Sashe 39
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Rama cuta ga macuci ibada ne, cutarwar da kika min sai na ninka miki ita Anty Ummi sai nasa an wulakanta...”
[3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *HAFSATU MANGA*
30
Yau kwanan Zain biyu be leka inda Anty Ummi ba, wanda a da baya iya zama sai yaje idan ma be wuni can ba da dare sai ya lekata. Ita kuma bata sake kiransa ba, duk wata magana da yai da Juwairriya akan mutumen da aka bawa Hafsatu manga ta gurin Ibrahim amman wai tsakaninsa da Anty Ummi kai tsaye ba.
Be taba samman Hafsatu manga ta zauna a ransa sosai ba sai yanzu, duk wani motsi da zai yi tunaninta ne a ransa, ya kasa samun sukuni kamar yadda yake tunanin ita ma bata cikin walwala da jindadi, mafarkinta yake a duk dare mafarkin rayuwar da su kai a asibiti da kuma gidansu Anty Ummi, tunaninta yana tuna masa da Haleema, yana jin kamar ba zai iya rasa Hafsatu ba a yanzu, but wai Haleema matarsa ce kuma yar'uwarsa Hafsatu fa wace irin alakace a tsakaninsu da har yake jinta da muhimmanci a zuciyarsa.
“Ga abinci can na gama”
A can cikin duniyar tunaninsa ya jiyo muryar Farhat dake risine a gabansa. Idanuwan dake lumshe ya bude ya watsa mata wata muguwar harara, ita kanta yanzu ya tsaneta saboda Anty Ummi.
“Sai yaushe za ki saba da daina taya min abincinki?”
“Sai ranar daka fahimce minene aure ka dawo ma hanya”
Ya sake kallonta da kyau, kamar zai ce wani abu sai kuma ya tashi ya nufi Upstairs, tashi tai ta shiga gabansa tana kallon cikin idonsa.
“Kana min yadda kake so Zain, ni ba matarka ce ba baiwar ka ba, amman baka min magana kamar zaman gaba muke da kai a gidan nan, idan har ka bude baki kai min magana sai idan wata maganar ce marar dadi zaka fada min, baka cin abinci ka hana ni shiga dakinka kullum babu annuri a fuskarka kamar an maka mutuwa, dukan abunda nake ina yi ne saboda na samu aljannata kuma na faranta maka amman kai baka gani sai kokarin munana min kake”
Ta karasa maganar muryarta na rawa hawaye na sauka a idonta.
“Ki adana kukanki domin akwai ranar da zai taimakeki, be kamata ki fara kuka a yanzu ba, ba kin zabi zama da mijinta wata?mijin da soyayyar wata mace ta ginu a zuciyarsa, ta yadda wata mace mai kamala da tarbiya ba zata taba samu gurbi a zuciyarsa ba, balle ke da sai da kika yi aure kika san hanyar neman aljanna, dacan baki san da aljanna ba shiyasa kike barin wasu maza suna ganin surarki? Ba zan taba son ki Farhat duk abunda zaki yi ba zaki burgeni ba, babu abun burgewa gurin macen data yada mutumci a hanya tayi mu'alama da maza kala ciki har da mijin yayarta....!”
Yana gama fadar hakan ya ratsa gefenta ya haye sama. Tsaye tai a gurin kamar an dasata, wasu tawayen hawaye suna sauko mata, maganarsa ta daki zuciyarsa ta huda har gadon bayanta, a take duniyarta ta rikice tunaninta ya fara yi mata gudun ruwa, kalaman mahaifiyarta na mata yawo a kwalwalwa. Cike da nauyin jiki ta daga kafarta tana takawa amman sai taji kamar ba takawa take ba, kamar wacce bata da lakka a jikinta haka ta zauna saman cushion ta saka dayan hannunta ta dafe kanta.
Ba a taba fada mata magana mai daci marar dadin ji kamar yadda Zain ya fada mata a yanzu ba. Ta dade a gurin zaune tana jin zuciyarta tayi mata wani mugun nauyi har numfashinta na kokuwar subuce mata. Sai da taji ana kiran sallah la'asar sannan ta samu unkurawa ta tashi ta nufi dakinta. Tsayawa tai kallon dakin tana masa kallon kurrillah.
“Indai har zan zauna da mijin wata ya fada min magana marar dadi akan matarsa, to ko nafi cancanta dana zauna da mijin yayata yafi dace na fuskanci wannan kalubalen a gurinsa, amman zan koya maka darasi Zain, sai na maka bitar karatun da baka manta”
Ta fada tana hade wani abu mai daci daya tsaya mata a makoshi. Kayan dake jikinta ta cire ta shiga bathroom tai wanka, sai da ta zabi lace mai kyau ta saka ta chaba kwalliya, sannan ta sauko downstairs ta zauna saman cushion, ta gabanta Zain ya bi ya wuce hannusa da fuskarsa jike da ruwa da alama alwala yai, ko da wasa bata kalli inda yake ba har ya fice daga falon. Tana jin tashin motarsa ta tashi ta nufi kofar fita daga falon, gabanta ya fadi da farko saboda abunda take son aiwatarta ta ina zata fara?
Tsaye tai a bakin kofar tana tunani kamin ta daga saket dinta ta nufi gate din gidan ta tsaya tana kalle kalle. Kamar an turo Abida sai gata da gudu ta zo ta risina gabanta.
“Allah ya taimakeki da abunda kika bukata”
She act like princess domin ta kusa minti daya zuwa biyu kamin ta amsawa Abida.
“Yarima yace a shirya min mota zan fita yanzu”
Abida ta dago ta kalleta sai kuma tai saurin maida kanta kasa.
“To ranki ya dade”
Juyowa tai ta dawo part din gabanta sai faduwa yake, ala ala take kar Zain ya dawota san zata samu damar aiwatar da bukatarta ba. Tana shiga ciki ta dauki mayafi ta rufe kanta sai kuma ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta, ta cikin madubin ta hango Hameeda wacce ta shigo dakin yanzu.
“Ina zaki je?”
“A iya sanina ke kanwar Zain ce ba yayarsa ba, baki da hurumin tambayar inda zanje balle idan na dawo ki tambayi daga ina nake”
“Al'adar masarautar nan ce amarya bata fita sai nan da wata biyar, kuma ina tunanin kina daya daga cikin mutane da basu fahimci fada sosai ba”
“Ba ke ya kamata ki min biyar sharudan gidanku ba, wanda ya dace yai miki tuni ya yi aikinsa, kuma da amincewarsa zan fita”
Farhat na kaiwa nan ta juyo ta nufi kofar fita, ganin Hameeda na tsaye a gurin yasa ta juyo.
“Idan kallon dakin dadi yake min, zan bar miki makulli sai ki rufe min”
“Bana daya daga cikin talakawan garin Gusau balle kuma bayi, babu dalilin da zai sa na karbi makulli na rufe miki daki, ban ga abun kallon a dakin ba, ina ganin ke ce bakuwar naira shiyasa aka zuba miki su ki kalla iya kallonki”
Tana gama fadar hakan ta fice daga dakin, Farhat ta rufa mata baya. A falo ta samu Abida risine tana fada mata ga motar can an shirya. Gurin da Zain yake aje keys din gidan ta nufa ta dauki ta mika Abida ba tare da tace mata komai ba. Tana gaba Abida na biya harta fita daga falon sannan Abida ta rufe kofar ta mika mata keys din.
“Gada biyu”
Ta fadawa mutumen dake gaban motar sanye da jajayen kaya na dogarai.
“To Ranki ya dade”
Tun da ya kama hanyar be tsaya ko ina ba sai gidansu Anty Ummi kamar yadda ta kwatanta masa, shi ya fitoya bude mata motar ta fita.
“Ka koma anjima Yarima Zain koma da ni”
“To ranki ya dade”
Tura kofar gate din tai ta shiga, Malam Adamu yai mata maraba sama sama suka gaisa ta karasa cikin gidan. Bugu daya tai Baba Asabe ta bude mata kofar.
“A maraba da Farhat”
“Anty Ummi na nan?”
“Eh tana ciki bata jindadi”
Cikin saurin Farhat ta nufi dakinta, da sallama ta shiga Anty Ummi dake kwance saman gado ta dago ta amsa mata.
“Farhat ke ce yanzu?”
“Eh Anty bakida lafiya?”
“Ee tare da Zain kuke? Aa ni kadai na ke”
“Lafiya kalau Anty, wayar da kika min alkwari nake so”
Anty Ummi ta tsaya kallonta. Sai ta zauna bakin gadon tana fadin
“Anty kadai ce ya dame ni, ina bukatar waya ko dan chat kuma ina son waya da Mamana, i miss my friends”
“Nasa an miki welcome back din sim dinki, amman ban siya miki waya ba sai Zain ya yarda”
“Ina Sim din yake? Can I borrow your phone”
Anty Ummi ta nuna mata inda wayar take, kamin ta sauka daga kan gadon ta bude drawer ta dauko layin ta mika mata. Cikin sauri Farhat ta dauki wayar ta tashi ta fice dga dakin ba tare data karbi layin ba. Ta kusan awa daya a harabar gidan sannan ta dawo ta mikawa Anty Ummi wayarta ta karbi layin.
“Na gode Anty Ummi, amman ko karamin wayarki ba zaki bani ba na saka layina?”
“Babu abunda zan baki har sai Zain ya amince, ina fatar da izininsa kika zo nan?”
“E ya sani ya mace na gaisheki”
Ta fada tana dariya kamar gaske.
“Amman Anty yau ba zan koma gida ba har sai kin bani labarin alakar wannan Hameeda da Zain”
Anty Ummi tayi murmushi tana kallon Baba Asabe wacce ta shigo cikin dakin hankalinta tashe jikinta har rawa yake.
“Hajiya wasu...wasu na nemanki...”
“Su wa?”
Kamin Baba Asabe ta amsa mata sai ga police wajen hudu sun shigo cikin dakin kowanne fuskarsa babu annuri.
“Ke ce Balkisu Salisu Fayau?”
Anty Ummi ta tsaya kallon wanda ya nuna ta da yatsan cike da tsananin mamaki kamin ta amsa masa.
“Ni ce”
“You're under arrest, ana zarginki da sace yar mutane....!”
Mikewa Anty Ummi tai tsaye cikin wani irin tashi hankali, Farhat kuma ta rufe baki ta zaro ido waje.
HAFSATU MANGA POV.
A kwana biyu da tai a gidan duk tabi ta rame sai kuka take faman musu komai aka bata sai ta ki ci sai taga dama.
Yau ma daker tai wanka saboda kukan da take taki da saba da gidan balle har ta sake duk kuwa da kasancewar akwai yara a gidan. Kayan data zo da su sune a jikinta kullum, yau ma bayan ta yi wanka ta sake saka kayan ta zo falo ta zauna.
“Ba zama zaki yi, tashi ku tafi”
Ta lake kafada alamar ita bata son zuwa.
“Tashi ko na saka a dakeki yanzu nan”