Sashe 75
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ya mai shari'a idan muka hada maganar Abida ta farko cewar Hameeda ta fada mata Farhat na kiranta, da kuma zancen Zain da ya fadi cewar babu jituwa a tsakaninsu, hakan na nuna ba Hafsatu manga kadai ya kamata mu zarga ba, da wannan na ke rokon wannan kotu mai alfarma da ta taimaka ta bada belin yarinyar nan kuma ta dage wannan zaman na dan lokaci domin ba mu damar bincike, sannan kuma ina rokon kotu data bawa aikawa Hameeda da takardar gayyata domin ta amsa mana wasu tambayoyin a zama na gaba, na gode”
Alkali ya dade yana rubutu sannan ya dago ya ce
“Kotu zata dage wannan zaman har zuwa ashirin da uku da watan shida, kotu ta bada umarnin a cigaba da tsare Hafsat a gidan kaso, sannan kotu tana umartar magatakarda da ya aikawa Hameeda da takardar gayyata”
Ya buga abunda ke gabansa sannan duk suka tashi, suka fito waje tare da Hafsatu manga wacce yan gandireba ke tare da ita tana ta shekar kuka. Mahaifinta ma Hawaye yana jin kamar ya figota ta karfe ya dawo da ita, Zain kam tuni ya bar gaban kotu ya koma cikin motarsa ya zauna yana jiran abokinsa Ibrahim, Anty Ummi da Barrister Hassana tare suka fito ko wannensu rai babu dadi domin sun so a bada belin Hafsat amman hakan be samu ba, Husaina kam taa can ciki daman tana da wat shari'ar bayan wannan.
[3/29, 10:17 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 52.
Dada ta rike takardar sammacin neman zuwa Hameeda kotu tana girgiza kai.
“Ina mamakin wannan kiyayyar ta Zain, wato yana kam bakansa cewar ita ta kashe masa mata ko? Lallai Zain ka bani mamaki”
Hawaye kawai Hameeda ta kasa cewa komai. Sapna wacce ita ce wacce Mai Martaba ya aiko ta kawo ma Hameeda takardar, ta kalli Hameeda cike da tausayawa ta ce.
“Ba fa wani abun ne, kawai dai an fadi cewar auna samun rashin jituwa ne tsakaninta da Farhat shine Barrister ta nemi kotu ta gayyatota ta amsa mata wasu tambayoyin, amman ba wai wani abun ba ne”
Ta dago kanta ta kalli Dada tana share hawayen da suka ki su tsaya mata.
“Zan je kotu, zan bada shaidar abunda na sani, kowa zai huta”
Dada ta dafata cike da tausayawa.
“Ki kwantar da hankalinki Hameeda, duk mai son ganinki a rana shi zai shiga cikin ranar nan da yardar Allah”
“Hankalina zai kwanta, kaddarata ta canja wata kila a zamanin labarin harihim rayuwata ya shude, amman bana hangowa kaina kwanciyar hankali a gobe, jibi, sati mai zuwa ko kuma wani zamanin”
Ta fada zuciyarta na ta raya mata wani abun da take jin ita din zata iya. Ta mike tsaye cikin rashin kuzari ta fice daga falon Dada ba tare da hawayen sun daina mata zuba ba.
“Da nasan haka zamankewarku zata koma, da ban rika daya daga cikinku ba, da duk ban ga wannan bakincikin ba”
Dada ta fada tana hawaye. Abunda yasa Sapna jin babu dadi, cox yana cikin abunda ta tsana ganin hawayen babba, saukowa tai daga inda take zaune ta zo gaban Dada ta zauna kasa ta kama hannayenta ta rike.
“Dada dukan abunda ya ke faruwa Allah ya riga ya tsara haka zai faru, kuma shi yasan yadda zai daidaita al'amurransa,dan haka ki barwa Allah komai ki yi addu'a baki san abunda Allah yake nufi da wannan ba”
“Haka ne, amman Sapna ni kadai na san abunda na ke ji akan abubuwan nan da suka faru”
“Nima bana jindadi ba, Dada kusan ko wace jarida ta kasar nan sai da ta buga labarin abunda nan da yadda aka gudanar da shari'ar, mutane da yawa sun saka ido akan wannan shari'ar ba abun jindadi ba ne, ace irin wannan case din ya taso a gidan sarauta balle ma irin wannan masarautar mai kima da daraja, tsakanin shekaranjiya da a kai shari'ar nan da jiya na karbi kira yafi a kirga mutane sai neman jin abun suke, even on instagram ban huta ba kowa sai tambaya yake, ba ni kadai ba nasan duk wanda ke da alaka da masarautar nan sai ya sha irin wadannan tambayoyin”
“Ai Mai Martaba be damu da zubewar kimar masarautar nan ba, a lokacin da nai masa maganar kar ya bari akai magabar nan kotu sai yaki daukar shawarata, ya goyawa dansa baya bayan kuma ya san abunda yake ba daidai bane, ai duk har da laifinsa gurin fadan nan da suka yi”
“Karki ga laifin Mai Martaba Dada, maganar ce ta riga ta fita, idan ma be yarda anje kotun ba, ba za iya fayyace mai gaskiya tsakaninsu ba, idan har ya hana zuwa kotun Zain zai iya ganin laifinsa kuma ya ga an tauye masa hakki, amman zuwa kotun yana da amfani za a fayyace mai gaskiya a tsakaninsu, a yadda na ji wai an gano mahaifin Hafsat din kin ga shi ma ai ba zai kyale ba, zai ga kamar zaluntarta ne za'ayi amman idan kotu ce ta fayyace gaskiya kuma ta hanke hukunci dole kowa zai yarda”
“Haka ne, Allah ya yanke mana wannan jarrabar hakan, ya kawo mana mafita da duk abunda zai fi zama alheri a rayuwarmu gaba daya”
“Amin Dada shine kawai addu'ar daya kamata ki yi”
Cikin hikima Sapna ta jata da wata hirar ta daban gudun kar ta saka abun a ranta.
*** *** ***
“Har yanzu baka ci abincin ba”
“Anty na fada miki ba zan iya cin abinci mai nauyi ba”
“Daurewa za kayi ka ci, Zain idan kana cewa ba zaka ci abincin ba zaka jawa kanka wata matsalar ne”
Babu yadda zai yi da Anty Ummi ya san indai be ci ba, zata tai ta sha masa kai ne har sai ya ci. Dan haka ya dauka ya fara ci kadan yana wani tunanin.
“Anty ina ganin kamar Mai Martaba zai ga cewar ban kyauta nasa ba ko? Labarin nan ya zaga ko'ina a garin nan, jaridu ni kaina tambayata ake ta yi balle kuma shi”
“Babu wani rashin kyautawa a ciki, abunda kotu zata yanke shine daidai kuma na san inshallah zamu yi nasara, shi kanshi hakan zai fi kara masa girma da Martaba aga cewar a gidansa abun ya faru amman hakan be hanashi barin hukuma tai aikinta ba”
“Haka ne, ina fatar zamu yi nasara”
Ya fada sannan ya dauki ruwa ya sha.
“Inshallah zamu yi, kawai ka cigaba da addu'a komai zai zo da sauki, amman kasan bana hangen nasararmu a yanzu, domin Hameeda shu'uma ce, zata yi kokarin duk yadda zata yi ta fidda kanta, gashi kuma wannan Barrister Husaina din tana son ganin bayan Hafsat”
“Tana bani mamaki sosai taya zaka yi kokarin saka yar'uwarka cikin ukuba”
“Ta dauki gefen mahaifiyarta ne, kuma daman kasan barewa bata gudu danta yai rarrafe, Allah dai ya kyauta”
“Amin”
Haka kawai ya fada ya mike tsaye.
*** *** ***
A duk lokacin da ya kwanta da sunan bachi sai bachin yai masa kwara daga idonsa, haka zai raya dare tana ta tunani kala kala, at first yana tunanin halin da Safiya take a yanzu, duk da kasancewarta ita ta saka kanta, amman abubuwan da ake bashi labarin tana yi suna bashi mamaki, a yadda ta fada sai idan Rufaida ta dawo sannan haukan zai koma kanta amman tana wasu dabi'u da halaye da ke nuna cewar kamar ba a hayyacinta take ba, idonta ya fada kuma yayi baki sosai kamar ana shafa mata kwalli har saman idon, ga wata uwar rama datai hallittarta na kokarin sauyawa zuwa wata kalar ta daban, duk bayan kwana biyu sai Hassana da Husaina sun zo dubanta, sai dai kowa tafiyarsa daban yake, domin Husaina ta dauki gaba da yar'uwarta, hankalinsu ya tashi sosai kullum Hassana cikin rokon mahaifinta take akan yaje ya dubata amman ya kasa zuwa ganinta saboda yana ganin kamar kallonta zai kara masa bakinciki ne kawai. Ta dayan bangaren kuma yana tunanin rayuwar Hafsatu manga, nasara da rashin nasarar duk suna ransa, sai yauahe zata fito zuwa yaushe zai kasancewa guri daya da yarsa yana ganin kamar lokaci ne mai tsawo ko ma ba zai zo ba gaba daya, ko da gaske Hafsat ita ce ta kashe Farhat zai yi duk abunda zai yi wajen ganin ya fito da ita, balle ma babu gaskiya a ciki, bashi da tabbacin komai a yanzu sai na fitowarta ta kowane hali, yana jin zai iya kashe dukiyarsa wajen kautar mata yancinta ko da hakan na nufin ya rasa komai na sa ne, a wani babin kuma yana jin babu dadin akan rashin jituwar da yayansa suke samu wato Barrister Hassana da Husaina, dukansu suna sukar junansu ne da abunda yafi wuka da bindiga, ko wance na kokarin ganin ta kifar da yar'uwarta ne, kuma akan mutum daya suke wannan abun, wato yarsa Hafsat, da wanne zai ji, ga Rufaida ta tsaya masa a rai addu'a ba dare ba rana nemanta kan har yanzu be daina ba, kamar yadda yan'uwanta ma basu taba nuna karaya ba.
Haka kai spending one month kowa da abinda yake ta nuna a ransa, da kuma abunda yake hangowa a matsayin nasara da rashinta, da bangaren Hasana da Husaina ko wannensu ya damu da halin da mahaifiyarsu take ciki, wani lokacin Husaina har Tsoro take ji, ganin cewar sai Rufaida ta dawo abun zai koma kan mahaufiyarta amman tun yanzu tana abu kamar ya dawo kanta, ko dai hakan na nuna cewar Rufaida ta mutune abun ke dawo mata ko kuma tana can tana warkewa a duk inda take shiyasa mahaifiyarsu ke kara shiga cikin tashin hankali. Daga asibitin aka canja mata zuwa wata asibitin ta daban saboda halin da take ciki ba sauki abu sai karuwa yake.
*23-06*
Kotun ta yi tsit kamar babu wani abu mai rai ciki, kowa ya maida hankalinsa gurin alkali wanda ke ta rubuce rubuce, kamin ya dago ya kalli Hafsatu manga, sai kuma ya kallin sauran mutane ta saman farin gilashin da ke idonsa.
“Idan lauyoyin sun shirya za su iya farawa”
Barrister Husaina ce ta mike tsaye, hannunta rike da takardu ta kalli Alkalin ta ce.