← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 93

Sashe 43

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta gyada kai hawaye nata sauka a idonta, duk yadda tai kokarin danna kukanta sai ta kasa har sai da ta fasashi, daukarta yai sama ya dorata saman kafadarsa yana jijjigata.

“Shiiiiiiiiiiii”

Saman karamin dinning da ke gurin ya zauna yana rumgume da ita, yana sauraren yadda zuciyarsa take mugun bugawa.
[3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *HAFSATU MANGA*

32

Suna zuwa state cid sa ita saka sakata cell cikin wasu karuwan mata dake gurin.
  Bata wuce awa daya a gurin ba, wani police ta zo ya fito da ita ya shiga da ita wani daki da babu kowa a ciki sai kujeru da tebura, gurin zama police din ya nuna mata, tana zaunawa sai ga wasu yan sanda biyu sun shigo dayan na rike da abun rubutu.

Kujerar dake facing din nata ya zauna yana kallonta fuskarsa ba yabo ba fallasa.

“Madam zamu dauki statement dinki, dukan abunda zaki fada zamu amfani da shi a gaban kotu”

Anty Ummi bata ce komai ba, mutumen dake rike da littafin ya bude ya dora alkalaminsa saman littafin yana jiran ta fara magana ya fara rubutawa.

“Section...... Under.... A karkashin dokar Nigeria ana zarginki da satar yarinyar mutane”

“Ni ban sace yar kowa ba, taimakonta kawai nai, ita da kanta ta kawo kanka kofar gidana tana neman taimakona, I just help her bayan shi babu wani abu”

“Amman mutum zai shigo gidanka haka nan kawai ka taimaka masa ba tare da kasan miye yake tafe da wannan mutumen ba? Ki fada mana gaskiya ko kuma nasa a wulakanta ki a gurin nan”

“Babu dokar da tace a dake ni ko a wulakanta ni, zargina kuke yi dukan abunda zaku min nima zan nemi hakki a wani gurin”

“Oh wato har kina da bakin magana ko? Sajan”

Wanda aka kira da sajan din ya amsa da sauri

“Sir”

Kamin ya bashi umarnin da zai bashi sai ga Dcp Faruk ya shigo, da sauri suka tashi tsaye suka tsare masa.

“A fito da matar nan ka kawo ta Office dina”

“Yes Sir”

Yana juyawa suka saka Anty Ummi a gaba zuwa office dinsa, fita suka yi suka barta daga ita sai Dcp sai kuma mijinta Alhaji Masa'ud.

“Hajiya ayi hakuri da abunda ya faru, amman abunda ake zarginki da shi case ne mai girma, wanda dole ne mu yi bincike, wadanda suka shigar da karar suna zarginki da sace musu ya, kuma ina tunanin a matsayinki na mai aiki da kare hakkin dan adam ko da ba ke ake zargi ba, zaki iya tsaya musu wajen ganin komai ya tafi daidai”

“Yanzu dai ba wannan ba, ni dai abunda nake so a bani belin matata in yaso duk abunda zai biyo baya sai ya biyo”

“Gaskiya ba zai yiyu a bada belinta ba, a halin yanzu haka babu wani bincike da muka yi, yanzu ma saboda Alhaji Salisu Fayau ne yasa na fito maka da ita”

“Amman kun bincika kun gane iyayen yarinyar ne? Domin yarinyar yar gudun hijirace an kashe iyayenta, wannan dalilin ne yasa na taimake ta”

“Baki da wata hujja ta rike yarinya karama a hannunki kuma kice taimakonta kike son yi, miyasa lokacin da kika riketa baki zo hukumar yan sanda kin sanarba saboda gudun irin wannan? Yanzu ni abunda nake so ki fada min ina yarinyar take?”

“Na bada yarinyar a kaita kauyensu, wa kika ba ya kaita? Tare da wa kuka je?”

“Ban san mutumen ba, wata kawata ta hadani da shi, yace min shi dan kauyen Kufawa ne kuma ya san gidansu yarinyar, shiyasa na hadusu ya kaita”

“Kin tabbata? Zamu bincika ina fatar dai gaskiya kike fada mana, domin wannan ba magana ceda hankali zai dauka ba, gurin wa kika ce a kai yarinyar?”

“Gurin Sarkin gari”

Telephone Dcp ya dauka ya danna kira.

“Zo yanzu nan”

Ko minti biyu be yi da aje wayar ba, sai ga wani police ya shigo tare da sare masa.

“A saka kofur Illiyas yaje Kauye kufawa ya bincika mana idan an kawo yarinyar mai suna Hafsatu manga, kai kuma ka shigo mana da iyayenta yanzu”

“Yes Sir”

Yana fita sai ga wasu tsofin fulani mace da namiji sun shigo dakin macen jikinta sai rawa yake namijin ne kawai yake da juriya, shi ya zauna saman a Cushion dake can gefe, ita kuma mace ta zauna kasa jikinta na rawa kamar mazari.

“Kune iyayen yarinyar nan Hafsatu manga”

“Mune Ranka ya dade”

“Ina hoton yarinyar yake?”

Namijin ya mika masa hotun dake hannunsa. Anty Ummi ta mika hannu ta karbi hoton tana dubawa, Hafsatu manga ce zaune saman manyan kujera na alfarma, ba zata iya gane ina ne amman tana gani tasan ba a kauye ba, wani abun mamaki kuma tufafin dake jikinta tufafi ne masu tsada a jikinta. Phone din dake hannun Dsp din ce tai ringing sai yai picking yana murmushi.

“Ranka ya dade babban likita”

“Kana office?”

“Ina nan, kujerar ce tamu ta Hajji ta fito”

“Kai baka rabo da abun dariya, yayata ka kama ba dole na zo ba”

Yana fadar hakan ya kashe wayar, sai gashi yayi knocked ya turo kofar office din ya shigo.

“Bari mu tashi mu gaida saraku”

Zain yayi murmushi yana mika masa hannu su gaisa.

“Dcp ka yi babbab kamu, ka kama min uwa gaba daya”

“Au haba, to ai kaga na ci ribar kamun ko mai komai ka kawo kanka da kanta har office dina”

Zain ya yi dariya sannan ya zauna tare da kai hannu ya karbi hoton dake hannun Anty Ummi.

“Wannan ai Mama ce”

Sai kuma ya juya ya kalli mutanen dake bayansa.

“Kune iyayenta?”

“Ee ni mahaifinta ne ga mahaifiyarta nan”

Namijin ya amsa.

“Ina kuka samu wannan hoton?”

“Wanda aka dauketa ne lokacin da muka je gidan wani baffan mu”

“No wannan kayan ni na siya mata su, ta saka su ranar dana kaita gidansu Doc Hafsat, sannan kuma Hafsat ta fada min da bakinta cewar bata san inda mahaifinta yake ba, mahaifiyarta kuma mahaukaciya ce ita kuma wannan naga hankalinta na jikinta”

Antar cikinsu ce ta kada, a take marar matar ta cika da fitsari. Dcp din yai saurin tarewa

“Wannan ba hujja ba ce Zain, kuma wannan bincike mu zamu yi shi, yanzu dai abunda na ke ta so fada mana inda yarinyar take”

“Bata san inda yarinya take ba, ni na dauka yarinyar daga wajen gidanta na kawo ta cikin gidan, kuma ni na hana a kaita gurin police saboda yarinyar tana tsoron police, yanzu haka kuma yarinyar ta gudu ba mu san inda take ba, so idan ma kamawa ne ni ya kamata ku kama ba ita ba”

“No look Zain, ita muke zargi dan haka ita zamu kama”

“Wannan wulakanci ne aka saka ku mata Dcp na sani, fada min inda iyeyen yarinyar nan suka fito zan saka Mai Martaba ya bincika garin”

“Ba huruminka ba ne wannan, yanzu dai yarinyar muke nema”

“Baku da hurumin aje Anty ta a nan dan ku wulankatata, ni zaku kama ba ita ba”

Dcp yayi dariya.

“Haba dai abokina ai kafi karfin a kama ka, ita ma din zan maka alfamar baka belinta amman case din yana nan dole a nemo inda yarinyar take”

Zain ya juyo ya kalli mutane sai duk suka sadda kansu kasa macen na ta faman kuka. Babu ta inda suka yi kama da Hafsatu manga, duk wannan abun yasa plan ne , there's something behind it.

“Zan a nemo yarinyar insha-Allah, amman duk aka gano yarinyar ta tabbatar da wadannan ba iyayenta ba ne, ni kuma sai na rufe su”

“Wannan aikinmu ne ba naka ba”

Cewar Dcp. Sai bayan magariba suka baron gurin tare da Anty Ummi, bayan an dauki statement dinta, sannan suka bada belinta. Daga cid office Zain ya wuce asibiti gurin Ibrahim, a tare suka yi sallah magariba, bayan sun fito daga masallaci Zain yake labarta masa abunda ya faru.

“Duk yadda aka yi Doc Hafsat tasan komai akan case din nan, domin hoton da naga a hannunsu kayan da na saka mata ne lokacin da na kaita gidan”

“Amman bana tunanin zata yi wani abun dan kama Anty Ummi, idan ma har haka ne nafi zargin yayanta, domin shi Dsp ne kamin a masa transfer, ta taba labarta min cewar ya nuna damuwarsa akan yarinyar”

“Look yanzu muje gidansu yarinyar nan, ina son ganinta”

“Ba sai muje ba, ta shigo asibiti dazun nan muka tabu da ita”

A tare suka jera har sashen da Doc Hafsat take, a office ba ita kadai ba ce hakan yasa Ibrahim ya kira a waya, tana fitowa ta ganshi tare da Zain sai gabanta ya fadi.

“Lafiya”

Ta tambaya tana kallon Ibrahim. Zain be ce da ita komai ba ya wuce hanyar office dinsa, ita kuma ta jera tare da Ibrahim suka rufa masa baya.

“Ibrahim mi nayi?”

“Baki yi komai ba”

“Ni ba zan iya da wannan abokin naka ba”

“Tambayarki kawai zai yi”

A tare suka shiga office din, a lokacin Zain na zaune saman kujerarsa mai juyawa. Zaunawa tai kamar yadda ta ga Ibrahim ya zauna.

“Kin dauki Mama hoto lokacin da take gidanku ko baki dauke ta ba?”

“Na dauke ta, amman ban mata komai ba”

“Ke kika fadawa yan sanda cewar ta zauna gidansu Anty Ummi?”

“Aa Wallahi ba ni ba ce, miya faru”

“Komai be faru ba, amman nan gaba kadan wani abun zai faru, kuma idan har na bincika da hannu ciki sai na miki mugun wulakanci”

Ta kalli Ibrahim idonta raurau.

“Mi na masa”

“Baki masa komai ba, amman yarinyar ta bata kuma yanzu yan sanda sun kama Antynsa da sunan ita ta sace yarinyar, wasu tsufo sun zo sun nuna sune iyayenta hoton da suka nuna kayan dake jikinta tufafin da Zain ya saka nata ne lokacin da xa a kaita gidanku, kuma saman kujerun ne”

“Na shiga uku wallahi ban mata komai ba, kuma ban san yadda aka yi hoton ya fita ba”

“Yanzu ke Hafsat baki san inda take ba, ko jin labarinta ba ko wani abun daya shafe ta”
Chapter 43 · 0% Book details