Sashe 21
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk irin son da take ma wainar kwai yau kadan ta ci tea ma kadan ta sha ta mika masa ya karba ya aje, sai kallonta yake shi dai kam be san dalili ba amma yana jin ba zai iya barinta ta tafi ba, idan ma ta tafi ina zata je? Da wa zata hadu? Ko da da gaske cutar da shi zata yi ba zai kyaleta ba, dan har ga Allah tausayinta yake ballema yanzu da bata iya furta komai, taya za ayi tadake magana? Shine abunda yafi tsaya masa a rai, ya san wani bangaren Anty Ummi tana da gaskiya, tunda ya kawota asibitin nan rabon da ya kwana a gida, kullum cewa Mai Martaba yake aiki ya masa yawa a asibiti can zai kwana, wunin da yake a gida Anty Ummi ma ya daina saboda kawai ya kula da yarinyar da be san ta inda zata amfaneshi ba, but wani bangaren yana duba maraicinta domin bata da kowa a yanzu dai shi. Hannu ya kai ya shafa gefen fuskarta yana dan murmushi kadan. Ita ma murmushin tai sai ta mika masa hannunta alamar ya bata, da girarsa ya tambaye ta minene? Sai ta dora hannunta saman kunnenta tayi masa alama da waya.
Hannu yasa aljihu ya fiddo wayar ya kunna mata bubble shooter ya mika mata.
Tashi yai tsaye ya fiddo dayar wayarsa ya kira abokisa Ibrahim, ya fice yana kara wayar a kunnensa. Sai da ta kusa katsewa sannan Ibrahim ya dauka.
“Hello...”
“Bachi ma kake”
“Hutu ai dole ne”
“Bana iya tuna when last nayi bachin safe”
“Ai kai ka so”
“To ya zanyi? Abun ya zame min dole ne, yanzu ma Anty Ummi take min wata magana wai bazan kai mata ita gidanta ba, kuma dole Mai Martaba ya san da maganar”
“To minene a ciki ni daman tuntuni ina tunanin ya kamata ace Mai Martaba ya sani Maybe ma zai iya taimaka wajen gane iyayenta”
“No Ibrahim yarinyar nan tana cikin wani hali na bukatar taimako, abu ne mai wahala a iya gane iyayenta a yanzu saboda abunda ya afku wata kila an kashe su, gashi ba magana take ba ko wani abun ne ba fitowa zatayi tai magana ba, ba kowa zai iya kula da ita ba a yanzu”
“Yanzu ya zaka yi da ita?”
“Shiyasa na kira ka”
“Ka kawo ta nan, Zubaida zata kula da ita”
“Look Ibrahim ba ko wace mace bace zata iya daukar dawainiyar yarinyar nan, kasan halinta da rigima kuma abu kadan zata ce ba a mata daidai ba dai kuka, gashi bata iya bachi ita kadai”
Ibrahim ya dan yi shiru na wani lokaci kamin ya ce!
“Ko muyi ma Doc Hafsat magana? Naga tana da kirki kuma sun dan shaku da yarinya.. -”
Be gama maganar ba, Zain ya katse wayar saboda haushi, taya zai kirashi neman shawara ya kawo masa zancen wata can daban macen da ba yar'uwarsa ba be hada komai da ita ba. Cikin jin haushin kiran da yai ma Ibrahim ya bude motarsa ya shiga.
HAMEEDA POV.
A hankali take cin dabinon dake cikin faranti tana wani shu'umin murmushi, murmushin dake kara fitar da muguntar dake zuciyarta, ranta fari kal a yau.
“Allah ya taimaki Shugabata ya tabbatar da wannan farinciki na ki”
Cewar Abida cike da banbadanci tana gyara mata gado. Hameeda ta kara fadada fuskarta da murmushi.
“Anfi wata daya rabon da Yarima ya kwana a gida ko kin lura da hakan?”
“Na lura sosai ma Gimbiyata, a kwanakin baya mun taba wannan maganar da ke”
“A kullum cewa Mai Martaba yake aiki ya masa yawa a asibiti, sanadin hakan yasa baya zama a gidan nan kuma baya kwana a ciki, amman kin san minene?”
“Sai kin fada Gimbiyata”
Tashi tsaye Hameeda tai ta nufi window tana kallon harabar gidan.
“Wata yarinya yake jinya”
“Yarinya kuma? Wacece ita kuma miye alakarsa da ita? Gimbiya ina tsoron kar wata ta dauke masa hankali fa hakarmu yaki cimma ruwa”
“Hakarmu ta cimma ruwa Abida, kadan ya rage mu dibi ruwan mu sha, ba zan taba shukar dusa ba, kuskuren da na tafka a baya ba zan sake tafka irinsa ba, sakaci ne yasa yar'uwata ta auri mijina, a lokacin ina bachi yanzu kuwa na farka, mutuwar Haleema ya isheki ishara, dan haka daga yanzu babu wanda zai shiga gonata ya kwashe lafiya, na dade ina jiran wannan ranar taya zan sake sakarcin da zai sa na rasa Zain?”
Juyowa tai ta kalli Abida dake tsaye a bayanta.
“Ko kin san a can baya babu wacce Zain yake so sai ni? Amman Anty Ummi ta shiga tsakaninmu ita ta haddasa masa kiyayyata a zuciyarsa, dan haka alkawarina ne wannan sai nasata kuka da idanuwanta kamar yadda nima ta sakani”
“Ta cancanci fiye da kukan ma Gimbiya, dukan wanda ya rabaka da masoyinka ya cancanci kisa ma domin shima kokarin kasheka yake...”
Cije lips Hameeda tai tana mai jin tsanar Anty Ummi har cikin ranta.
“Mai Martaba ba zai bar Zain ya auri wata bare ba, yanzu kuma sai naga da wacce bakar matar nan zata bullo...”
“Ai idan baki yasan abunda zai fada be san wanda za a maida masa ba, daman can baya saka ci muka yi shiyasa har zai ya auri wata ba ke ba”
Cewar Abida. Hameeda ta kalleta
“Kaddara ce ta rubuta masa auren yayata kamin ni, yanzu kam kaddara bata rubuta masa auren kowa ba sai Hameeda....!”
Ta karashe maganar cike da kasaita. Juyawa tai tana kallon Zain daya faka motarsa a parking space ya fito ya nufi part dinsa.
“Ina abincinsa yake?”
“Yana sashen Hajiya Yalwa”
“Jeki dauko min ni zan kai masa”
Cikin rawar jiki abida ta fita daga daki, bata dauki tsawon lokaci ba, sai gata ta dawo dauke da tray abincin ta aje gaban Gimbiya Hameeda.
“Gashi ranki ya dade”
Kai kawai ta daga mata sai ta juya ta fice. Ita kuma ta dauki abinci ta nufi sashensa da shi. Door bell ta danna sau daya dan tasan baya son ayi ta dannawa ko ayi ta knocked anyhow, bayan kamar minti goma ya bude kofar.
“Ina Abida?”
Ya tambayata dan ba kasafai yake son tana zuwa part dinsa ba, duk da kasancewar a yanzu suna dan samu fahimtar juna ba kamar baya ba, saboda fadan da Mai Martaba yai musu.
“Na aiketa ne shiyasa na kawo maka da kaina”
Ta fada bayan ta shigo falon ta dire masa abincin a dinning.
“Muna da masu hidima da yawa a gidan nan, ko bayan Abida wata zata iya yi ba dole sai ke ba”
“Bana jin kaskantar da kai a abunda na aikata, ko kuma wadanda zan aikata a nan gaba, ko ba komai kai mijin yayata ne kuma dan'uwana dan haka ka cancanci girmamawa daga gareni ta ko wanne fanni, besides a yanzu ba kasafai nake son shigowa part din da yar'uwata ta rayu ba, ko ba komai yana tuna min da ita, a halin yanzu nafi son Haleema ta fiye min komai aduniyar nan Zain na taka wani mataki da kai kanka idan na ganka raina baci yake saboda yana tuna min da ita... ”
Sai kuma tai shiru ta nufi kofar fita, sai da ta kai hannu ta murda kofar ta bude sannan ta juyo ta kalleshi.
“Kwana biyu baka kwana a gida...”
Shiru yai kamar ba zai amsa mata ba, yana cire agogon hannunsa.
“Aiki ne yake min yawa”
“Ka tabbata?”
Dagowa yai ya kalleta, ba shiri ta hadiye yawun dake bakinta ta sha jinin jikinta.
“Ina nufin idan kana bukatar wani taimako zan iya taimaka maka...”
Tayi shiru fuskarta narau-narau gwanin tausayi sai yawo take da idonta a falon kamar bakonta.
“Kasan wani abu Yarima? Wani lokacin baka taba sanin muhimmanci abu har sai ranar da ya subuce maka, masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce duniya makaranta ce mai ajujuwa da yawa kuma mai darussa mabanbanta, rayuwa tana zuwa ma bawa ba a yadda ya tsammace ta ba, in seconds komai zai iya canjawa include rayuwa, tunani, buri, ra'ayi da ma wasu abubuwan da dama...
Wani lokacin mutum yana da bukatar abokin tattauna musamman na kusa da kai, a misali ni! Bani da abokin fira wanda zan saurareni na fada masa damuwata ya fahimce ni har ya sama min mafita, na tashi ban san mahaifiyata ba, dan haka ban san dadi da rahamar dake jikin uwa ba, daga baya kuma sai na rasa mahaifina, yanzu kuma yar'uwata wace ita kadai ta rage min, na koma ni kadai sai cousins sai kuma waenda muke uba daya da su...”
Ganin ya maida hankalinsa sosai akan maganar da take ya bata dama cigaba.
“Duniya tana da daci a gareni Yarima, wata maganar ba zanyi ta da Dada Yalwa ba, ba komai ne zan fadawa Mai Martaba ba, ba kowace shawara zan yi da mutum ya fahimta ba, ba kuma kowa ne yake iya rike min sirrina ba..”
Ya dauke kansa daga barin kallonta, hakan ya bata damar busar da iskar dake bakinta, ta lumshe idonta tana budewa ta saukesu cikin nasa.
“Dukan abunda nake ina yi saboda Mai Martaba, bana son na sake yin abunda zaisa ya zargeni da laifi, zuciyata ba zata iya daukar komai da komai ba Zain, amman zan iya rushe tawa rayuwar saboda na gina ta wasu, ko ba komai nasan tawa rayuwar gajera ce mai cike da kunci...”
Ta karashe maganar cikin tattausan lafazi hawaye na silalo daga idonta, juyawa tai kamar marar kuzari ta fice daga falon taja masa kofa.
FARHAT POV.
ONE MONTH LATER....