← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 93

Sashe 92

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu tasa ta ture masa fuska jin yadda yake cizon kunnenta. A tare suka karya da abinci da aka kawo musu, a gidan Mai Martaba da kuma na Anty Ummi.
Bayan sun gama suka sake shiryawa cikin kayan alfarma, mai Martaba ya aiko da mota da dogarai aka je da su. Ko da suka je sun samu fadar makil da mutane, bayan sun gaisa da Mai Martaba ya sake yi musu nasiha da jan kunne sannan ta wuce sashen matansa. Sai da yamma akai hawan amaryar kamar yadda al'adar masarautar Rishim ta gada na yi ma sukukarta busa da wata wasar hawan dawakai wanda ake kira da hawan Amarya. Duk abunda akai aka gama Hafsat bata a cikin walwala saboda har yanzu bata daina jin zafi ba, tafiyarta ma idan ka kura mata ido zaka gane komai, dan bata tafiya kamar yadda ta saba, sai dai ba kowa ya kula ba kasancewar tafiyar yayan sarakuna take dai-dai da dai-dai.
An gabatar mata da yan'uwa da kuma wadanda suke da muhimmanci a masarautar duk ta gaisa da su, wani iri ta ji lokacin da bayin masarautar da yan'uwan Zain suke ta bata girma, ko a nan kadai ta san ta yi sa'ar aure domin kuwa ta yi aure gidan da suka san muhimmancinta kuma suke son ta kamar yar gidan.
Kusan kwana uku aka jera kullum da kalar abunda ake a fadar, a daren na uku ne akai liyafar cin abinci tare da addu'ar neman tsari da kuma albarkar aure.
Bayan gama bikin fada, sai gaisuwar yan'uwan ta biyo baya, kusan kullum sai Mai Martaba ya aiko da mota da dogarai da bayi anje da ita gurin gaisuwar gwaggwanni da iyaye, bayan ta gama kuma kannensa suka biyo layi, daman haka al'adar take, surukar fada zata je ta gaishe da iyayen mijinta da gwaggwoninsa, su yi mata kyauta da alherai kala kala, kannensa kuma za su zo su gaisheta tai musu kyauta da tarba mai kyau. Bayin da aka aje mata ne suke fada mata irin abubuwan da zata yi, a gidansu ba a san da wannan al'adar ba, Zain kuma be fada mata ba, duk wani abu data dauka ta bawa yan'uwansa daga bangare Hajiya Hadiza ya fito da kuma Dada Yalwa.

A month later suka bar kasar zuwa paris gurin da mijinta yake aiki daman can paris na daya daga cikin kasar fa Hafsat take da mafarkin zuwa, ta yi farinciki sosai lokacin da ta bude ido ta ganta a kasar with the love of her life. Hakan ya hanata bachin kirki cikin dare already ta gaji ga kuma Zain daya hanata sukuni, daukin zuwa paris ma be barta ba, she wake up early a lokacin da Zain yake ta sharar bachi, kamar like shi ya gaji ba ita ba.
Dan karamim jean ne a jikinta wanda ya tsaya iya guiwarta, sai yellow vest mai siririn hannu, ta maida hankalinta sosai kan abunda take, amman tana jin kamshin turarenaa sai ta juyo da sauri ta kalleshi. Jingine yake jikin kofar kitchen din ya rumgume hannayensa yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi. Ita ma murmushin tai masa ta kanne masa ido daya. Cheek dinsa ya nuna mata.

“Good morning kiss”

Cup din hannunta ta aje ta karaso kusa da shi tai dage ta manna masa kiss din a kunci.

“Good morning Mi Omri”

Ta fada tana watsa da hancinsa. Sai yasa hannayensa ya zagaye kwankwasonta.

“Morning how was your night”

“It was so much fun”

“Ohhh a kara kenan ko?”

Ya dage gira daya with smile.

“No i mean it was boring”

“What?”

Yayi fuskar shanu. Sai tai saurin rufe bakinta.

“No i mean nice”

Yar dariya yai ya juyar da ita ta bashi baya ya saka hannunsa cikin vest dinta.

“Me kike dafa mana?”

“Pizza”

“Oh no Pizza at this early morning?”

“To fada min abunda kake so bayan indomie”

“Indomie kawai na ke so”

“No ba za mu sake cin indomie ba”

Ya dora kansa saman wuyanta still yana ta yawo da hannunsa a tsakanin cikinta zuwa kirjinta.

“You know ina son indomie sosai tana tuna min da ke a duk lokacin da nake cinta it's my favorite”

“It's my favorite too amman yanzu bana sonta”

“Why”

Ya tambaya yana lumshe ido tare da dan cije bakinsa. Sai ta juyo ta dora hannayenta saman wuyansa.

“Saboda kai na ke cinta and now I'm with you, kai ma kuma saboda ni kake sonta kuma yanzu gani a kusa da kai, so we're each other favorites ,we don't need indomie anymore”

“Really”

Ya fada yana dora goshinsa saman nata.

“Yes”

Hancinsa yake goga mata kamin ya kai bakinsa ya tsotsi lebenta na sama. Tsalle tai ta lake kafafunta a kunkurunsa shi kuma ya kara dagota da kyau kamar wata baby. Jikin door din kitchen din ya jingina da ita yana romancing dinta sannan ya sauke yana shafa kitson da ke kanta.

“I love you”

Ya furta kamar mai rada, sai a lokacin ta bude idonta ta ta kalleshi.

“I love you too”

A gida suka wuni, kasancewar sai Monday zai koma aiki, washe gari kuma ya zaga da ita cikin garin ya nuna mata places da dama da bata sani ba. Wasa wasa ta fara sabawa da garin har guraren da bata je ba a da a yanzu duk taje domin week yana fita da ita ya kaita guraren bude ido da kuma shakatawa. Idan kuma suna gida suna a kujera daya a guri daya, every day a bayanta yake kwana ko kuma ya kwanta tana kirjinsa har garin Allah ya waye, wanda ya riga tashi a cikinsu shi zai hada breakfast. Bata da gurin zama sai saman kafafunsa a tare suke cin abinci har wanka tare suke, they spend two years together a paris suna ta rayuwarsu ta jindadi da farinciki.

*** *** ***

A duk yadda take daukin zuwa Nigeria ganin familynta, sai tafiyar ta fita a kanta ta kuma mata babu dadi, saboda damuwa da kuma kukan rashin Dada Yalwa da Zain yake ta yi, ita kanta bata farinciki da tafiyar ta zame mata ba dadi domin ta mutuwa ce ba ta ziyara ba kamar yadda take so.
Irin taron da suka tarar a masarautar Rishim har tsoro ya bata kana gani kasan babban mutum ne ya rasu, duk yadda Zain yayi kokari danne zuciyarta sai ya kasa saboda yayi babban rashin da babu wanda zai maye masa gurbinsa har gaban abada. Da ita kadai ya rayu ita ta raine shi tun be san komai a duniya har ya kawo yanzu. Kukan da Zain yai kusan shi ya saka kowa kuka cikin har da wanda basu yi niyar kukan ba a kokarinsu na danne zuciyarsu. A masarautar akai mata sallah bayan anyi mata sutura, babu kalar addu'ar da Zain be mata ba, Mai Martaba ya nemi alfarmar aka zo da Hameeda daga prison ta ga gawar Dada tai mata addu'a da kuma bankwana sannan aka maida ita, a lokacin da aka dauki gawarta za a bar gidan ta ita sai yaji kamar ya rikota ya tasheta ya dawo da ita.

Har akai amsar gaisuwar aka gama Zain baya cin wani abun kirki babu komai a zuciyarsa sai tunanin Dada Yalwa, idan har ya ci abu mai nauyi sai idan Hafsat ce ta tsare da abincin ta saka shi gaba tai feeding dinsa. Satinsu biyu a garin Gusau, har lokacin ba a daina zuwa musu gaisuwa ba, ana saura sati daya su koma Zain ya kai Hafsat Kaduna gurin iyayenta ta gansu, a ranar da ta dawo ta sha wahala sosai saboda aman da tai ta yi kamar zata amaye hanjin cikinta, sai da aka mata allura sannan ta samu bachi. Washe gari sai ta tashi da karfin jiki, daman Zain ya fada mata tun tana Kaduna cewar idan ta dawo zasu je gurin Hameeda, kasancewar Friday zasu koma.
Daga ita sai shi ne a motar sai kuma direban da yake tukasu, ita dai kallonsa kawai take tana kwatanta irin bakinciki da damuwa na rashin da ke ransa, wani mugun tausayinsa ne ya kamata, a hankali ta kai hannu ta rika hannunsa, sai ya matse hannun nata gam ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya, ita kuma ta kwanto jikinsa tana kallon titi har suka isa.
A dayan bangaren ta fito shi kuma ya fita a dayan bangaren sai ya zagayo gefenta suka jera suka nufi ciki, direbansu na a baya rike da manyan ledodi. Suna zaune a inda aka tanadar dan zama masu kawo ziyara aka fito da Hameeda. Kallo daya tai ma Hafsat ta dauke kai bata a fada wacece matar da Zain ya aura ba, iyajar abunda ta sani Zain ya yi aure domin yan'uwansa da suke kawo mata ziyara suna fada labarin abubuwan da ke faruwa, cikin kuwa har da Dada Yalwa wacce ke kawo mata ziyara every week. Sam bata gane Hafsat ba bata ma kawoma ranta Zain zai auri Hafsat ba. Har ta zauna bata kalli inda Zain yake ba kuma bata ce masa komai ba.

“Hameeda”

Ya kira sunanta yana kallon yadda ta lalace ta koma kamar ba ita ba, idonta har wani baki suka yi saboda kukan da take wanda ya zame mata jiki. Bata amsa ba tana ta kallon kasa kamar ba ta san da su a gurin ba.

“We both lost her, kamar uwa take a garemu and now Mai Martaba kawai ya rage mana”

“Har yanzu kana jin ni yar'uwarka ka ce?”

“Yes no matter what kika yi you're still my blood, wacce Dada ta raina ta girmar da Ita”

“Thank you Zain, amman ina rokon ka yafe min kamin nima tawa ta kasance”

“Ni na riga na yafe miki”

“Nima na yafe miki”

Hafsat ta fada, sai a lokacin ta dago idonta dake zubar da hawaye ta kalleta.

“Ke din wacece?”

“Hafsatu manga, yarinyar kauye, yarinyar da kika dorawa kisan Farhat”

Zain ya amsa mata, kallon ta sosai Hameeda take tana tunanon abubuwan da suka faru, yau gata a prison yarinyar kuma tana tare da Zain.

“Na gode”

Ta furta cikin muryar kuka. Sai ta mike tsaye hakan yasa suma suka tashi tsaye, Zain ya dauki daya daga cikin ledodin da yanzo da su ya mika mata.
Chapter 92 · 0% Book details