← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 93

Sashe 56

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jikinsa yayi sanyi, sai ya kasa ce mata komai har ta tashi ta fice daga dakin hawaye shabe shabe a fuskarta, tafiya kawai take ba dan tasan abunda take takawa ba, hawaye na rufe mata ido bata ganin komai sa hudu, kamar wacce aka fisgo haka ta zame ta fadi jiri na dibanta. Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un da Zain yaji Dada na fadi ne yasa shi saurin tashi ya nufi falon, sai ya tararda ita kwance Dada na kokarin kamata.
He was helpless sai kawai ya sa kai ya fice daga gidan gaba daya, ya saba zuwa gaishe da Mai Martaba da safe amman yau be tsaya gaishe shi ba ya fice. He was busy thinking of inda zai je, gurin Anty Ummi ko gurin Ibrahim, but seriously he don't know what to do now he needs someone da zai magana da shi. A harabar gidan Anty Ummi yai parking din motarsa bayab yabi shawarar zuciyarsa na son magana da yar'uwarsa fiye da abokinsa.

Fito yai ya shiga cikin falon, Baba Asabe akwai ya tarar tana aikin gyara falon, tana ganinsa da risina ta gaishe shi, ya amsa mata tare da nufar dakin Anty Ummi, sai da yai knocked sannan ya tura ya shiga, tana tsaye gaban madubi tana fasa turare da alama yau da wuri zata fita, juyo yai ta kalleshi fuskarta dauke da murmushi. Sai dai yanayin yadda taga fuskarsa yasa ta zauna bakin gado tana cigaba da kallonsa.

“Zain lafiya dai?”

Hannayensa biyu yasa ya shafa fuskarsa ya cika bakinsa da iska ya busar sannan ya kalli Anty Ummi ya ce

“Ya zaki ji idan na ce miki i raped Hameeda or Hameeda raped me, maybe we raped each other, zai kuma iya yiyuwa ba mu yi din ba”

Anty Ummi ta tsaya kallonsa, at first dariya ta fara yi, sai kuma ta rike baki.

“You're not a drunker, bari na ce ko wani abun kasha, na san kuma ka fada min zaka je kai magana da Hameeda jiya then what happen”

Yayi shiru kamin ya ce

“Maybe tana jiran ranar da zan kebe da ita ne dama, ni dai nasan ta zo na fara tambayarta kawai ta shafa min abu a hanci na buga kanta da table na shige daki, daga nan ban sake sanin inda nakeba, ina farkawa na ganni Naked, and yau da safe Dada na fada min wai wani yayi raping din Hameeda”

Anty Ummi ta daga masa hannu.

“Wait wait, ni fa ban gne kan wannan labarin ba”

A nan ya kwashe abunda ya faru tun barinsa gidan ya fada mata. Anty Ummi ta tsaya tana mamaki.

“Zain, Hameeda deserve you, idan har mace kamar Hameeda mai ji da kanta yar sarauta zata iya yi maka haka, to ta cancanta ka aureta, ina tsoron halin da zata shiga nan gaba, zata iya kashe wani akanka Zain ko kuma ta kashe kanta, kuma na tabbatar ba zaka taba son haka ya faru ba, ba kyau dan'uwanka yana cutuwa da abu kuma ka barshi ya cigaba da cutuwa da shi bayan kuma kana da yadda zaka yi a sama masa mafita”

“Anty ko dai baki gane kan abunda tai ba ne? Shikenan kuma ni sai na cutar da kaina na aureta? Bana son ta ban taba mata son aure ba”

“Wani lokacin so ya shigar mutum ne da inda be yi zato ba, kamar yadda yai ma Hameeda, wani lokacin kuma muna iya koya ma kanmu son, saboda muso yan'uwanmu, wani be iya so ba Zain, ka tausayawa yarinyar nan, kar ta fada hallaka, ji yadda Allah ya jarrabeka da son yarinyar kauye nan batanta duk yasa ka bi ka rude, yanzu idan wani abun ya same ta ya zaka ji?”

“Nono Anty Allah ya tsare ni fa ba son aure nake mata ba, ba son soyayya ba kawai dai ina mata kallon yata ne”

“Zain kai yi tunani, idan akwai yiyuwar hakan, ka daure ka aureta ko da na dan wani lokaci ne in yaso sai ka rabu da ita”

“Ai dana aureta Dada ba zata bari na rabu da ita ba, ni ba wannan ba, yanzu so nake ki fadawa Farhat ta yarda ta bini zan cewa Mai Martaba zamu je Damagaram gurin honeymoon ni da ita, sai na dauko Mama”

“Mama dai Mama dai yanzu kaji inda take hankalinka ya kwanta ko? Sai kuma me? Ai Farhat Matarka ce kai kafi dacewa ka sakata taje ba ni ba”

“Bata jin magana ta Anty”

“Baka mata da dadi ne shiyasa bata jin maganarka”

“Amman ai ni mijin”

“Shikenan dan kana miji sai kawai ka shigo cikin gida kai gaka boss kana mata yadda kake so”

“Haka tace miki?”

“Na san hakinka ne ai idan baka son abu, ita ma kuma na mata fada kuma na san ta gyara sai dai idan kaine baka gyara ba”

“Kin gani ko? You always take her side”

“This is not the right time to take anyone side, kawai ina fadar abunda yake shine kai da ita duk ya kamata ku gyara, zama aure ba haka ake yinsa ba, be kamata ace dayan na danne hakkin wani ba, yarinyar marainiya ce, gashi mahaifiyarta bata son auren nan, dukan abunda ya sameta a yanzu dariya zasu mata, da hakure a haka tana zaune da kai kuma ka zo kana gallaza mata”

“Ita take hakuri zama da ni ko kuma ni nake hakurin zama da ita? Jin wata magana Anty kamar dai ita ce taki ni tsintoni kika kai”

Ta tabe baki ta tashi.

“Yanzu dai hankalinka ya kwanta ka gano inda yarinyar take, sai ka nemi gurin ajeta dan ni ba zaka ja min wani ballin ba, Abban Amal ma nasan ba zai yarda ta zauna a nan ba”

“Ba zam ma zaunar da ita a nan ba, a cikin masarautar mu zan kaita, i feel like naje yau na daukota amman ba dama tun da Farhat bata da lafiya...”

“Miya sameta”

Anty Ummi ta tambaye shi da sauri. Sai ya daga kafadunsa.

“I mean bata cikin far'a kin san yadda take ai, idan naje zan bata ki yi magana da ita”

Ya tashi yana saka hannayensa aljihu. Bata sake ce masa komai ba har ya fice, tana tausayin Zain ta wani bangaren saboda halin daya shiga, zama da Farhat ga kuma Hameeda data taso shi a gaba yanzu, ga kuma Hafsatu manga da yake kokarin saka kansa cikin wata matsalar saboda ita. Bata tunanin kai Hafsatu manga a masarautar abu ne mai sauki a gareshi, sai dai tana ganin hakan shi yafi dacewa duk kuwa da kasancewar bata san abunda gaba zata haifar ba.

Daga gidan Anty Ummi asibiti ya wuce, a can ya wuni, a can ne yake fadawa Ibrahim yadda suka yi da Hameeda yayi dariya sosai yana jinjina shu'umancin Hameeda
Sai da yamma ya koma gida bayan ya biya a ten o seven ya tsaya yai musu takeaway, a falo ya samu Farhat tsaye, tana sanye da doguwar riga hannunta rike da cup. Tana ganinshi ta aje cup din ta nufi stairs.

Da kallo ya bita har ta haye sannan ya aje ledodin a dinning ya hau sama ya watsa ruwa ya canja tufafi ya sake saukowa kasa, ya dauki takeaway ya nufi dakinta. Tana ganinsa ta juyar da fuskarta ta mikar da kafafunta ta kwanta, kasa ya aje ledodin ya zauna bakin gadon yana kallonta. Be san me zai ce mata ba, tashi ki ci abinci ko kuma ya jikinki yake? Hawayen daya fito ta gefen idonta ne yasa shi jin tausayinta for the first time, ya san be kyauta mata ba, ba kamata ya zo mata a cikin yanayin daya zo mata, but yayi farincikin daya sameta a mace, zargin da yake mata ya tafi, yanzun kan yasan ba duka mai shigar banza ce yar iska ba, wasu suna yi a tunaninsu wayene bayan kuma suna zubarwa da kansu mutunci ne kawai. Hannu ya kai ya shaye mata hawayenta sai ta buge masa hannun ta tashi zaune.

“Ka daina taba ni bama”

“Ga abinci ki ci? Fada min me kike ji yanzu?”

“Ina ruwanka ba zan ci ba”

Hannayensa biyu yasa ya rikota da dukan karfinsa sai gata ta dawo saman jikinsa, sai ya matse kanta a kirjinsa, dayan hannunta kuma ciki hannunsa yana murzawa.

“Why are you so stubborn? Na san na yi kuskure amman ai sai kiyi hakuri komai ya wuce”

“Kai a gareka ya wuce ni gurina be wuce ba, kuma ba zan taba mantawa da wannan ranar ba”

Ya fada cikin kuka tana kokarin janye kanta daga jikinsa. A maimakon ya saketa sai ya juyo da ita ya zama bayanta ne ke gugar kirjinsa a yanzu, sai ya kai bakinsa saitin kunnenta ya rada mata.

“Ban ce ai ki manta da wannan ranar ba, you know it's special, nima ba zan manta da ita”

“Special day da miji yai raping din matarsa ba”

“Bakinki ba zai daina fadar irin maganganun nan ba ko?”

Yatsanshi ya saka cikin bakinta ya rika watsa da halshenta yana soka mata shi har can kasan halshenta. Cizo ta gatsa masa ba shiri ya saketa ya zare hannun yana yarfarwa. Ita kuma ta sauka saman gadon ta zimmar bar masa dakin, sai yai saurin fisgota ta fado kansa ya rumgumeta da dukan karfinsa, tana jin yadda zuciyarsa take mugun bugawa as well as yake jin yadda nata zuciyar ke bugawa. Dayan hannunsa ya kai ya ciro wayarsa daga aljihu ya kira Anty Ummi sai ya saka hands-free.

“Anty Ummi zata yi magana da ke”

Sakinta yai ya mika mata wayar, sai ta ki karba har Anty Ummi tai picking.

“Anty fadi tana jinki”

“Farhat”

“Na'am”

Ta amsa tana share hawaye.

“Kina lafiya”

Sai da ta kalli Zain sannan ta amsa.

“Lafiya ta kalau”

“Kin tabbata? Idan akwai wani abun ki fada min”

“Ba komai, amman Anty kin san nace miki ina son waya”

“Ban mata ba, Zain zai baki kamin ku tafi”

“Ina zamuje?”

“Raka shi zaki yi Damagaram ya dauko wata yarinya, na san ai ba zaki ki ba”

Tayi shiru na wani lokaci, ba damar tace ba zata ba tunda Anty Ummi ce, sai dai kuma bata jin zuwan tunda hidimarsa ce ba tata ba.

“Yaushe?”

“Shi zai fada miki lokacin, kin yarda?”
Chapter 56 · 0% Book details