba, bana tunanin haka”

“Nima ban ce son soyayya kake mata ba, amman dai kana sonta, irin son nan da kan hana mutum samu natsuwa da kwanciyar hankali, a iya abunda zan maka a yanzu shawara zan baka a matsayena na amininka kuma dan'uwanka, ban sani ba ko zaka dauka”

Maganar yake fuskarsa na nuna gaskiyarsa, sai da Zain ya busar da iskar bakinsa sannan ya cigaba da kallon Ibrahim.

“Abunda na ke ganin ya fi ka fita waje na dan wani lokaci, Zain you need some spaces and fresh air, idan ka daga ma kasar nan a yanzu saka masu natuwa da kwanciyar hankali daka rasa, zaka yi nisa da Hameeda da kuma Dada, so kaga ka huta da matsalarsu dole zasu daga maka kafa, Anty Ummi ma da kake ganinta as wicked woman zaka kai nisa da ita, zaka samu natuwa idan har kai nisa kasan baka kusa da Mama and kasan she's nowhere to be found”

“A a wannan ba shawara ba ce Ibrahim, ko kasar nan na bari ba zan taba samu kwanciyar hankali ba, taya ma za ayi na samu kwamciyar hankali bayan ba wacce nake so na aura ba”
Chapter 48 · 0% Book details