← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 93

Sashe 45

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ka shigo?”

“Ee ya aka yi?”

“Dan Allah same ni office”

In few minutes Ibrahim ya shigo office din, ganin Farhat kwance a gurin ana sa mata jini ya bashi mamaki, miyasa ba zai kaita dakim jinya ba ya aje ta office dinsa.

“Ta tambaye mi take ji a kafafunta”

“As how?”

“Just ask her”

“Mi kike ji a kafafunki Farhat?”

Juyowa tai ta kalli Ibrahim fuskarta dauke da murmushi.

“Ina kwana?”

“Lafiya kalau”

“Tana min zafi, kuma bana iya takawa idan na taka sai na ji ciwo sosai amman idan ban taka ba bana jin komai, ta dan kumbura kadan kuma ta yi ja”

Ta dan unkuro zata ta nuna masa gurin Zain ya bude nata hannu.

“Wai miyasa baki da hankali, tun yaushe ya fara miki ciwo?”

Ta ki amsa masa har sai da Ibrahim ya maimaita mata tambayar.

“Tun jiya ya fara min”

“Buguwa kikai da wani abun ko kuma haka kawai ya rika miki ciwon?”

Zain ne yai mata tambayar, amman sai ta juya gurin Ibrahim tana bashi amsa.

“Hakan nan akwai yake min ciwo”

Zain ya kalli Ibrahim.

“That's all”

“Allah ya daidaita tsakaninku”

Cewar Ibrahim sannan ya fice daga office din yana ta mamaki wane irin zama ne zasu yi haka ko ma suke yi.

Sai da ya gama kara mata jinin sannan ya dauko mata magani bayan ko wanne ya rubuta mata yadda zata yi amfani da shi ya mika mata. Hannu biyu tasa ta karba.

“Zain dan Allah kai hakuri kaji”

Ya mata banza.

“Dan Allah kai hakuri, idan ka yi hakuri ka kaini inda Anty Ummi ina son ganinta”

Daukarta yai kamar dazu ya saka a Wheelchair ya fito da ita, sai magiyar ya kaita gurin Anty Ummi take masa ta marairaice masa kamar ba ita ba.
Be ce mata komai har ya isa gidansu Anty Ummi, she was very happy da taga ya kawo ta gidan Anty Ummi, kamar dazu yanzu ma bude mota yai ya dauko ta, sai dai wannan karon fitowa kawai yai da ita ya barta nan ya shigarwa falon Anty Ummi. He feel uncomfortable, saboda ganin yan uwan Anty Ummi na gurin Ubanta dan haka yana zama ya taso ya zo waje.
Jikinsa motarsa ya jingina yana jiran Farhat ta fito su tafi, sai ga Anty Ummi ta fito ta nufo inda yake tsaye.

“Zain na sani ba abu ne mai sauki ka rayu da wanda kake so ba, ni kaina da nasan Farhat zata hada da irin matsalar da Haleema ta hadu da ita da ban cilasta mata aurenka ba, yarinyar nan marainiya ce mahaifiyarta bata son aurenta da kai, saboda ta tsaya kai da fata akan ita ba zata auri Alhaji Bashir ba, and na san matsalar gidanku Farhat ba zata iya daukar duka ba, ta fada min wannan ne karo na biyu da tai aman jini kuma tana jin cikinta na ciwo kamar yadda da Haleema take yi, ta fada min kafafunta na ciwo ba zata iya takawa, dan Allah Zain ka yi duk abunda za ka iya wajen ganin yarinyar nan ta samu lafiya, ka yi zaman lafiya da ita ba musan abuna gaba zata haifar ba, ta fada min irin zamantakewar da kuke, na mata magana na mata nasiha and she promise me ba zata sake wanin abun ba...”

Ta karasa hawaye na sauko mata, sai Zain ya dauke fuskarsa.

“Mama tana Kaduna gurin wani Dsp, na fadawa Dcp hka jiya”

Hannu tasa ta share hawayen idonta.

“Ee ya fadawa Abbah haka jiya da dare, yace yau za a zo da ita kuma idan an kawo ta zai kira, amman Zain baka tunanin kamar akwai sa hannun wani a lamarin nan?”

“Yes ko wanene ma soon asirinsa zai tonu, mutane da suka gabatar da kara ba iyayenta na gaskiya ba ne”

“Nima naga alamun haka, amman ba kake zargi?”

“Dsp”

A nan ya kwashe labarin komai ya bata.

“Amman idan Dsp Auwal ne wanda akai ma transfer ai shine wanda ya yaudari Farhat”

Zain yai shiru yana sauraren wani bakon al'amari, tare da kallon Farhat wacce ta fito daga falon Anty Ummi tana dingishi tana taka kafar a hankali alamar tana jin zafinta sosai. Tun kamin ta karaso ya bude mata front seat, ta shiga ta zauna shima ya zagaya ya shiga Anty Ummi tana masu bye bye.

Tunda suka kamo hanya yake tunanin kalaman Anty Ummi, what if she's telling the truth? Yana iya tuna yadda ya rayu da Haleema cikin farinciki har mutuwa ta rabasu, what will happen idan har ciwon Haleema ne da Farhat? Driving yake yana kallonta har sai da jikinta ya bata ita yake kallo, ta juyo ta kalleshi ta murguda masa baki ta juyar fuskarsa, shi kuma ya dauke kansa ya cigaba da driving din yana jin dansa babu dadi. He needs to investigate, ya kamata ya gano abunda yake damunta, maybe ba irin cutar Haleema ba ce.

HAFSATU MANGA POV.

Tun ciki dare Zainab ta fada mata gobe ta tashi tun da wuri ta share mata ko ina ta goge, dan haka ta tashi tun da sallah asuba ta share falon da irin sharar da ta iya, taje ta kunna fanfo ta debo ruwa a bokiti tazo falon ta watsa a ko in sannan tasa tsumma tana gogewa, idan ta dibi ruwan da tsumma sai taje kofar falon ta matse ruwan ya sake dawowa, gashi ba tai removed center carpet ba. Duk abunda take Auwal na tsaye jikin kofa yana kallonta bata san yana kallonta ba shi ma kuma be mata magana. Har sai da taga tsumman ba zai yi ba taje ta dauko mopper ta saka tana gogewa gashi ruwan yayi yawa, sai kawai ta fashe da kuka. Takowa yai yaje inda take tsaye yaja hannunta zuwa gurin kujera ya dauketa ya dora saman kafafunsa. Ya rumgume a kirjinsa.

“Hafsat zaki je gida yau”

Ta daga kai ta kalleshi.

“Gurin Uncle ko gurin Mama?”

“Nima ban sani ba, but am sure zaki dawo nan, sai na nemo iyayenki ko a ina suke, daga Hafsat har Zain din sai sun yi regretting wannan”

“Wa zai kai ni gidan?”

“Yan samda zasu zo su tafi dake, umarni ne daga sama”

“Aa bana son su, bana so”

Around seven o'clock police suka kai knocked kofar suka karbeta, wani irin kuka Hafsatu manga take na fitar hankali, duk wanda ya ganta a lokacin xai yi zargin ko wani abin za a mata.
A cikin mota wani police ya cilasata mata yin shiru, a haka tai bachin dole, misalin sha biyu na rana suka iso da ita Gusau. A maimakon a wuce da ita police station sai aka biya da ita wani gida, a wani madaidaicin falo suka shiga da ita, Hameeda na zaune saman kujera tare da Dcp da Fulanin mutanen nan da kuma wasu police biyu a tsaye.

“Wallahi na so an daure matar nan”

“Idan muka zafafa abun asirinki ne zai tonu, kin ga Zain classmate dina ne kuma zai iya yin bincike wajen ganin ya gane komai, and know Alhaji Salisu ma zai tsaya ma yarsa”

“Amman ai tun farko baka fada min ka san Zain ba”

“Nima ban san zai shigo cikin lamarin ba”

Dcp ya kalli Hafsatu manga wacce ta sha jinin jikinta ta kame a guri daya ya nuna mata fulanin dake gurin tare da daka mata tsawa.

“Kin ga wadannan sune iyayenki, idan aka tambaye iayyen ki nuna wannan ki ce shine mahaifinki, wacan kuma innarki, idan kika fadi wano abu wanda ba haka ba, sai nasa bindiga na harbe kanki kiji”

Ta gyada kai hawaye ma mata zuba yana numfashi daker.

“Wacece wannan?”

Hameeda ta tambaya.

“Ma... Ma... Mama...”

“Good, wannan fa?”

“Ba... Baba... ”

Sai kuma ta juya gurin mutane.

“Ana gama case din nan zaku bar kasar nan ku koma can garinku Nijar, ku tafi da ita ko da wasa karku yi saken barin ta dawo kasar nan”

“To Hajiya, Allah ya saka da alheri”

Kudi mai yawa ta diba ta basu, sannan Dcp yasa police din su tafi da ita office dinsa dake cid, ya kira Alhaji Masa'ud, da Alhaji Salisu da Zain ya sanar musu cewar an kawo yarinyar. A tare suka fito da Hameeda ita ta nufi unguwar Samaru shi kuma ya nufi Cid office.
[3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 35

DOC HAFSAT POV.
Kamar wata marar tafiya ta tashi a yau, tun shekaranjiya da abun ya faru ta kasa sake jiki ta dauki damuwa ta sakawa kanta.
Tana son aikinta, ta san zata iya samun aikin a wani gurin, sai dai barinta gurin ne be mata dadi ba, domin tana jindadin gurin sosai, bata san iya maganganun da zasu biyo baya ba, domin kowa zai yi mamakin jin Zain ya koreta haka kawai.
Bata dakinta ba har sai da Momy ta aika Sapna ta kira, sannan ta fito tana wani tafiya, kallonta Momy take har ta karaso ta zauna a kujerarta.

“Wai Hafsat Lafiyarki kuwa?”

Ta dan dago kadan ta kalli Momy.

“Momy ina son aikina”

“Kina son aikinki ko dai kina son Zain din?”

Cewar Sapna tana zuwa kofin shayinta.

“Aikina nake so, kin fi kowa sanin babu soyayya tsakanina da Zain, duka abunda na ke ina yi saboda Ibrahim shi nake so ba Zain ba, kawai dai ina jindadin gurin kuma ina jindadin mu'amala ta da kowa a gurin”

“Amman ai zaki iya samun gurin da yafi wannan, miye abun damuwa a ciki? Ko wace asibiti kike so aiki a kasar nan zaki iya samu tunda kina da takardun masu kyau”

“Amman Zain yana min kallo na ci amanarsa, kuma Ibrahim ya fada min mutanen da suka tafi da ita are not her real parents”

“Ina ruwanki da yarinyar da aka koreki saboda ita zaki kanki a damuwa saboda ita? Ji rashin jutuwar dake kokarin shiga tsakaninki da yayanki haba Hafsat”

“Momy har yanzu be kyale maganar ba, jiya ya kirani ya son na nemo masa number matar nan wacce ta zo tana tambaya akan yarinyar kauye”

“Wacece”

“Ina ganin yar'uwar Zain din ce”

“Wato duk maganar da nai masa bata shiga kunnensa ba ko? Bari zan kira shi sai na bata masa rai”
Chapter 45 · 0% Book details