← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 93

Sashe 13

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Magana take kamar tabbabiya, kana kallonta kasan kokarin fita hayyacinta take, sai lalaben hannun Anty Ummi take wai wayarta take nema, hawaye dake zuba a fuskarta kai kace fanfo aka bude. Hannunta Anty Ummi ta rika ta nufi dakinta da ita, saman gadonta ta zaunar da ita sannan ta cire mata Hijab din dake jikinsa ta kwantar da ita saman gadon.

“Yi bachi Farhat kina da bukatar bachi”

Anty Ummi ta fada idonta cike tab da kwalla.

“Anty sanyi nake ji, kaina ciwo yake ko ina a jikina ina jinsa kamar ba nawa ba, zuciyana kamar zata tsage biyu nake ji”

Bedsheet Anty Ummi ta dauka ta lullubeta hawayen na mata zuba. Juyawa tai ta fice daga dakin taja mata kofa, falo taxo ta xauna sai ta rasa abunda xata fara tunanin rashin kyautarwa Anty Ummi ko kuma cin amanar Auwal? Wani mugun tausayin Farhat ne ya lullube mata zuciya, abun ne mai wahala ace Farhat ta iya rayuwa a kauye a halin yanzu, idan kuma ta kara gaba bata san wane hali zata shiga ba, gata marainiya ga cin amanar da Auwal yayi mata, hawaye take sosai tana auna kanta a mazaunin Farhat idan har ita ce ya zata dauki kaddara uku a lokaci daya?
Hankalinta ya dauku sosai har bata ji tsayawar motar Zain ba sai shigowarsa ta ji shima dan kofar falon tayi kara ne, sai tai saurin share hawayenta ta kalleshi, shima kallonta yake irin kallon nan na neman dalilin kukan yayar tashi dan yaga damuwa shimfide a fuskarta. Har ya zauna be dauke idonsa akanta ba, ba kasafai yake ganin kukan Anty Ummi ba, so that's duk abunda ya saka ta kuka yana da muhimmanci a rayuwarta ko kuma ta taba mata zuciya matuka.

“Mutuwa aka yi?”

Ta girgirza masa kai, daga haka be kara tambayarta ba, dan yasan ba zata bashi amsa a yanxu ba har sai ta samu natsuwa.

“Ina Mama take?”

Ta dago tana masa kallon rashin fahimta tare ta saka hannayenta ta share hawayenta.

“Wace Mama?”

Ta tambaya cikin muryata mai kama da mura.

“Baba Asabe bata fada miki komai ba?”

“Ban ma ganta ba, tana can ciki tana aiki”

“Mai sunan Mama nake nufi yarinyar data gudu”

“Ina ka sameta?”

Ta tambaya tana gyara zamanta.

“Wani mai mota ne ya kadeta sai ya kawota asibitin mu”

“Subhanallahi tana ina yanzu?”

“Tana cikin gidan nan”

“Ban gane ba, daga asibitin ka kawo ta gidan nan?”

“Kuka take wai bata son asibiti shiyasa na kawo ta”

“Again? Zain miyasa baka bari shi da ya kadeta yaje da ita ba? Ai ba kadai kake son lada ba, baka san inda yarinyar nan ta fito ba dan me zaka rika shigar da ita jikinka ne?”

Tsaya yai kallonta kamar ba hausa take masa ba, can kuma ya dauke kansa ya maida gurin plama.

“Kawai yarinyar tana kwanta min ne”

“Tana kwanta maka kamar ya?”

“Kamar dai haka...”

Ya daga kafadunsa biyu yana tabe baki, sannan ya tashi ya nufi dakin yara, Anty Ummi tashi tai ta bishi zuciyarta cike da rashin fahimtar yarin da ya mata. Ganin abincinta kawai babu ita yasa gabansa faduwa, juyowa yai ya kalli Anty Ummi ita ta kalleshi, sannan ya karasa cikin dakin yana dube dube. Kafafunta da basu karasa shigewa karkashin gado ba ya tsinyaka, sai ya isa gurin ya mika hannunsa ya jayowa. Bachinta take hankali kwance har da minshari, hannunsa yasa ya dauketa ya dora saman gadon Amal.
Anty Ummi dai kallonsa kawai take har ya dorata saman gadon ya juyo ya fito, sai ita ta fito tana fadin

“Miyasa ba zaka kaita gidanku ba sai gidana?”

Tsayawa yai kana ya juyo ya kalleta.

“Saboda nan din ma gidanmu ne, ki tausaya mata Anty baki ganin halin da take ciki? Ni na dauka ma ita kike yi ma kuka”

Da shigar zolaya yai maganar amman fuskarsa babu dariya sai dan murmushin kadan.

“Haka kawai zan zauna ina mata kuka, yarinyar da ban san ma da zuwanta gidana ba?”

“Fada min abunda ya saki kuka? Kin sani jin babu dadi ina ganin kamar na miki laifi ko kuma wani ya bata miki rai?”

Ajiyar zuciya ta sauke, ta gumde bakinta ta bude sannan tace

“Ban san yadda zaka kalli abun ba, Farhat ce take bani tausayi, wai Auwal ya fasa aurenta... ”

Tabe baki yai irin abun be dame shi ba, kuma be bashi mamaki ba, ya nufi dinning ya dauki kofin tea ta zuba ruwan zafi ya soma jefa sugar.

“Ai daman ba zai aureta ba, duk wani namiji mai mutunci ai ba zai aure Farhat ba, wata kila ya gama da ita shiyasa ba zai aureta ba”

Anty Ummi ta zaro ido.

“Zain zato zunubi ne, Wallahi Farhat yarinyar kirki ce”

Be dai ce komai ba, ya dauki tea sa da yanka uku na bread ya koma saman cushion din falo ya zauna yana sha. Ita kuma ta cigaba da hadama mijinta tea da take hada masa ta dauka ta nufi part dinsa cike da jin haushin Zain saboda furucin da ya yi akan Farhat. Sai goma saura ta fito daga part din mijinta zuwa harabar da ake aje motoci, suna tafw tana masa fira har ya shiga motarsa. Ba ta bar wajen ba sai da motarsa ta fita daga gidan gaba daya. Sannan ta biyo ta kofar falo ta shigo part dinta.

Baba Asabe kawai ta tarar a falon tana fusa air freshener, dan shine last aikin da take bayan ta gama ko wane aiki.

“Ina Zain?”

“Yana gama karyawa ya fita”

Baba Asabe ta amsa mata.

“Tare da yarinyar ya fita?”

“Aa shi kadai ya fita”

Sai da ta leka dakin ta hango Hafsat kwance sannan ta nufi dakinta, a nan ma ta samu Farhat tana ta sharar bachi sai faman sauke ajiyar zuciya take. A gaggauce Anty Ummi ta shirya dan tayi latti zuwa aiki yau, gashi har goma da ashirin ta yi. Ko da ta fito Baba Asabe bata falon kuma bata kitchen da alama tana bq inda dakinta yake ita da yar jikanyarta. Tsabar sauri bata ma janyo kofar falon ba ta fito ta shiga motarta ta yi mata key, a bakin gate ta tsaya ta mikawa Malam Adamu dari biyar

“Dan Allah ka karbo mana green beans da carrot ka bawa Baba Asabe jollof za ayi”

Yasa hannu biyu ya karba yana fadin

“To Hajiya a dawo lafiya”

Bayan ta fice ya maida gate din ya rufe, sai ga Hafsat ta fito daga falon ta doso inda yake tana tafiya kadan kadan.

“Ina zaki je?”

Tayi shiru kamar mai tunanin abunda zata ce.

“Koma can cikin gida”

Kamar gaske sai ta juya ta koma, shi kuma ganin hakan tasa ya fita zuwa titi domin siyo kayan. Tana ganin ya fice ta dawo gurin gate din ta tsaya, a tunaninta yayi nisa hakan yasa ta bude gate din ta fito. Hango ta fito yasa shi dawowa, a maimakon ta koma sai ta kara sauri har da son hadawa da gudu dar kar ya tararda ita.
Tafiya take tana waigensa, bata kallon gabanta ita dai burinta kar ya tararda ita sai kace wace tasan wani gurin zuwa. Kamar an dauketa an jefa haka ta fada cikin kwalbati dake gefen gidaje, hodin dake ciki ya daki bakinta har sai da hakuranta biyu suka datse halshenta ya fito waje....!

https://my.w.tt/QM4r0PWFl3

*HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_

Wattpad @KhadeejaCandy

1⃣2⃣

YARIMA ZAIN POV.

Tun da suka fito tiyata yake jin ba dadi, ba kuma na rashin lafiya ko na bacin rai ba, jikinsa na bashi kamar wani abu ya faru da shi ko kuma zai faru da shi ko wani nashi.
Tafiya yake kamar mai tausayi kasa, a yadda ya sake fuskarsa zaka dauka murmushi yake maka saboda yadda ya samu kansa a yanzu shi ba farinciki ba kuma ba damuwa ba.

Duk inda ya ratsa gaisheshi ake amman be daga kai ya amsa ba balle ya amsa musu, a kasaitaccen office dinsa ya shiga, wanda aka kawata da kayan ado na zamani irin wanda ake gyara manyan offices da su, sai da ya zauna saman kujerarsa mai juyawa sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali.
Wayarsa ya dauko ya shiga contactlist dinsa neman Number Ikram, dialing yai in few minutes aka dauka muryar Hameeda yaji bakinta kumshe da sallama.

“Assalamu Alaikum”

Wani dip yai kamar ba zai amsa sallamar ba, yaji kamar kar ya amsa sallama.

“Ina Ikram?”

Ya tambaya yana wani hade rai kamar ance masa tana gabansa.

“Bata kusa, kana da bukatar wani abun ne”

Be jin zai iya kara amsa mata, sai kawai ya sauke wayar, daman yana son ya tambaya ne idam Mai Martaba yana gida kuma yana lafiya, duk da kasancewar yasan ya baroshi lafiya amman yana da bukatar jin lafiyarsa, saboda abunda yake ji, obviously jin muryar Hameeda ya hana shi tambayar hakan. Juyi ya soma yi saman kujerar yana lilo, bayan Mai Martaba Anty Ummi ce mutum ta biyu da suka fi kowa muhimmanci a rayuwarsa, it could be her wani abun ya sameta ko zai sameta, numberta yai dialing ringing biyu ta dauka.

“Doctor”

“Professor”

“Ya aka yi?”

“Kalau, kawai ina son ji daga gareki ne”

Jimm tai, dan tasan ya saba kiranta a duk lokacin da yake tunanin wani abun ya sameta.

“Lafiya ta kalau, sai dai ko Mai Martaba”

“Na kira Ikram yanzu Hameeda ta dauka da akwai wani abun da zasu sanar da ni, kina gurin aiki ne?”

“Yeah ban dade da zuwa ba na zo late ma”

“To ina kika bar Mama?”

“Wace Mama...?”

Tuna Hafsat yasa ta ce

“Oh tana can tana bachi”

“Ita kadai?”

“Baba Asabe ai tana nan, kuma Farhat ma tana dakina tana bachi”

“Haba Anty kin san Farhat din nan ba wani hankali ya isheta ba, last time ma ba ita ta bude mata kofa ta fita ba, kuma ita ma Baba Asabe idan ba magana kika mata ba ai zata iya barinta ta fita...”

“Hey hey hey... karka dame ni da zacen wata yarinyar kauye, aiki nake yi sai anjima”
Chapter 13 · 0% Book details