Sashe 51
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ki taimaka min Farhat ki kula da Zain kamar mijin da kike so, ki koyawa kanki sonsa, ki manta da Auwal domin ya butulce miki, kuma ya nuna baya son zama da ke, ki dauki wannan auren a matsayin kaddararki, baki san sakamakon da Allah zai miki ba, kuma bana son ki bani kunya Farhat”
Ta dora dayan hannunta saman na Anty Ummi tana murmushi.
“Insha-Allah Anty Ummi ba zan baki kunya ba”
“Na gode, bari na je Allah ya kara miki lafiya, na san nan gaba kadan Zain zai fara son ki idan kika haifa masa yara”
Tayi murmushi a ranta tana
‘Wannan mutumen zai iya aje girman kai ya taba ma, nima gaskiya am not ready’
A fili kuma sai ta ce
“Anty ba zaki tsaya na dora abinci ba”
“Aa nima yarana yanzu na san sun dawo suna jirana”
Har gurin motarta Farhat ta rakota, sannan ta koma ita kuma ta shiga motarta ta shiga Part din Hajiya Hadiza suka gaisa, ta mika gaisuwarta gurin Mai Martaba sannan ta kama hanyar gidanta.
37
Sai da ta fara shiga kitchen ta dora girki sannan ta shiga dakinsa ta gyara masa ko'ina ta canja masa bedsheet, wallet dinsa dake aje a kan aljihun gado ta dauka ta bude bedside drawer zata saka masa, sai ta tsaya kallon abubuwan data gani, dauko tai tana budewa gabanta ya fadi, kar dai ace Zain shaye-shaye yake.
“Idan har baya yi miya kawo wadannan abubuwan a nan? Shiyasa yake abu kamar marar tausayi, haka suke basa sa tausayi a take zasu iya kashe mutu”
Tayi saurin maidawa ta rufe, ta taso da sauri ta baro dakin, tana fitowa yana hawo stairs, tsaye tai tana kallonsa har ya karaso inda take tsaye kusa da kofar dakinsa.
“Ba na ce karki sake shigar min daki ba?”
“Saboda baka son naga abunda ke ciki ko?”
Ta tsaya kallonta kamar be fahimci zancenta ba.
“Do you know what the biggest mistake I have ever done is marrying you, mutumen da be yarda da kaddara ba, babu ruwansa da kowa, and the worst part of it dan shaye-shaye, na tsane ka Zain ban taba son ka ba kuma ba zan taba son ka ba”
Uffan be ce mata ba, ya zagaye ta ya wuce dakinsa, sai kuma ta fashe da kukan da baya san na minene? na maganar data fada masa ko kuma kyaleta da yai. Bata san abunda a duk lokacin da tai unkurin kyautata masa sai ta kasa ba. A gurin ta ci kukanta har ta koshi sannan ta tashi ta shiga kitchen ta kashe gas din ta sauke girkin ta shige dakinta ta zauna.
Be yi minti talatin dakin ba ya fito daga dakin, ya sauko kasa waya mallake a kunnensa, daga part dinsa part din Dada ya wuce kamar yadda Farhat ta sameta haka shi ma ya sameta fuskarta babu annuri tana hakimce saman kujera.
“Dada ina kwana?”
“Da ban kwana ba ai ba zaka ganni ba”
Yayi murmushin daya tsaya iya bakin lebi ta zauna a kujerar dake kusa da ita.
“Office zan je”
“Da akwai wanda ya rike kafafunka ne”
“Shawara na zo muyi da ke, amman kina min wulakanci”
Tayi kamar ba taji ba.
“Ina son naje Paris”
“Gurin mai?”
“Wata daya zan yi na dawo”
“Wai gurin me zaja je? Kai da wannan yarinyar zaka je?”
“Ko na bar miki ita?”
Taja tsaki. Sai yai yar dariya kadan
“Ba dadewa zamu yi ba, just one month darling”
“Dole ne sai kaje? Aiki ne zai kaika ko kuma yawonka ne kawai”
“Aiki ne zai kaini”
“To kuma dole sai kaje da matarka? Tafiyar wata daya za ka ce sai kaje da ita?”
“Ina son matata a kusa da ni, zan fi jindadi”
Kallonsa tai da kyau kamar zata ce wani abu sai kuma tai shiru. Ganin hakan yasa shi tashi ya fice ya bar mata falon.
Kai tsaye office ya wuce, wunin ranar be saka komai a cikinsa ba, kamar yadda yake jin zuciyarsa kamar babu komai a ciki, tunanin ya masa yawa har besan da wannen zai fara ba. He just decided ya bar kasar zai fi masa fiye da komai kamar yadda Ibrahim yake ce masa, amman kuma baya tunanin zai iya zuwa ya dade zaune a can tare da Farhat. Wani gurin gurin kuma yana ganin kamar bar kasar ba zai masa ba, shi namiji ne na dole ne a matsa masa auren Hameeda ba, idan har Mai Martaba ba zai masa dole ba to be kamata kowa yai masa dole ba, and yasan Mai Martaba ba zai yarda ya bar kasar ba, idan ma yaje wajen ba kwanciyar hankali zai samu ba tunda yana tare da Farhat. Ajiyar zuciya ya sauke ya kwanta saman kujera yana juyawa a hankali. Yana da bukatar Anty Ummi ita kadai ce abokiyar shawararsa bayan Ibrahim. Da la'asar ya bar asibitin ya dawo gida, sai kuma yaji gidan ya masa ba dadi, wanka yai ya canja kaya, on his way downstairs wayarsa yai ringing, Anty Ummi ce sai da yai kamar ba zai dauka ba sai kuma yai picking, fuska babu annuri kamar ance masa tana kusa da shi.
“Zain kana ina?”
“Gida”
“Yara sun yi missing dinka suna ta tambayarka, kuma nima ina son magana da kai”
Sai da ya aje numfashi sannan ya amsa mata da okay. Kitchen ya shiga ya dafa ma kansa indomie, bayan ya gama ya zuba a plate da zimmar ci sai kuma yaji abincin ya guntse shi, sai kawai ya aje plate din ya koma dakinsa ya dauki keys da wasu abubuwan ya fice.
Kai tsaye gidan su Anty Ummi, ita kadai ya tarar a falon yara duka sun tafi islamaiya, tana kallon yanayinsa har ya zauna.
“Zain duk ka rame?”
“Mi nake da shi da zai sa hankalina ya kwanta ko nai kiba, yau kwata kwata ban saka komai a bakina ba”
Ya karasa yana kallonta, tashi tai ta shiga Kitchen ta hada masa tea sannan ta zubo masa abinci a plate ta kawo masa. Tea kawai ya dauka ya sha.
“Ban san abunda zan yi tunani ba Anty, ban san iya abunda yake damuna ba, na rasa Mamata, kin yi forcing dina na auri Farhat, gida kuma suna ta ganin laifina akan naki auren Hameeda da wanne zan ji?”
“Kana manta wani abu Zain, kai fa Namiji ne komai zai iya tafiya a karkashinka, kaga wannan fushin da zafi zuciya babu inda zai kai ka, ka kwantar da hankalin ka fahimci komai...”
Ya sake kai kofin tea a bakinsa, yana kallon Anty Ummi, a zahiri ita yake kallo amman zuciyarsa da tunaninsa suna can wani gurin.
“Wannan Auwal din yace kai masa ita aikayi a matsayin mai aiki right? Waya kai masa ita? Ya akai aka kai masa ita?”
Anty Ummi ta masa kallon Mamaki da rashin fahimta.
“Mama again?”
“Yes Anty, mu kadai muka san sirrin nan, ke ni Ibrahim Hafsat, Ibrahim ba zai fada ba, amman Hafsat ba zata iya rike mana sirrinmu ba, ina kika hadu da wannan mutumen da kika bawa Mama? Miyasa be kai ko ina ba sai gurin Yayan Hafsat, mutumen da already ya ganta a gidan? Ke kika nemo shi ko shi ya nemi ki bashi ita”
“Aa ni na nema, amman ni ban ce ya kaita ga aiki ba, gidansu na ce ya kai”
“An saka police sun kamaki saboda yarinyar, wai kin sace ta right? Talaka kamar irin wadannan mutanen police ba zasu iya tsayawa su wulakanta babban mutum kamar kiba, wacce sun san waye ubanki a garin nan, and ansan wanene mijinki a garin nan, wa zai miki wannan wulakanci?”
Anty Ummi ta daga kafardarta alamar bata sani ba.
“Hameeda ce kawai zata iya miki haka, amman ta ina Hameeda ta samu labarin? I have to find out maybe Hafsat kawarta ce, if not to Auwal ne, amman kuma me zai sa Auwal din yai haka? Bayan bashi da alaka da Mama kuma ba shi da ni? Hameeda zata iya yin komai wajen ganin ta wulakanta ki saboda yana ganin kamar ke kika hanani aurenta, amman kuma miya kai Mama gidan Auwal din?”
“I dunno”
“Hafsat ce kadai zata warware wannan”
Ya yi saurin ciro wayarsa daga aljihu ya shiga blacklist ya nemo Number Hafsat ta cireta daga blocking ya danna mata kira, har tai har ta tsake ba a dauka ba, a haka ya jera mata kiran kusan uku ana hudu tai picking.
“Hafsat kina ina?”
“Ina gida”
“Zaki iya zuwa nan gada biyu ki same ni House number 7”
“Why”
“Kawai ki zo, gidan Anty na ne ba sai kin fada a gidanku na san ba za a bari ki zo ba”
“Okay”
Ta amsa kasakasa, yana sauke wayar Anty Ummi ta kalleshi
“Zain mi zaka yi karka saka yarinyar mutane ciki matsala”
“Ku yanzu ai rayuwar wata yar kuka saka ciki matsala, duk abunda zai samu Mama ko ya sameta saboda ni ne, ya kuma bata fi ya ba, yadda Hafsat take yar wasu haka Mama take yar wasu, so idan zaki fadi wata magana akan Mama za ki kara bata min rai ne kawai”
Hannu tasa tai zip up a bakinta. Suna zaune cikin falon suka ji tsayarwa mota, cikin sauri Zain ya tashi ya leka window Anty Ummi, motar Ibrahim ce yana hango yadda suka fito tare da Hafsat suka doso kofar shigowar.
“Wato dana kirako shine kika kira Ibrahim ko?”
Shine abunda Zain ya fada mata a lokacin da suka shigo falo, sai ta koma bayan Ibrahim ta tsaya kamar wata yarinya tana kallonsa kasakasa.
“Yes, yadda kake da temper din nan ai sai ka faketa idan tai maka ba dai dai”
Ibrahim ya fada bayan ya zauna kujera daya da Hafsat.
“Ko kana nan zan daketa idan tai min shirme”
“Aa kana wasa dai, a baka isa ka bugi Amaryata a gabana ba, yadda kasan idan An taba Mama sai inda karfin ka ya kare itama haka ne”
Zain ya tabe baki.
“Whatever, ke fada min bayan ni da Ibrahim baya san sirrin Hafsat tana karkashin kulawata?”
Zain ya karasa yana kallonta, sai tai yi shiru kamar mai tunani. Duk suka zuba mata ido, zuwa can ta kalli Zain da mugun tsoro ta ce
“Isma'il”