Sashe 7
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Munafuka ai daman ya fada min, komai game da ke duk abunda kike masa yana sanar da ni na zuba miki ido ne kawai naga iya gudun ruwanki, yar iska kawai wato an kawo ki kin sha jar miya kin waye ko? Shine kike son hada ni da miji ni ki kashe min aure ki gina taki rayuwar, to Wallahi bari kiji na fada miki baki isa ba, kuma ki hada komai naki ki bar gidan nan tun kamin ma ya dawo, jaka kawai”
Ta karasa tana jan wani mugun tsaki, ta juya a fusace ta fice. Hannu Farhat takai ta share hawayenta ta dauki wayarta ta saka password ta bude wayar, number Auwal ta lalubo har zata aika masa kira sai kuma ta kasa ta fashe da kuka. Ta kai minti talatin tana ta kuka sannan ta unkura ta tashi tsaye ta dauki Hijab din Anty Ummi da tazo da shi ta saka ta fito falo rike da wayar.
“Gidan uban waye zaki? Ba nace ki hada kayanki ki bar min gida ba? O... Gidan Ummi zaki koma ta sake kullo munafurcin ta sake iskoni office ko? Koma ki hado kayanki koma”
Ta turata da karfin ta koma dakin. Sai a lokacin hankalin Farhat ta fara dawowa jikinta har ta soma tuna maganganun dazu da tai mata, kayanta ta shiga hadawa sai kuma ta kasa, jin tai bata bukatar komai a yanzu , duniyar ma idan za a rabata da ita tana farinciki dan ita yanxu bata san wane irin hali take ciki ba.
“Mama... ”
Ta furta cikin kuka tana jin mugun son mahaifiyarta kusa da ita. Tashi tai da sauri ta dauki jakarta ta ratayawa ta fito daga dakin.
“Ai kin san nan ba gidan ubanki ba ne ko?”
“Tafiya zan yi Anka zanje yanzu Anty”
Ta fada cikin kuka, bata tsaya jiran abunda Anty Rukaiya zata sake ce mata ba, ta nufi kofa hawaye na bin fuskarta kamar ba gobe.
“Kara ma ki zo ki kwashe kayanki dan ni ko an dawo an bani hakuri ba zama zanyi da ke ba, makira kawai tsohuwar yar iska”
Babu irin tambayar da mai gadi be mata ba, amman bata ma kula shi ba balle ta masa shi. Tayi sa'ar samun napep a bakin gate.
“Babbar tasha zaka kai ni”
Ta fada tana kokarin tsagaita hawayenta, sannan ta shiga Napep din.
“Hajiya lafiya dai”
“Ba komai”
Tunda ya kama hanya be tsaya har sai da suka isa Babbar tashar gusau.
“Ina zamu ki je Hajiya”
“Anka”
Ta furta tana hadeye kukanta. Da gudu masu tarbon mutane suka biyo Napep din suna tambayar inda zata je, mai Napep di ya amsa da Anka, sai suka nuna masa inda motar Anka take. Dari biyu ta mika masa bayan ya aje ta kusa da inda zata shiga motar anka din. Gabanta ne ya shiga faduwa tambayoyi nata zuwa mata a rai kala kala, ta samu damar yin kukanta ishasshen a cikin motar kasancewar ita ce ta farko kamin a samu wasu Passengers, sai biyar da rabi suka kama hanya Anka domin direbobin basa son tashi sai mota ta shiga, duk irin kiran da Jawahir take mata sai taki dagawa sai kuka take har passengers din suka fara tsarguwa wasu kuma suna tunanin ko mutuwa aka mata ne.
Tunda suka kama hanyar garin kowa yake ta addu'a saboda sanin matsalar garin ta matsalar tsaro, Farhat kan bata komai sai kuka, har suka kai Mayanci, suna karawa gaba kadan suka ango wasu motocin an tsayar dasu a gefe sun danji tsoro sai dai ganin mutanen sanye da kakin soja yasa hankalinsu ya kwanta. Sai da suka karasa daf da su sannan suka gane cewar ba sojoji ne ba, fulanin nan ne na daji masu kashe mutane suka sanya kayan sojojin suna dauki da mugaye makamai. A take suka fitar da kowa dake cikin motar suka sa su kwanciya a gefen hanya, cikin har da Farhat dake kukan da zame mata na bakar rana.
https://www.wattpad.com/story/179794212?utm_medium=link&utm_content=story_info&utm_source=android
*HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_
Wattpad @KhadeejaCandy
7⃣
Anyi tiyata lafiya kuma cikin nasara kamar kullum, a Masallacin asibitin ya tsaya yai sallah la'asar sannan ya dauki hanyar gidan Anty Ummi.
A harabar gidan yai parking sannan ya fito ya nufi cikin gidan cikin rashin dadin rai, be samu kowa a falon ba, kasancewar yaran sun tafi islamiya, Anty Ummi kuma tana kitchen tana girki guri ya samu ya zauna ya maida hankalinsa kan wani film da ake a African magic channel.
Yafi karfin minti talatin zaune a gurin sannan Anty Ummi ta fito daga kitchen sanye da abaya hannunta dauke da karamin roba, a hannun cushion ta zauna tana kallon dan'uwanta.
“Kaga yarinya ne?”
“Ban je namanta ba balle ma na ganta, nasan ba kusa zata tsaya ba”
Ya fada ba tare daya dago ya kalli inda take ba.
“Farhat din ma bata dawo ba har yanxu, na aika gidansu ance bata nan, na kuma kira wayarta a kashe Wallahi duk na damu”
Tabe baki yai. Sai ya dauko wata magana.
“Dada tasa an cire hotunan Haleema”
Ko a yanzu ma be kalleta ba, sai dai sautin yadda muryarsa ya karantar da ita bacin ran dake zuciyarsa. Ajiyar zuciya ta sauke ya zauna daidai saman cushion din tana kallonsa.
“Dada Yalwa tayi daidai kuma tayi abunda ya dace...”
Sai a lokaci ya dago kansa ya sakar mata mayan idanuwansa yana kallonta, be yi mamakin furucinta ba, daman ya tsammaci hakan ita ce mace ta biyu bayan Dada da take kokarin saka shi ya manta da Haleema.
“Lokaci yai daya kamata ace ka canja rayuwa Zain, a izuwa yanzu ya kamata ace ka yarda da kaddara kuma ka dauketa a yadda ta zo maka, shekara uku kenan da rasuwar Haleema a halin yanzu addu'a take nema ba tunani ba, mahaifinka ma baya jindadin rayuwar da kake kaine babba, amman kana maida kanka wani kalar mutum saboda mutuwa? Wacce tana kan kowa? Kai ma baka wuce ka mutum ba, balle kuma matarka da Allah be yi ta danka ba”
Dauke kansa yai yana sauke numfashi a hankali.
“Na kasa mantawa da ita ne Anty, tana yawan fada min tana tsoron kishiya, ina ganin kamar idan na auri wata ban kyautawa Haleema ba, musamman wacce suke son na aura din, uba daya suke da Hameeda amman kamar makiya suke saboda Hameeda bata son ta ko kadan, tana yawan min complain akan Hameeda, Hameeda ce kadai mace data hana Haleema zama lafiya da kwanciyar hankali a gidan nan, amman su kasa gane haka Mai Martaba da Dada suna son tsayawa akan sai na aureta, a ganinsu ita ta dace da ni saboda Haleema, a ranar da zata rasu ta rike hannuna, tana kuka tana cewa Zain karka barni ina jin tsoro, na tambayeta na ce tsoron me? Sai tace bata sani ba amman dai tana jin tsoro kuma bata son na tafi ashe tsoron mutuwa take, tsoron rabuwa da ni take, ina fita dakin da minti uku Allah ya karbi abarsa, i can't forget this”
Ya cikama bakinsa iska tare da yin shiru na wasu yan mintuna sannan ya cigaba.
“Anty bana jin akwai wata mace da zan iya zaunawa da ita naji dadin rayuwa da ita, itama kuma ta jidadin rayuwa da ni, Musamman wacce suke son hadani da ita, bana son Hameeda Anty kuma ni bana son bazawara, hankalina baya kwanciya da macen da bani na fara kusantarta ba, a kullum ina kallon Hameeda kamar ita ta kashe min Haleema saboda ita ta sakata a cikin halin da ta shiga wanda yai sanadiyar mutuwarta, taya za'ayi na zauna da ita? Taya zan ga farinta?”
Anty Ummi ta sauke ajiyar zuciya mai nauyi, tasan yadda Zain yake son matarsa, tasan irin gwargwamaryar da matarsa tasha a gidan da irin kiyayyar da Hameeda ta nuna mata.
“Wannan be isa ya zama dalilin da zaisa kayi ta zama ba aure ba, irin Haleema suna nan da yawa a duniyar nan, kuma nasan mai martaba yana kaunarka sosai xai so abunda kake so, dan haka duk yarinyar daka kawo xai sota matukar kana sonta, kayi kokarin neman kalar matar da kake so ka gabatar masu da ita tun gabanin su gabatar maka da Hameeda a matsayin matar aurenka, nasan ko Mai Martaba be yi haka ba, Dada Yalwa na daf da yin hakan”
“Kin sani Anty, a dokar da kuma al'adar masarautar Rishim, yayan masarautar basa auren wacce ba jininsu ba, ko kuma ba jinin fulani ba, taya zan karya dokar da zata sa Mai Martaba ya cigaba da yi min kallon marar tarbiya, Dada kuma ta tsani matar da za a kawo a gidan?”
“Ka bincika duk matar da kake so ni kuma zan tsaya maka kai da fata wajen ganin ka aureta, lokaci yayi da ya kamata ka rushe wannan dokar da al'ada ta gidanku, kana da hakki Zain kamar ko wane da, be kamata ka bar sarautar gidanku tana tauye maka hakki ba, kai ne Baban dan Mar Martaba idan ka lalace magauta dariya zasu masa kuma su maka, idan kuma ka gyaru shi kansa zai ji dadin hakan”
Da sauri Zain ya mike tsaye fuskarta dauke da mamaki, maganar Sadiq ta dazun xe ta fado masa a rai na yarinyar da tai hadari kuma ba a san kowa nata ba, what if Hafsat ce.
“Anty ina zuwa”