← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 93

Sashe 16

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga Bashir har Farhat da wata gwaggonta da yan uwan Bashir da Samira da wasu abokan aikinta suna tsaye suna jiran fitowar likita. Yanayin yadda likitocin suka fito kadai ya isa ya karantar da su cewar Rukaiya ta rasu. Baya baya Ya Bashir yai har ya fadi kasa zaune sai ya cire hular kansa ya fashe da kuka kamar mace, a take kowa ya saka kuka a gurin ban da Farhat da take jin da ganin komai a mafarki, takawa tai ta karasa kofar dakin ta tura kofar tana kallon yadda aka lullube Anty Rukaiya, lallai mai rai ba komai ba ne, ta kasa yarda Anty Rukaiya ta rasu, gani take kamar zata tashi zata koma gida suka cigaba da rayuwa kamar da, tasan mutuwa bata da notice balle warning tana zuwa a da zarar lokaci yayi amman yanzu zuciyarta na raya mata dogon suma Anty Rukaiya tai bata mutu ba iyakar abunda ta sani alkawarin Allah baya tashi. Ji tai am dafata an kai hannu an rufe kofar dakin sai ta juyo ta kalli gwaggonsu wato Gwaggo Binta dake hawaye.
Hakan ya kara tabbatar mata da Anty Rukaiya ta tafi kenan har abada, murmishi tai amaimakon kuka sai ta nuna kanta amman ta kasa magana, faduwa tai zaune tana son kuka amman ba hawaye.....

ZAIN POV.

Da yamma lis Zain ya shiga dakin da a kai Hafsat bayan anyi mata aikin a kunne kuma an sake mata bandeji gurin data jimu jiya, a sanyaye ya shiga dakin yana hango yadda take kwance zuciyarsa ta soma sosu, tsaye yai yana kallonta wani mugun tausayi ta bashi an saka wani karfe an bude bakinta sama da kasa, ga wani dinki da aka mata a halshe gwanin tausayi, zaunawa yai saman gadon idonsa da hankalinsa duka yana kanta, irin kallon da yake ma Haleema yake mata, duk abubuwan da suka faru lokacin daya fito da ita daga tiyata ne suka soma dawo masa daya bayan daya. Hannu ya kai ya shafa gefen fuskarta sai yaji tayi sanyi da yawa kamar wacce ke cikin kankara, wani tunanin ne ya zo masa sai yai saurin maido dubansa gurin bakinta yana kallon halshenta....

Manage 🙏🙏🙏

*HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_

Wattpad @KhadeejaCandy

1⃣4⃣

Ba ta gasgata gaskiyar mutuwar Anty Rukaiya ba har, sai da ta ga an fito da gawarta, hannu Farhat ta dora saman kai ta kurma wani uban uhu wanda ya tashi hankali duk wanda ke gurin.

“Na shiga uku, na bani na lala ce Anty Rukaiya ta tafi ta barni La'ilaha illah Innalillahi Wa'inna ilaihirraji'un...”

Gwaggonsu ce ta rikata tana kuka tana bata hakuri. Daker aka fito da ita daga asibiti saboda kukan da take, kamar sabuwar mahaukaciya haka aka isa da ita gida.
   Suna fitowa mota sai yaranta suka fito daga cikin gidan da gudu sanye da uniform da alama basu dade da dawowa daga makaranta ba. Hankalinsu ya tashi duk kuwa da kasancewarsu kanana, ganin Farhat na kuka da Abbansu da kuma duk wanda yake tare da su.

“Anty Farhat miyasa kike kuka?”

Aliyu ya tambaya kasancewar shine babba ya fisu wayo, tausayin ne yaranne ya shiga zuciyar kowa, musamman ma Farhat data rasa abunda zata ce musu, taya zata fada musu mahaifiyarsu ta mutu macen data fita dazu lafiya kalau? Ya Bashir ne ya share hawayensa ya kama hannayensu ya nufi cikin gidan da su.

“Abbah miyasa kake kuka? Ina Momi? Miyasa naga motar asibitin a nan gidan?”

A take Aliyu ya jero masa tambayoyin amman ya kasa amsa masa ko daya hawaye sai sauka suke a idonsa. Dakinsu ya shiga da su ya janyo kofar ya rufe, sai kuma ya jingina jikin kofar ya fashe da kuka mai karfi kukan da be san ta ina yake fito masa ba.

Ba a bari Farhat ta sake ganin gawar Anty Rukaiya har aka mata wanka aka mata sutura, daya daya aka hadeta da su Aliyu har lokacin kuka take kukan tausayin yayanta da kuma ita kanta. Su kansu yayan kuka suke domin a lokacin sun fahimci sun yi rashin mahaifiya ta tafi kenan har abada.
  Mutuwa Anty Rukaiya ta taba, makota da yan'uwa da ma abokan aikin kowa sai al'ajab yake, daga wanda zai ce ya ganta jiya sai wanda zai ce satin daya wuce suna tare, gashi bata kwanta ciwo ba, mutuwarta kawai aka ji , mutane Anka ma da suka zo kowa kuka yake da kuma fadar alherinta.

  A yadda Anty Ummi take kuka da alhinin mutuwarta sai ka dauka wata yar'uwarta ce ta jini, kuka take sosai saboda tana ganin komai daya faru laifinta ne, saboda Farhat ta labarta mata komai abunda ya faru, tayi dana sanin yin zancen da Anty Rukaiy da ace bata yi mata magana akan abun ba da duk haka be faru ba.
   Anty Rukaiya ta samu mutane sosai ta kuma samu addu'ar da kyakkyawan yabo wanda ake son ko wane mamace ya samu, abokai da makota dukansu sun yi mata shaidar kwarai, dukansu babu wanda be zubar mata da kwalla ba.

***         ***        ***
Misalin Bakwai da Rabi na yamma ta bude idonta, dizzy take ganin silin, hakan yas ta dade tana kallon sama kamin ta bi dakin da kallo sai wani lumshe ido take tana budewa. 

“Mama... ”

Ta juyo ta kalleshi da idanuwanta da suka yi rawaya, kokarin rufe baki take amman sai ta kasa sakamakon karfen da aka saka tsakanin lebenta na sama dana kasa, wani zafi taji halshenta nayi kamar an saka mata wuta. Duk iya kokarinta na yin kuka ne, amman sai ta kasa, hawaye kawai suke sauko mata babu kakkautawa. Tasowa yai daga inda yake zaune yazo gurin kanta ya tsaya yana kallon yadda hawaye ke sauko mata. Tausayinta ne ya rufe shi, as her age tana cikin mayuwacin hali ga kuma abunda ya sameta a yanzu, secondly ya tsani kuka  ko da haka kawai ne balle mai dalili irin wannan, musamman na mace domin yana ganin wanda aka cuta ko aka zalumta ne kawai yake kuka ko kuma wanda be shi da yadda zai yi. Risinawa yai bakin gadon yana saukar hawayenta har cikin ranshi.

“Idan kina kuka ba zai yi saurin warkewa ba...”

Yayi shiru yana cigaba da kallonta kamar yadda take kallonsa.

“Kina son bakinki ya warke da wuri”

“Na siya miki abun dadi?”

Haka yake ta raba maganar yana tsayawa kamar mai jin wahalar maganar, alhalin babu gajiya ko wahala a tare dashi face kasaita da kuma sabo da yin maganar a haka. Tunda yake maganar kallonshi kawai take amman bata daga masa kai ba, bata daina hawayen ba. A hankali ya sauke ajiyar zuciya ya busar da iskar bakinsa, kana ya kai hannunsa share mata hawayen.

“Mamana daina kuka kinji? Zan siya miki nama da minti kina so?”

Taji zancen abunda tafi so fiye da komai a duniya wato nama hakan yasa tai saurin daga masa kai.

“To ki daina kukan...”

Ya fada fuskarsa babu walwala.

“Nan da kwana biyu zaki warke sai na siya miki kinji?”

Ta gyada masa kai tana ta kokarin tsayarda hawayen, sai kuma ta nuna masa cikinta, shi kuma ya sakar mata ido yana kokarin gano abunda take nufi, bata isa jin yunwa yanzu ba, domin a drip din saka daura mata akwai abubuwan da aka saka a cikin wanda zai hanata jin yunwa da wuri, so ifa ba yunwa bace that's means fitsari ne kenan.

“Fitsari?”

Ta daga kai, sai ya kai hannu ya zai cire mata drip din tai saurin yaje hannun ta tashi tsaye tana lakame kafada, hannu ya sake mikawa zai kama hannunta sai ta sake gwacewa.

“Robar zan cire miki kiyi fitsarin”

Ta lake kafada tana hawaye. Ido ya sakar mata dan be san yadda zai yi da ita ba, zuwa can ya fiddo wayarsa ya shiga sashen message ya nemo number Doc Hafsat wato kwarirriyar likitar halshe, likitar data dinkewa Hafsat halshenta, ya aika mata da saka, sannan ya maida wayar aljihu ya cigaba da kallon Hafsatu data bata fuska tana kallonshi idonta cike da tsoro, gira daya ya daga mata sai ta kara lake kafadar ta juya masa baya.
   Guntun murmushi ne ya bayyana a fuskarsa, kallonta kawai yake yadda take kiriniyar sauka saman gadon burgeshi yake, ita ala dole da karfin karin ruwan zata shiga bandaki tai fitsari, a ganinta idan aka cire zafi zata ji wata kila ma za a cire tare da fatarta ne gaba daya, yadda aka saka mata shi be dame ta ba cirewan ne yafi tsaya mata a rai, daman ko da aka saka mata shi bata cikin hayyacinta da ba zata bari a saka mata shi ba.
Shi dai kallonta kawai yake har ta sauka saman gadon ta soma jan karfen ta nufi inda take zaton bandaki ne, lokacin data isa gaban kofar sai ta kao hannu ta murda amman ta kasa budewa juyowa tai ta kalleshi sai ya daga mata gira daya kamar dai dazu amman wannan karon ta gyada masa kai sai ya karasa gurin kofar ya dora hannunsa saman nata ya murda kofar ta bude. Sai kuma tai tsaye tana kallon toilet din komai dake ciki irin na gidan Anty Ummi ne ita kuma bata saba da irin wannan ba, abunda take masa kallon kula ko randa ita bata ga gurin fitsari a nan ba, hakan yasa ta bata fuska ta kalleshi.

Shi kuma ya daga mata kafada, suna haka Doc Hafsat ta turo kofar ta shigo fuskarta shimfide da murmushi kamar kullum, har ta karaso inda suke tsaye Zain be tada kai ya kalleta ba kamar ma be san da shigowarta dakin ba, hakan be dame ta domin ta saba da dabi'unsa duk kuwa da irin kyakkywar fahimtar dake tsakaninsu.

“Afternoon Doc”

“Yarinyar nan ta farka fitsari take ji...”

Bayan ya numfasa ya cigaba.

“Kuma ba zata bari a cire mata drip ba”

Murmushi Doc Hafsat tai ta karasa kusa da Hafsatu ta dafa kafadunta.

“Wata kila ka mata wanin abun ne shiyasa taki yarda da kai, amman ni ai kawarta ce ko?”

Hafsatu manga ta girgiza kai alamar a a, a ranta tana fadar.

‘Katuwa dake za ki ce kawata ce ke’

A fili kam babu bakin magana sai ido da lake kafada.

“Yanzu dai fada min sunanta”

“Sunanku daya”
Chapter 16 · 0% Book details