← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 93

Sashe 2

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana tsaye jikin fanfo yana wanke hannunsa ya jiyo karar taba gate, hakan yasa shi dagowa ya kalli gurin gate, kasancewar windows kitchen din da kuma dayar kofar duka suna fuskantar gate ne. Yasan Malam Adamu mai gadi be isa dawowa daga aiken da Anty Ummi tai masa ba, to waya turo gate din? Hakan yasa shi maida hankali sosai gurin gate din zuciyarsa cike da son sanin dalilin motsin kofar gate din. Bayan kamar mintuna uku sai aka sake turo gate din, karamin kai ya fara hangowa an ziro ana karewa gidan kallo, kai tsaye ya koma gurin windows yana son tantance abunda yake hangowa tana kallo inda yake sai ta juya ta zira da gudu, shi dai ba zai iya tantance abunda ya hango ba duk kuwa da kasancewar akwai wadataccen haske a ko ina na gidan, mutum ko aljan? Iyakar abunda zai iya tabbatarwa mace ya hango ba namiji ba saboda yawan gashin kanta, kuma karamar yarinyace sai dai idan mutum miyasa be hangota da tufafi complete a jikinta ba, ko dai mahaukaciyace ko kuma aljana haka zuciyarsa take raya masa sai sai tafi raja'a ga cewar aljanar ce ba mahaukaciya ba.
Ji yai bashi da natuwar jiki da ta ruhi har sai ya tabbatar da abunda yake zargi ko ba komai ya kamata ya duba yaga ko minene saboda tsaro ba dan tsoro ba. Ta kofar kitchen din ya fita kai tsaye ya nufi gate din, yana isa ya kai hannu ya bude ya fita waje gaba daya ba tare da fargabar komai ba, cike da natsuwa yake kallon damansa kamin ya juyo zuwa hago, sai dai ko kadan be hango abunda zai sada idanuwansa ga kallon abunda ya gani dazu ba balle kuma har ya sake ganinsa, kamar zai juyo ya koma sai kuma yai gaba kadan ta inda kunnuwansa suke jiyo masa sautin kuka duk da bashi da tabbacin kukan ne. Ba'a iya jin sauwon takunsa balle kuma har mutum ya iya auna tafiyarsa, Yarima Zain irin mutanen nan ne da ba saka ta zuba zance baka saka suna kusa da kai ba har sai kamshin turarensa ya sanar maka da zuwansa, hannayensa duka biyu suna baya har ya karasa inda yake jiyo kukan.
Wannan karon kallon Aljana yai mata dan ta bashi baya ne fuskarta tana kallon karshen kwararo, hakan ya bashi damar kallon bayan kanta da kuma sauraren kukanta, yasan babu abunda zai kawo mutum cikin daren nan kuma a irin wannan gurin ko da kuwa mahaukaciya ce, babu komai a cikin sautin kuka sai.

“Yunwa wayyo yunwa zata kashe ni”

Juyowa yai ya dawo zuciyarsa na raya masa abunda ya kasa natsuwa da shi, miyasa shi kadai ya ganta? Akan mi ya bibiyeta har ya ji tana jin yunwa? Idan be taimaketa da abinci ba mai zai faru da shi? Idan ma da gaske aljana ce mi zata masa?
Har ya dawo cikin kitchen din wadannan tambahoyin ne a ransa, Anty Ummi ya tarar cikin kitchen din tana hada ma yaranta ginger tea. Kallo daya tai masa ta dauke idonta daman tasan yau kanenta baya cikin walwala saboda ta tabo masa inda baya son a tabo masa, bata bukatar tambayar damuwarsa domin hakan ya wuni a gidanta da abarsa. Tsaye yai yana kallon kofar gate din har ta gama hada tea ta mika masa nasa.

“Kamar kana jiran wani”

Ta fada tana kallon gate din ganin yadda ya tattara duka hankalinsa ya maida can. Hannu ya mika ya karbi kofin tea din.

“Maybe...”

Ya fada yana daga kafadunsa tare da tabe baki, sai ya kawar da idonsa daga kallon gate din. Aje kofin yai dan baya jin zai iya shan ginger a yanzu, yana son ya ce Amal ta kawo masa keys din motarsa dake falo kuma yana jin hauyin bude baki yai maganar hakan yasa ya nufi falon da kansa ya dauki keys dinsa ya fita ta kofar falon. Da sauri Anty Ummi ta fita ta kofar kitchen ta zagaya ta nufi inda yake kokarin bude motarsa tun kamin ta karasa ta fara masa fada saboda ranta a bace yake.

“Au kayi fushi kenan ko? Saboda an fada maka gaskiya, kai ba dama a zaunar da kai ayi magana Allah da Annabi? Kanka farau mutuwa da zaka dauki abu ka saka a ranka? Ai ban san son da kake mata ya kai haka ba har sai ka hadiye zuciya ka mutu sai a binneka kusa da ita sannan hankalina zai kwanta”

Tun da ta soma maganar be dago ya kalleta ba har ta gama ta juya ta koma, zaunawa yai cikin motar ya lumshe idonsa yana sauke numfashi a hankali. Ko kadan maganar Anty Ummi bata masa dadi ba, sai dai yasan ranta ne ya bace, kuma bata nufin komai a gareshi sai gyara domin ba zata so wani abun cutarwa ya same shi, ta fi kowa shiga damuwa da halin da yake ciki, shi kuma baya hango abunda take hangowa a matsayen mata a gareshi.

Bayan kamar mintuna biyar zuwa shi da ya tashi motarsa, kamin ya karaso bakin gate din sai ga Malam Adamu ya dawo tare da Farhat Malam Adamu komawa yai gefe ya aje ledodin dake hannunsa ya bude masa gate Farhat kam yin tai yi kamar ba san da mutum a compound din ba ta wani dauke kai ta nufi cikin gidan. Da mugun gudu Zain ya bi ta kusa da ita kamar zai kadeta har sai da ta matsa gafe. Kwafa tai ta nufi kofar falon a fusace.
Anty Ummi na zaune falo Farhat ta shigo kamar an jefota.

“Wallahi Anty Ummi wannan kannen naki bashi da kirki kin ga yadda ya bi kaina da mota kamar zai takani, shiyasa bana son zuwa gidan nan idan yana nan”

Murmushi Anty Ummi tai ta aje kofin ginger dake hannunta ta kama hannun Farhat ta zaunar da ita.

“Kin riga kin san halin Zain amman kullum sai ki tai min complain akan matsalar, yanzu haka it wasn't intentionally amman kin wani fusata, kina da zagar min dan'uwa a gaban idona, kuma wasu abubuwan rayuwarsa ce amman idan baka saba ba sai ka dauka wulakanci yake maka”

“Wallahi da gangan yai, shikenan dan yana dan sarauta sai ya dinga yi ma mutane wulakanci son sansa, haka ranar fa ina zuwan gidan nan ya dinga hararata”

“No no no Zain amman baya harara haka dai kallonsa yake, maybe ya tsareki da idone ke kuma kika tsargu, amman ni nasan waye kanane”

Anty Ummi ta fada tana dariya.

“Ni dai gashi inji Anty Rukaiya tace wai idan na kawo miki ki kirata kayan mata ne...”

Farhat ta fada tana dankama Anty Ummi bakar ledar dake hannunta.

“Ba sai kin fada min ba, na sani marar kunya, tashi kije kar dare ya miki”

Anty Ummi ta fada fuskarta babu alamun wasa, Sai ta ta dauki ragowar ginger da Anty Ummi take sha ta shanye sannan ta tashi ta fita tana mata sai da safe.

Babu wani nisa sosai tsakanin gidansu da gidan Anty Ummi amman hakan be hanata gudu ba duk da kasancewar akwai haske a ko'ina. Ko da ta shiga gidansu har haki take saboda gudun data debo, da sanda ta shiga falon sanin cewar Ya Bashir na nan yana jiranta dawowar daman kamin ta fita ya fada mata zai yi magana da ita. Duk da hankalinsa yana gaban Plasma hakan be hanashi fahimtar shigowarwata ba.

“Farhat bana nace ina son magana da ke ba?”

Cak ta tsaya duk wani kuzari nata sai ya yanke, tsoro da fargaba tare da tunanin abunda zata fada masa suka cika mata zuciya lokaci daya. Zagayowa tai gabansa ta zauna tana mai nuna tsantsar ladabi da biyaya a gareshi ta risinar da kanta kasa tana jiran abunda zai fito daga bakinsa.

“Ya kuka da Auwal?”

“Ya na fada mishi sai ya ce dan Allah ka yi masa uzuri har ya dawo dan sunje Abuja gurin wani meeting da sun dawo zai zo ya sameka”

Kai kawai ya daga mata, ta tashi jiki a sanyaye ta nufi dakinta, da shigar ta maida kofar dakin ta rufe ta fada saman katifarta tana sauke ajiyar zuciya, tana mai jin nauyin irin karyar da tai ma Ya Bashir sai dai idan ba karyar ta masa ba ya zata ce masa? Auwal din ne yaki ya fito a duk lokacin da tai masa maganar aure sai ya kawo mata wani uzurin, iya daga kafa tasan Yayanta yai mata kuma ya bata dukan danar data kamata amman ta kasa gane kan Auwal yadda yake ta mata yawo da hankali a duk lokacin da tai masa maganar aure har ta rasa gane kansa, a iya abunda ta sani zuciyarta tana son Auwal sosai kuma bata jin zata iya rayuwa da wani namijin bayan shi, wannan ne dalilin daya hana ta kula kowa a duk tsawon shekaru hudu da suka kwashe a tare, Auwal gwani ne kuma gwarzon da zai iya cinye ko wane irin kambu na masoya a fashen soyayyar irin tarairayar da kulawar da yake nuna mata a waje take fatan samun a gidansa, irin soyayyar da ake a cikin finafinai da littafai take son su yi ita da shi a gidan aurensu, saboda tana gani da tunanin babu namijin da zai iya bata wannan kulawar da soyayya kamar Auwal dinta.

Farhat mace ce da idan tana son abu takan so shi duka, zata iya mutu da sake mutuwa ta kuma sake mutuwa akan Auwal, a shekara hudu nan da suka yi a tare babu wani a cikin familynta da be san da zancen Auwal ba, kama daga kawayenta har makota da yan'uwanta, tun tana makaranta gashi har ta gama tai service be taba maganar aikawa a gidansu ba, duk kuwa da sakancewar yana mata komai daya kamata saurayi yai ma budurwarsa babu abunda ya rage ta da shi, abu daya ne zai tabbatar wa da Farhat cewar Auwal yana da niyar aurenta saboda gabatarda ita da yai a gaban iyayensa shekaru biyu da suka wuce.

Turo kofar da Anty Rukaiya tai ne ya katse mata tunanin da take.

“Kin ce ta kirani?”

A firgice ta kalli matar yayyan nata.

“Ee tace zata kira ki”

“Better”
Chapter 2 · 0% Book details