Sashe 37
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Itama ta fada tana murmushi, ba karamin zafi maganarta tai ma Hameeda ba, amman sai ta nuna kamar bata ji komai ba.
“Wow ashe haka aka gyara falon Yayata, Allah sarki yar'uwata, mutuwa tai mata gaggawa duk irin son da Zain yake mata yana fadar ba zai taba son wata mace kamar ba, yau gashi ya kawo wata a cikin gidanta”
“Wacece yayarki?”
“Macen da Zain yafi so fiye da kowa a duniyar nan, kuma macen da kike kokarin maye gurbinta”
Farhat tasa dariya, sannan ta zauna kamar yadda Hameeda ta zauna a kujarar dake falon.
“Ni bana kokarin maye gurbinta, sai dai na rufe gurbinta na gina nawa gurbin a zuciyar mijina”
“Kinyi kokari gaskiya amman kin san komai lalacewar dan giwa yafi gawurtaccen bunsuru”
“Wani dan girwar ba, amman idan ana maganar Zaki a dawo kin san ai shi ke da sarauta”
“Haka ne, bari na tashi naga dakin Amaryarmu tunda taki gabatar ni ga dakin yayata”
Ta fada tana murmushi, kana ta tashi ta nufi hanyar stairs, sai Farhat tai saurin cin mata tasa hannunta biyu ta juyo da ita ta rika fuskarta.
“Ina tunanin kyakkyawar fuskarnan bata bukatar arba da dakin yayarta, wanda aka canja safur aka mallaka min shi a matsayin dakina, kamar yadda na mallake zuciyar mai gidan gaba daya”
Hameeda tayi murmushi tare da ture hannun Farhat sai ta koma ta zauna.
“Haka ne fa, yanzu dai fada min ina yayana yake”
“Bana da tabbacin inda yayanke yake a yanzu, abu daya nake da tabbacinsa zuciyar yayanki tana nan tare da ni”
Hameeda na kokarin soka abunda ke hannunta cikin hannun kujera ta ce.
“Hakan yayi kyau Allah ya kara danko soyayyah”
“Amin”
Kamar kar Farhat ta rufe baki, sai ga Zain ya turo kofar falon ya shigo cikin wani irin bacin rai.
“Dan Allah kin ganshi ya dawo”
Ta tashi ta nufi inda yake tana murmushi. Tana shan gabansa ya kaice sai ta sake shan gabansa rikota yai ya jefar saman kujera, cikin wani irin bacin rai daya rufe masa ido har baya iya ganin Hameeda dake falon, haka yake idan ransa ya bace shi kansa baya iya controlling temper sa.
“Wai baki da hankali ne ke? Useless”
Yana fadar hakan ya nufi upstairs, wani kallon mamaki Hameeda tai ma Farhat, sai kuma ta tashi da sauri ta bar falon.
Yana shiga dakinsa ya tararda dakin a yadda ya barshi ga aman da tai saman gadon bata cire bedsheet din ba, komawa yai falon ya riko kanta ta tuso keyarta har cikin dakinsa.
“Wace irin mace ce ke? Baki san ki gyara daki ba, five minutes na baki ki gyara min dakin nan”
Yana fadar hakan ya juya ya fice zuwa fadar Mai Martaba, faduwa Farhat tai a gurin ta fashe da kuka..
Ina aka kai Hafsatu manga?
Anya Zain zai sake ganinta?
Ya Anty Ummi zata kasance?
Ya rayuwar Farhat zata kasance?
Anya Hameeda zata rufe ido ta bar komai ya wuce kuwa?
Wa za a kashe?
Wa zai yi kisan kan?
Ta wace hanya Dsp Auwal zai shiga rayuwar Hafsatu manga?
Wane hali Zain zai kasance ce?
Tsakanin Barrister Hassana da Barrister Husaina wa zai tsayawa Hafsatu manga a kotu?
Ta ina zasu gane alakarsu da ita?
Ina Hafsatu manga zata ga mahaifinta?
Anya Rufaida Mahaifiyar Hafsatu manga tana nan raye?
Sai yaushe asirin Safiya zai tonu? Wane hali take ciki kuma zata kasance?
Miye alakar Zain da Hafsatu manga?
Miye alakar Anty Ummi da Hafsatu manga?
Shin Hameeda zata cin ma burinta na auren Zain?
Wane irin hali Hafsatu manga zata shiga, mi zai faru da ita?
Domin samun amsar wadannan tambayoyin turo 300 ta 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, sai ka turo da shaidar biyan kudin ta wannan number 08036126660.
Ko kuma katin waya mtn 300 ta wannan number 08036126660.
A nan na kawo karshen free pages din Hafsatu manga, kamar yadda na fada tun a Rai biyu cewar zan yi Hafsatu manga na kudi.
Best regards 😍🌺
Khadeeja Candy ❤
[3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 27
Ko da ya shiga fadar ya tararda Mai Martaba na da baki wandanda suka kawo masa ziyara. Hakan yasa shi dawowa ya zagayo ta cikin gida, ya shiga bangarensa.
A falonsa ya zauna ya natsu sosai kuma ya kagu mai martaba ya shigo ciki. Ya kwashe awa daya da rabi a falon sannan Mai Martaba ya shigo. Zain na ganinsa yai saurin saka daga kan kujerar ya zauna kasa, sai Mai Martaba ya kalleshi yana murmushi ya zauna.
“Yarima lafiya dai?”
“Lafiya kalau Mai Martaba, akwai wata magana da nake son mu yi da kai, na san kasan an kaiwa Kauyen Kufawa hari, shine nake ganin ya dace ya ashirya wani abu daga masarautar nan a kai musu, domin gaskiya ance sun yi hasarar dukiya da yawa ina ganin ya dace mu shirya wani abu sai na wakilceka”
Mai Martaba yayi murmushi yana kallon Zain cike da burgewa.
“Na jidadin da wannan maganar ta fito daga bakinka, hakan ya nuna ka fara maida hankali da yin abunda ya dace, amman ka makaro domin masarautar nan ta riga ta aikata musu da abunda zamu iya tun daga lokacin da abun ya faru”
“Hakan yayi kyau, Allah ya kara maka lafiya”
Ya fada hankalinsa na kokarin komawa wani gurin, wata mafita yake nema ta yadda zai sake ganin Hafsatu manga, ko da bata dawo gareshi ba yana son ya tabbatar da lafiyarta.
“Allah ya taimakeka zan shiga cikin gida”
Kai kawai Mai Martaba ya daga masa, sai ya tashi ya fice daga falon, wannan karon ta kofar waje ya fita, wato kofar fada ba kofar cikin gida ba kamar yadda ya shigo.
A kofar fadar ya tsaya yana neman sarkin dogarai, sai gashi ya zo da gudu ya fadi gabansa yana kwasar gaisuwa.
“Same ni a kofar gidana”
Yana fadar hakan, ya nufi hanyar da zata sadashi da part dinsa. Sarkin dogarai na biye da shi sai fama saba rike yake har suka isa inda Zain yake son su tsaya. Sai da Zain ya duba yaga babu mai ganisu sannan ya kalleshi
“Wani aiki nake son ka min, amman bana son kowa ya sani ko ya ji”
“Allah ya taimake, babu sirrin da Yarima zai yi da ni wani ya jishi a bakina, idan har zan iya fadin sirrinka to zan iya kashe kaina da kaina”
“Ina son ka nada wani amintaccenka yaje masarautar kufawa ya bincika mana wata karamar yarinya mai suna Hafsatu manga, a yau aka aika da ita masarautar gobe nake son samun labarin halin da yarinyar take ciki”
“Yadda kace haka za'ayi Yarima, dan sarki jikan sarki, ba a musa maka ba dan zaki mai isa da takama, sarkin gobe sarkin jibi sarkin dake yanke hukunci ko da sarki na nan, matsayinka daban ne cika....”
Zain ya daga masa tare da mika masa yan dubu dubu masu yawa.
“Wannan ya zama sirri a tsakaninmu”
“Ya zama Yarima, umarninka wajib ne”
“Tashi ka tafi”
Cikin sauri Sarkin dogarai ya tashi ya fice daga gurin. Shi kuma ya fito ya nufi masallaci a lokacin ana kiran sallah magariba ne, bayan ya gama ya fito ya nufo part dinsa, yana jin ransa babu dadi idan ya tuna abunda Anty Ummi tai sai ya rasa wane irin suna zai bata, a dayan bangaren kuma yana halin da Hafsatu manga take ciki. Yana taba kofar yaji ta rufe ba dan bashi da yadda zai yi da ba zai yi knocked.
Sau biyu kawai yai knocked din sai gata ta bude masa kofar idonta a kasa kamar bata son kallonsa.
“Sannu da zuwa”
Ta fada murya can kasa kasa, yayi mamakin jin ta gaisheshi sai dai hakan be sashi ya amsa ba, sai ma cewa da yai
“Karki sake rufe min kofa”
“Tau insha-Allah ba za a sake ba”
Kai tsaye upstairs ya nufa, a lokacin ta daga kai ta kalleshi.
“Ga abincin ka nan”
Har ya shige dakinsa be waigo ba balle har ya amsa ta, sai ta soma jin haushinta kanta miyasa ma tai masa magana?
Yana shiga ya cire kayan jikinsa ya shiga bathroom yai wanka, sai da ya fito sannan ya lura da ta canja bedsheet din, gaban madubi yaje ya zauna yana kallon fadada kirjinsa, saitin zuciyarsa yake kallo gurbin da Hafsatu manga ta samu guri ta tsaya masa, ya nemi sukuninsa da walwalarsa ya rasa duk kokarin da yake na ganin ya yaki bacin ran abunda Anty Ummi tai masa sai ya kasa, ta ko'ina ganin laifinta yake baya jin zai iya yafe mata matukar wani abun ya samu Hafsatu manga.
Wayarsa ce tai ringing sai yai saurin juyawa ya kalli inda wayar take kamar daman can jiran kiran yake. Tashi yai ya karasa ya dauki wayar ya duba brahim ne mai kira. Iskar bakinsa ya busar ya kamin yai picking.
“Zain kana ina?”
“Why?”
“Anty Ummi ce tai min waya, ina son magana da kai”
“Bana da bukata”
Ya kashe wayar ya jefar saman gado, cikin kankane lokaci ya shirya ya fice daga gidan, domin yasan Ibrahim zai zo nemansa akan maganar wacce baya son jin komai daga gurin Anty Ummi a yanzu.
Ciki ya gari ya shiga, gurin da yasan Ibrahim ba zai nemi shi a can ba, yana ganinsa kiransa yaki yai picking, har ya gaji da kiransa ya daina.
Tun da ya bar gidan be dawo ba, sai karfe goma na dare, a dakinsa ya samu Farhat kwance tana bachi, wani irin haushi yaji kamar ya shaketa, cikin fushi ya fisge zanen da take lullube da shi ya tsaka mata tsawa.
“Ke....!”
A firgice ta tashi tana kallonsa tsoro shimfide a fuskarsa.
“Tashi ki koma dakinta”
Cikin sauri ta sauka daga kan gadon ta nufi kofar fita jikinta har rawa yake. A dakinta ta shiga sai taji ba zata jiya kwana a ciki ba saboda tsoro tsoron da bata san na minene ba, domin a gidan Anty Rukaiya ita kadai take kwana a dakinta. Bedsheet ta dauko tare da matashin kai sai ta shimfida a kofar dakin Zain ta kwanta.
*** *** ***
A hankali Alhaji Masa'ud ya saka spoon ya debi tuwon shimkafa ya tsoma cikin miyar allayahu kana ya kai bakinsa
“Yau dai kamar baki cikin hayyacinki, duk rashin lafiyar Abbah ne?”