← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 93

Sashe 91

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tun da Hafsat ta koma Kaduna saboda scul shi ma ya koma Paris saboda aikinsa, a ko da yaushe cikin waya suke, su yi chat amman be hanasu missing din suna ba, be dawo ba sai da ana saura one week ayi bikin sannan ya dawo, duk wani shirye shirye da ake na bikin Ibrahim ne yake yi a madadinsa, wanda kuma iyaye ne ya kamata su yi already sun yi nasu.
   Ya dawo on Saturday aka yi sa lallebon Wednesday, Thurday akai friends evening, Walima akai Friday a ranar akai yi ma amarya lalle da kitso, Washe gari Saturday aka daura aure a garin Kaduna babban masallacin jumma'a da ke garin Kaduna, daurin auren daya samu halarta manyan mutane yan'siyasa yan kasuwa da kuma ma'aikatan gov... A ranar a kai mothers day da yamma akai wanki amarya lalle sannan aka kama hanyar Gusau da Amarya bayan iyayen da gwaggowani sun yi mata huduba, kuka sosai momy tai wanda zaka kasan gane na minene? Farinciki ko bakinciki rabuwa da yarta. Sun isa Zamfara late saboda jirgin be taso da wuri ba. A masarautar Rishim akai ma Amaryar kuma surukar fada tarba mai kyau, a fadar Mai Martaba aka fara shigowa da ita, sai gwaggonin Zain suka shigo da Dada Yalwa, suka budewa Amaryar kai suka saka mata turare kamar yadda al'adar masarautar ta tanada. A bangaren Hajiya Hadiza aka wuce da ita bayan an gama zaman fada, a nan Amarya ta ci abinci tare da yan rakiyarta sannan ta sake wanka ta shirya cikin wasu tufafin da alkyabba sannan aka zo da ita dakin Hajiya Zara, da Hajiya Maryam suka mata hudu, sai aka sake maida ita gurin Mai Martaba, yai mata huduba da nasiha akan zamantakewar aure. Sai kuma aka kaita gurin Dada Yalwa, tai mata nata huduwar, Dada har ta kukan tana tuna abubuwan da suka faru a baya, a dayan bangaren kuma kukan nata na farinciki ne yau ta sake ganin matar da Zain yake son kuma ya aura.
   Bayan an fito da ita daga masarautar Rishim, aka dauki hanyar GRA ring road da ita. Haka aka jera motocin kaita kamar motocin saidawa babu shege a ciki balle yar'iska duka manyan motoci ne na alfarma. Har aka isa da ita gidanta kuka take abunda kowa be sa ran zata yi ba, tana kukan rabuwa da iyayenta ta san ba ta bar su bane har a bada amman ta nisanta da su, wata sabuwar rayuwa zata fara, duk irin daukin auren da take be hanata kewar iyayenta ba.
   Babban gidane wanda idan za a kasa shi zai yi gidan hudu, amman aka hade akai yi gida daya, fentin gidan sky blue ne mai kyau, ko ina na gidan fulawoyi ne da shuke shuken itace ko'ina na gidan haske ne kamar rana.

     Tsayawa fadin yadda aka tsara falon da kayan alatu bata lokaci ne, domin babu abunda aka siye shi a naija duk na abroad ne, har spoon din cin abincinta Abbah be yarda an siye shi a nan ba, sai waje. Balle kuma furniture da kayan kitchen, royal chairs aka saka mata like her dinning table.
Ga wata uwar wallpaper da aka saka mata mai kyau da daukar hankali, an kawata falon da kayan kawai na zamani da mutum zai iya tsammanin a wata kasar yake idan yana ciki, kasancewar left and right side na falon an yisa ne da glass mai kamar fulawa, ga wani tattausasan Center carpet da aka saka mata a tsakiyar falon.

A dakinta Turkish furniture aka saka mata and all the room was decorated with red curtain and red Center carpet just like her bed, everything was so perfect and beautiful.
   A gefen gadon aka zaunar da ita her friends and relatives sa suka rakota suna tare da ita, da kuma wasu yan'uwan Zain, around eleven wasu suka fara watsewa, sannan aka shigo da Ango tare da abokansa. A bakin gadon ya zaune yayinda ita kuma take zaune a a tsakiyar gadon kanta a sukune ta rufe kanta da alkibbar da aka saka mata a fada.

  Duk wani abu da akai na siyen baki da wasanin da kawayen amarya ke yi da abokan ango har akai aka gama bata dago ba, she's just smile tana wasa da yatsun hannunta. Bayan ya raka abokansa ya dawo dakin ya zauna bakin gadon kamar dazu fuskarsa dauke da murmushi, sai kuma ya leki fuskarta sai tai saurin saka hannayenta ta rufe fuskar.

“Komai ya zamo mana kamar a mafarki, ban tsammaci zuwan wannan ranar ba, amman Allah ya tsara mana komai”

Sai ta sauke hannayenta ta kalleshi.

“Ni kan na tsammaci zuwanta, domin na san komai daren dadewa wata rana zata zo wanda zan kasance Amaryar a guri mijin da zan aura, kuma ina da yakinin Allah ba zai min zaben da be dace da ni ba”

“Ko? Nikam kin ga ban dauka zan aureki ba, dukan abunda ya faru a yanzu ban kawowa raina zai faru ba”

Ya fada yana kokarin saka hannayensa ya janye mata alkibar da ke jikinta. A tare suka yi sallah suka gode Allah tare da addu'ar neman tsari, sai da suka zauna suna cin ya kara ganin irin kyau da tai, hannayenta sun san kumshi ga kanta ya sha kitso jikinta har wani shining yake. He feed her just the way da ita tai feeding dinsa, bayan sun gama ya fita daga dakin yaje dakinsa ya canja tufafin jikinsa zuwa na bachi, wanda hakan ya bata damar canja nata ita da saka rigar bachi pink color. Ko da ya shigo ya tarar har ta kwanta saman gadon, sai kawai ya kashe wutar dakin ya kwanta bayanta. (Ban yi aure ba, so ban san yadda first night take ba 😜 beside kowa ya san idan akai aure abunda yake faruwa so no need to write 🤗)

After sallah asuba suka sake komawa bachi, misalin takwas ta farka, bayan bayanta baya ma dakin gaba daya, cike da karfin hali ta sauko saman gadon da zimmar shiga bathroom amman jikinta ko ina yayi tsami, tana mikewa tsaye ya shigo dakin rike da kofin tea. Saurin aje tea yai ya nufota ta rikata.

“Ina za ki je?”

Ya tambaya bayan ya rikata ta Kwanto jikinsa.

“Bathroom”

Ta fada cike da shagwaba kamar za ta yi kuka. He kiss her forehead.

“Bari na kai ki”

Hannayensa ya saka ya dauke ta cak kamar ya baby ya kai ta toilet din ya aje kissing her neck, sannan ya fita daga bandakin.
Ta kusan awa daya a toilet din tana gasa kanta sannan tai wanka ta fito daure da tawul, sai a yanzu take jin kunya, a idan tana tuna abunda ya faru sai tai murmushi wani abun kuma ya bata kunya, ji tai kamar ba zata iya kara hada ido da Zain ba, har ta shirya kanta be dawo dakin ba, ita kuma bata daina taro abunda ya faru ba a daren jiya ba, zuwa wayewar garin yau.

Door bell aka danna tana jin lokacin da ya fita daga dakinsa yaje ya bude kofar, bata san me ba amman ta dan ji hayaniyar sisters dinsa, kamin wayarta tai ringing. Ganin number MB yasa tai saurin dauka tana murmushi,

“Hello”

“Amarya yar hutu, na san yanzu ma ba ku tashi ba ko?”

“Mun tashi tun da asuba ma”

“Aa ba zan yarda ba gaskiya, babu angon da za a kaiwa amarya kyakkyawa irinki, ace kun farka tun da safe ba zai yiyu ba”

“Laaa baka yarda ba?”

“Ya za'ayi na yarda? Ai ko qur'ane kika dafa min ba zan yarda ba, yanzu dai fada minnya gaji kuma ya angon na ki?”

“Lafiya kalau muke, ina madam dinka?”

“Tana nan lafiya ta ce a gaishe ki”

“Ina amsawa na gode”

Tana aje wayar Zain ya shigo dakin.

“PureHeart ta so mu ci abinci, ga breakfast can an kawo”

Ya fada yana dafa shoulder dinta yana kallon fuskarta ta madubi. Ita kuma ta kasa hada kasa hada ido da shi.

“MB ya ce na gaishe ka”

Ta fada tare da Mikewa tsaye.

“MB”

Ya nanata sunan yana tuna lokacin fa ta fada masa abotar da ke tsakaninsu.

“Yeah wannan friend din nawa”

“Na gane shi”

Ya fada yana kokarin riko kwankwasonta.

“Bana son ya kara kiranki dear, kin yi aure a yanzu so karki sake kulashi ni ban yarda da wani friendship ba tsakanin matar aure da mijin aure”

“He just my friend”

“It's not just.. Duk abunda musulunci ya ce mu bari ko mu gujeshi barinsa shi yafi, ni fa ina da kishi kuma ba zan so wani abun da zai kawo matsala a tsakaninmu ba”

Ya fada yana goga mata hancinsa a gefen fuskarta tare da zagaye cikinta da hannayenta.

“Fine, i will talk to him zan fada mishi kar ya sake kira mijina baya so, indai har hakan zai saka farinciki”

Sai da yai mata kiss mai kara a kunne sannan ya ce.

“Yes na fi son hakan, not just call har chat karku yi”

“Yes Mi Omri”
Chapter 91 · 0% Book details