Sashe 29
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Da kina tsoron fushina da baki auri wani ba sai Auwal, miye yar'uwarki bata miki ba? Ku nawa na haifa? Ku biyar na haifa amman ke ta dauka ta rike ta sakaki boko kika waye bayan kuma ga yan'uwanta can wadanda suke uwa daya uba daya babu abunda basu ce ba lokacin da ta daukeki amman ta toshe kunnuwanta ta zauna da ke, sai ke yanzu dan ance ki auri mijinta ki rike mata yayanta sai kice ba zaki iya ba, ai gashi can yanzu sun dauki kanwarta wacce suke daki daya sun bashi sai ki zuba ruwa kasa ki sha, ba baki nake miki ba amman wannan auren ba zaki taba samun farinciki a cikinsa ba, ba auren kudi kikayi ba dan kinga dan sarki? Gaki ga shi ai basa ganin talaka da daraja”
“Ba kisan yadda nake ji ba Inna, Wallahi idan na auri Ya Bashir mutuwa zan yi”
“Ai da shi kika aura ana kaiki sai ki fadi ki mutu zai fi min kwanciyar hankali fiye da wannan da kika aura, tashi ki bani guri kuma karki kuskura ki shaida min duk abunda zai biyo baya....”
Tashi tai tsaye sai kuma ta fadi zaune ta rike kafafun mahaifiyarta ta fashe da kuka, kuka tai sosai sannan ta tashi ta fita a lokacin ne idon Inna ya cika da kwalla.
Kamar kwacce aka cirewa rai haka ta fito daga dakin Inna tana kuka, daya faga cikin dattijiwar da zasu rakata ta rika hannunta ta sakata cikin mota, sauran suka shiga a dayar motar dogaran suka kama hanyar Gusau da su.
Har suka isa cikin birnin Gusau Farhat bata daina kuka ba, idonta duk ya kumbura fatar fuskarta tayi ja sosai saboda murjar da take. Tayi tunani gidan sarki za a wuce da ita sai aka nufi wata unguwar da ita wacce ba zata iya tantancewa ba, sakancewarta sabuwar unguwa dake can bypass hanyar kaduna.
Babu kowa a cikin gidan sai dogarai da kuma bayi, domin su suka tarbesu dayar ta rika hannunta dayar ma ta kama hannunta suka nufi wani bangare na gidan da ita.
Kato gidane plate mai girma da aka kawata ko ina da fulawoyi. Babban falo suka shiga da ita har lokacin hawaye be daina sauka a idon Farhat ba.
Suna shigowa Abida ta zube kasa tana kausar gaisuwa.
“Allah ya taimaki Gimbiya, Allah yaja kwanaki muna barka da zuwa a wannan masarauta mai dinbin albarka da alfarma, takawarki lafiya surukar mai martaba surukar da tafi ko wace suruka daraja da sa'a a duniya...”
Bayan ta gama ta dauki wani carpet ta shimfida a saman carpet din dake falon.
“Shimfidar nan taki ce Gimbiyata Allah ya taimakeki ya kara miki imani da nisan kwana”
Karasa Farhat tai ta zauna sannan ta kai hannu ta share hawayenta. Hannu biyu Abida ta taba sai ga wasu bayin uku sun fito dauke da abinci suka dire gaban Farhat sannan suka kwashi gaisuwa. Da ido Abida tai musu magana dai duk suka tashi suka fice, sannan ta kalli gefen da Farhat take dan ba zata iya kallonta kai tsaye ba.
“Idan Gimbiya ta min izini zan fita waje domin yin wani aikin”
Kallonta Farhat tai tana tunani abunda zata ce mata, in her life wani be taba neman izininta dan yin wani abun daya shafi rayuwarsa.
“Ranki ya dade ko akwai wani abun da kike so ne?”
“Aa tashi ki tafiyarki”
“Na gode Gimbiya, Allah ya taimakeki”
Abida ta tashi ta fice daga falon cikin sauri, wani bangare na gidan ta nufa inda babu kowa sai shukeshuke, tsohuwar nokia ta dake cikin zane ta fito da ita ta saka number Hameeda ta kirata bugu daya ta dauka kamar mai jira.
“Ta ci abinci?”
“Aa yanzu suka iso, amman gashi can an kawo mata”
“Ki tabbatar fa ita kadai zata ci shi ba tare da kowa ba, duk kika yi kuskure wani ya ci bayan ita kin shiga uku, kuma idan ta gama cin abinci ki dauke shi ki zubar inda babu wanda zai iya gani”
“To ranki ya dade amman ina jin tsoro”
“Kiyi ta sanyi jiki har tsoronki ya ja miki asirinki ya tonu, kiga yadda zan yi dake a cikin masarautar nan”
Ta kashe wayar tare da yin kwafa. Abida ta dade rike da wayar kamin ta maidata a cikin zanenta ta nufi dayan bangaren inda aka sauke yan'uwanta, ko da ta shiga suna cin abinci da aka kai musu cikin girmamawa ta gaishesu, suma suka amsa mata da far'ah
“Idan kun gama, direba zai maidaku ga kayayyaki can Mai Martaba ya ce a baku”
Sai kuma ta tashi ta shiga wani dakin ta dauko wata farar takarda mai kamar ta sako ta mikawa gwaggonta.
“Ga wannan daga Hajiya Hadiza uwargidan Mai Martaba sunce a gaisheku, akwai atamfa da shadda a dayan motar su kuma daga Hajiya Zarah da Hajiya Maryam ne sukansu matan Mai Martaba ne”
Godiya sosai suka rika yi mata har suka rasa wani abun kara cewa, bayan sun gama ne Abida ta kaisu inda Farhat take suka mata sallama tare da yi mata addu'a sannan suka tafi, suna fita ta fashe da kuka kamar ance mata sun tafi sun bar ne kenan har a bada. Har gurin mota Abida ta raka su, sai ta ta shiga motar aka wuce da su sannan ta dawo gurin Farhat ta tarararda ita har yanzu tana aikin kuka.
“Haba Gimbiya kuka be kama ci wannan fuskar taki ba, farinciki ya kamata ki yi domin Allah ya kawo ki inda hawayen bakinciki ba zasu sake ziyartar idanuwanki”
“Rabuwa da yan'uwa babu dadi”
Farhat ta fada tana share hawayenta.
“Na sani Gimbiya amman wannan ai ba rabuwa ba ce ta har a bada, zaki sake ganinsu a duk lokacin da kika zo, yanzu dai ki share hawayenki ki ci abinci, Allah ya taimakeki”
“Ki daina ce min Gimbiya ni sunana Farhat”
“Ba zan iya kiranki haka ba ko da kuwa za a dora kaina saman dutse a dauki wani dutsen a fasashi, ni dai burina Gimbiyata ta ci wannan abinci”
“Ba zan iya ci ba, bana jin yunwa”
“Dan Allah dan Annabi ki ci abincin nan, ida aka bincika baki ci abinci nan ba ni za'ayiwa fada wata kila ma a koreni”
“Saboda ban ci abinci za a koreki”
“Kwarai kuwa kina da girma da martaba a gurin Mai Martaba, domin kin auri dan da yafi so cikin yayansa, kuma da namiji tilo a gurinsa, ai kekan yar gata ce gaba da baya”
Jin abunda Abida ta fada na cewar za a koreta idan bata ci abincin ba, yasa ta dauki plate ta zuba sinasir din da miya ta soma ci, haka Abida ta tisata a gaba tana kallon har ta gama cin abinci sannan ta kwashe kayan.
Farhat na zaune gidan har karfe takwas na dare, bayan ta gama sallah isha'i suna zaune tare da Abida sai knocked suka ji, cikin sauri Farhat taja gyalenta ta rufe kanta, abida kuma ta tashi ta fita daga bedroom din zuwa falon dan bude kofar. Ikram ce tare da kanwarta Sanaya, faduwa Abida tai ta kwashi gaisuwa, ko kula ta basu yi ba suka wuce cikin falon tare da barorin dake take musu baya, Ikram ce tai riga shiga dakin fuskarta dauke da murmushi, bakin gadon ta zauna tare kusa da Farhat.
“Amaryar mu, ko kuma na ce yayarmu ina fatar kina lafiya”
“Lafiya kalau”
Hannu ta mika sai daya daga cikin barorin ta miko mata wani kwali da aka nade da farar leda ta aje mata.
“Ga kyauta gada mahaifiyar mijinki, kuma sarakuwarki, tashi ki gyara zamu wuce masarauta yanzu”
Ikram na gama fadar hakan ta tashi ta fito daga dakin tare da Sanaya da barori uku da suka rakosu, bayan sun fita ne Farhat ta bude kwali farin lace ne a cikin mai mugun kyau da tsada sai farar alkibba da fararen takalma da kuma turare mai shegen kamshi. Tashi tai ta shiga bathroom tai wanka tana fito ta shafa mai ta dauki tufafin ta saka tare da alkibbar sannan ta feshe jikinta da turare, sai ta nufi kofar ta tare da fadin.
“Na gama”
Dukan kallonta suka yi.
“Masha-Allah ni daman nasan Yarima ba zai mana zaben tumun dare ba, duk abunda yasa Yaya ya kawarda fuskarsa ya auro wata bare to abun nan mai girma ne, sai dai kin manta da wani abu Yayan sarakuna basa kawo kansu idan ana nemansu sai dai aje inda suke a tararda su, fatar nan gaba ba zaki sake kuskuren kawo kanki da kanki ba”
Ikram ta karasa fada tana rika hannunta. Ita kuma ta gyada kai sannan suka fice tare da ita. Ko da suka isa masarautar Rishim tayi tsif kamar babu kowa a cikinta, a kusa da kofar fada dogare ya faka motarsa suka fito tare da Farhat. Sai ga wasu barorin sun zo da gudu sun rika albbibarta dake jan kasa. Faduwa gaban Farhat yayi irin faduwar nan na bakunta da kuma tsoro a lokaci daya, a yau dai ta shigo masarautar Rishim a matsayin suruka, masarautar da bata taba ganinta da ido ba sai dai a waya shi ma kuma wani bangare na masarautar ake dauka. A duk yadda za a misaltawa mutum girma, fadin da kuma kyaun masarautar ya wuce misali, daga lokacin da mutum ya saka kafarsa a cikin masarautar sai duniya ta canja masa ta kaishe wata kasar ta larabawa saboda tsaruwarta, sai ka rantse da Allah ba a Nigeria kake ba, kofar fadar ma abar kallo ce balle kuma cikinta.
Suna isa bakin kofar aka bude musu kofar, Farhat na saka kafatarta sai taji kamar tana cikin ruwa saboda sanyi da laushi da carpet din yake da shi, bata daga kanta ba har suka isa gaban wata katuwar kujera dake saman stairs. A tare da Ikram suka zauna Ikram ta gabatarwa Mai Martaba ita sannan ta juyo ta kalli bangaren iyayenta tana gabatar musu da ita, Hajiya Hadiza ce kawai ta amsa da far'a sauran duk shiru suka yi suka bata fuska.
“Lale marhabun da sarakuwarmu, muna miki barka da zuwa masarautar Rishim, Allah ya sanyawa rayuwar aurenku albarka”
“Godiya take ranki ya dade”