Sashe 19
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ee da har zan kira ka sai kuma nai tunanin ko akwai abunda ya tsayarda kai a gidan ne”
“A asibiti na kwana”
Kallon Mamaki tai masa.
“Jinyar yarinyar nan da kanka kake Zain? Anya...”
Kamar wacce ta tuna da wani abu sai kawai ta fasa maganar ta tashi tsaye tana fadin.
“Bari dai na kawo maka abinci ka karya, magana nake son mu yi da kai”
Shi dai da ido ya bita, zuciyarsa nata ayyana masa abubuwa mabanbanta.
Share
Comments
[2/19, 9:48 PM] خديجة أبو بكر القلوي😍: https://my.w.tt/E2nzUvfh93
*HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_
Wattpad @KhadeejaCandy
1⃣6⃣
Tun da yaga Anty Ummi tana jera masa abinci a center table ya san yau shi dan gata ne, abu ne mai wahala tai masa haka indai ba tea bane.
Gyara zama yai ya fara karyawa da wainar fulawa cox tana cikin favorite dinsa, sai da yai nisa da cin abincin sannan Anty Ummi ta fara magana a hankali.
“Zain ka san yadda nake da kai, ni yar uwarka ce kuma ba zan taba yi maka abunda zai cutar da kai ba, abu na biyu ban taba rokonka wani abu ba ban taba gabatar maka da wani abun ba, alfarma nake nema Zain ba zan cilasta maka ba, amman ina son kai nazari ka taimaki yarinyar nan dan girman Allah”
Ya juyo ya kalli Anty Ummi dake ta magana kamar ba tasan abunda zata fada ba, dan tattaro maganar take ta ko ina ta kasa kasa hadata.
“Wane taimako zan iya mata?”
“Ka aureta Zain...”
Ta fada kai tsaye, ba shiri ya furzar da dankalin dake bakinshi yana mata wani razanannen kallo. Sam be yarda Anty Ummi ta san abunda take fada ba.
“Zain yarinyar nan tana cikin matsala, kuma a bar tausayi ce Wallahi”
“Amman dan tana abar tausayi sai ki zo min da maganar da hankali ba zai dauka ba? Wani irin na aureta? Kin san yadda na tsani yarinyar nan kuwa?”
“Tsana mai wucewa ce Zain, kuma saboda na isa da kai yasa na nemi wannan alfarma a gurinka, kasan ban isa naje wani gurin na samu wani da wannan maganar, ban taba rokon kai min wani abun ba, kuma ban tsammaci haka daga gareka ba, nayi tunanin ni dima kamar mahaifiyarka ce Zain, na dauka girmamawa da mutumci da kake bani sun isa na roki abu kuma kai min, ka san dai ba zan taba yin abunda zai cutar da kai ba”
“Mai Martaba ba zai bari na auri wata yarinya da ba yar sarauta ba, ko kuma jinsinsa ba kuma jininsa, beside ba zan taba zuwa masa da wata magana akan wata yarinya ba, yarinyar ma Farhat”
“Ita Farhat din ba mutum ba ce? Ko kuma wata cuta ce a jikinta da zai hana namiji aurenta? Dole ne ka yi breaking rules din gidanku Zain kai namiji a gurin mahaifinka, ya kamata ka samawa yan'uwanka mata yanci kuma ka samawa kanka, lokaci yayi daya kamata ace kai kake saka musu rules ba wai su saka maka ba, ina son na taimaki yarinyar nan ko dan mu bawa tsohon saurayinta haushi”
Tunda take maganar kallonta kawai yake yana ganin kamar ba ita ce ba.
“Saboda kina son taimakonta sai kika babu wanda ya dace ya taimake ta sai ni ko? Yau dai kina son kanki da yawa Anty ke da kike tsoron abunda zai shafi gidanmu saboda dora miki laifi da suke amman yau ke da kanki kike cewa na karya dokokin gidan dan kawai na auri yarinyar nan?”
Tashi yai tsaye saboda ransa yai kololuwar bachi, sai dai yayi kokarin taushe fushinsa gudun kar ya fadawa Anty Ummi wata maganar marar dadi. Da kallo ta bishi har ya fice sannan ta dafe kanta tana fadin.
“Iyakar abunda zan iya kenan akanki Farhat, kuma bana nufin ki zama cuta a gareshi kai ne shaidata”
*** *** ***
Cikin bacin rai ya koma gida, wani bangaren kuma yana mamakin Anty Ummi, ko da ba Farhat ba baya jin ya shirya zaman aure da wata mace a yanzu balle kuma ita da yafi tsana da kowa, and taya Anty Ummi zata masa haka kamar wani karamin yaro?
Be yi awa daya a gidan ba, ya shirya cikin farar shadda ya fito part dinsa ya shiga part din Dada ya gaisheta sannan ya wuce part din Mai Martaba yai masa barka da tashi.
Bayan ya fito ya shiga motarsa ya nufi asibitin, yau kam ya dade be isa ba saboda yadda yake driving din. Rayuwarsa kawai yake tunani yadda zai gina wata sabowar rayuwar ba tare da Haleema ba, and now Anty Ummi ta dauko masa wata maganar marar dadin ji, a gida kuma Dada ta isheshi da zancen Hameeda da wanne zai ji? Ajiyar zuciya ya sauke yana tuna yadda ya baro Anty Ummi, kamar uwa take a gurinsa tayi masa hidimar da ko uwarsa ke da rai iya abunda zata masa kenan, and kullum yana neman hanyar da zai rama alherinta amman wannan ta masa nauyi, idan kuma be amince ba fa? Zata dinga ganin laifinsa ne? Let's assume ya amince din da wanne baki zai fadawa Mai Martaba cewar zai auro wata da ba zuri'arsa ba, da wanne ido zai kalli Dada? Hakan ba zai kara komai ba face fashim fahimta a tsakaninsu masarautar da kuma Anty Ummi.
Ya dade cikin motar yana wannan tunanin sannan ya tasheta ya hau titi ya karasa asibitin. A zaune ya samu Hafsatu manga tana ta kallon tv dake dakin ko juyowa ba tai ta kalleshi ba. Zaunawa yai saman gadon kusa da ita yana kallonta, ji yai kamar an zare masa duka damuwarsa dake ransa, sai ya samu kansa da murmushi ya kai hannu ya shafa kanta.
“Cutest...”
Ture masa hannu tai ta watsa masa wata banzar harara kamar ba wani sa'anta. Dauke kansa yai daga kallonta ba dan ya daina murmushin da yake ba, dan har ga Allah fushinta burgeshi yake.
Knocked akai kamin a turo kofar dakin a shigo Ibrahim dauke da kulolin abinci, ko be fada ba Zain yasan daga gidan Anty Ummi kulolin nan suka fito domin nata ne.
“Ga abinci inji Anty Ummi kuma tace tana gaida mai jiki sai ta shigo”
Ibrahim ya fada bayan ya aje kulolin tsohon dake bayansa kuma ya aje babbar jaka da plate da hitar ruwan zafi, sannan ya gaishe da Zain ya juya ya fita.
“Yaushe kaje can?”
“Yanzu nan ta kirani tace na zo na karba, bedsheet da fillo suna cikin jakar nan, and Yarima ta shawarce mu da mu kai report din yarinyar nan gurin yan sanda saboda gaba kuma tana da gaskiya, saboda Doc Hafsat ta fada min akwai yiyuwar ta kasa magana da wuri...”
Hafsatu manga na jin anyi maganar yan sanda tasa hannunta ta rike rigar Zain tana girgiza masa kai sai hawaye ya fara sauko mata. Zain ya kalleta ya kalli Ibrahim.
“Miyasa ni bata fada min ba?”
“Wata kila baka damu daka tambaya ba ne”
“Dole sai na tambaya? What kind of nonsense is this?”
Ibrahim ya dafa shi
“Easy Prince nan fa ba masarautarku ba ne”
Zain ya ture masa hannu.
“Don't told me this, aikinta ne ta fada min duk wani hali da yarinyar nan take ciki amman tana abu kamar wacce bata san aikinta ba”
“Kai kanka ka sani ma'aikatan nan suna shakkar fada maka abu kai tsaye idan ba kaj ka tambaya ba, shiyasa ta biyo ta wajena ta fada min, kuma ba maganar gaba daya take nufin zata dauke ba, tana nufin kamin ta warke zai dauketa tsawon sati daya ko kwana goma kamin da iya magana da shi saboda zai mata nauyi a yanzu”
“Wannan ba hujja ba ce sai idan wani abun tai mata, taya daga an dinke halshe za a ce ba zata iya magana ba har natsawon kwana goma? Ibrahim nima fa likita ne”
“Na sani, amman ai kai kwararren likitan zuciya ne, ita kuma na halshe so kowa da fanninsa, and ka daina dora mata laifi tunda ba ita tace yarinyar taje ta fasa bakinta ba, kuma ba ita tace ka kirata kasa tai mata aikin ba, kana magana kamar baka san wacece Doc Hafsat ba, har kake zargin tayi mata wani abun”
Iskar bakinsa ya busar ya kalli Hafsatu manga dake ta hawaye tana kallonsu.
“Ba gurin yan sanda za a kaiki ba, yi shiru”
Yasa hannunsa yana share mata hawaye. Ibrahim kallonsa kawai yake yana mamakin yadda Zain ya dauki lamarin yarinyar nan ya maida shi akansa.
FARHAT POV.
tsakanin jiya da yau wanda ya san Farhat kuma ya wayanceta sosai ne kawai zai iya shaidarta, domin ta canja gaba daya kamar ba ita ba, bata iya cin komai sai kuka da ciwon zuciya da suka sakata gaba, ga fargaba da tsoron abunda zai biyo baya, domin zuciyarta na raya mata zasu cilasta mata abunda bata muradi ne, sakamakon maganganun da take jin suna tasowa da kuma yadda taga familysu suna tausayin yaran da Anty Rukaiya ta bari da kuma mijinta da duk yabi ya fita hayyacinsa.
Ita kanta tana tausayin yaran, domin a kwana biyun nan kullum kusa da ita suke zama tare suke kwana abinci ma sai idan ta ci suke iya ci saboda suna ganinta kamar uwarsu ne, kuma tana rage musu kewar mahaifiyarsu, domin sun shaku da Farhat sosai.
Ranar da aka yi sadakan ukun Anty Rukaiya kowa ya tsammaci Ya Bashir binta zai yi saboda kuka da yake, babu wanda be tausaya masa ba, duk ya yabi ya zama wani iri, yana jin kewar matarsa a kusa da shi balle kuma idan aka watse aka barshi da yaran be san iya halin da zai kara shiga ba, a dayan bangaren kuma yana nadama da danasanin abunda ya aikata wanda yai sanadiyar mutuwarta matarsa uwar yayansa. Sai a yanzu ne yake gane ya tafka babban kuskure kuma shaidan ya rudeshi har yai galaba akansa, da ace yasan hakan zai faru ta tun farko be fara ba.
*** *** ***
YARIMA ZAIN POV.