Sashe 35
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Shikenan, zan kara auren shine burinki da na Hajiya ko? Da yan'uwana, daga yau matsalar kara aure ta wuce zan kara aure sai ki nemo min matar da zan aura"
Fashewa tai da kuka mai taba zuciyata ta nufi dakinta da gudu zuciyarta na mata mugun kuna saboda kalaminsa na karin aure abunda ko wace mace ta tsana.
"Kin gani ko? Yanzu ma ba a tsira ba"
Ya fada yana ware hannayensa tare da sauke ajiyar zuciya, komawa ya yi ya zauna ya dafe kansa sai ga hawaye masu zafi sun gangaro daga idanuwansa zuwa kuncinsa.
______________________________
Ya kuka ji wannan zubin? Akwai sugar kuwa?
Comments.
Share.
Like.
[3/4, 3:37 PM] Mrs Zainab Jega: *HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_
Wattpad @KhadeejaCandy
2⃣5⃣
Daidai gwargwadon dukiya Allah ya horewa Habib babu abunda ya nema ya rasa sai haihuwa, komai na duniyar nan Allah ya bashi ban da haihuwa. Hakan yasa Rufaida ta tsaya da kanta wajen ganin ya samu cikon burinsa domin shi ma yana son haihuwa, ita da kantata cilasta masa auren son auren a ranta domin kawai mahaifiyarsa ta samu kwanciyar hankali shima kuma ya samu.
Kanwar makociyarsu ta nema masa wato Safiya, Safiya mace ce da kowa ke yabon halinta ana yaba tarbiyarta, aurenta daya kishiya ta hanata zama, mijin ya sakota da cikin ta haihu a gida dan be zo da rai ba.
Rufaida bata tsira a gurin iyeyen mijinta ba, ganin ita ya saka ta nemo masa matar da kansa, zancen da suke cewa ta mallekeshi sai ya tabbata a garesu, duk wani abunda za a gudanar na bikin ita ce kan gaba sam ba zaka ganta kace tana kishi ba, sai dai idan ta shiga dakinta ta kanyi kukanta ita kadai, ko kuma a gaban kanenta kasancewar ita ce Babban a gidansu, babu irin magiyar da kannenta basu yi akan ta daina saka kanta a cikin lamarin auren amman ta ki.
Duk abunda Habib yai ma Safiya na kayan lefe sai da yai Rufaida, ya canja mata kayan daki har spoon na cin abinci sai da ya canja mata shi.
A dayan bangaren aka kawo Safiya, daidai gwargwadon ita ma iyayenta sun mata kaya kasancewarsu masu dan rufin asiri kuma sunsan wanda ta aura ba karamin mutum ba ne, rabar da aka kawo amarya Rufaida ta sha kuka kamar ta hadeye zuciyata ta mutu, hakika tana son mijinta kuma tana kishin ganinsa tare da wata, kanenta suna falo ita tana dakinta tare da Habib sai lallabata yake, be bar dakin ba sai kusan sha biyun dare, abunda ya tashi hankalin Safiya kuma ya bata mamakin ganin cewar ita amarya amman har tsowon lokacin yana tare da uwargidansa ita ya kyaleta.
Be taba nuna musu banbanci ba, yana kokarin kwatanta adalci dai dai gwargwadon yadda zai iya, sai dai har ga Allah son Rufaida yafi na Safiya a zuciyarsa wanda yasa baya iya boyewa yana nunawa a gaban kowa. Babu abunda ya canja daga Rufaida sai ma abunda ya faru, daman can tana masa biyayya amman na yanzu yafi na ko yaushe.
Tunda aka yi auren Rufaida bata da wata fargaba sai na gudun Safiya ta samu ciki, ita kanta tasan bata da matsala zata iya samun cikin a ko yaushe kamar yadda binciken likitoci ya tabbatar, amman ganin bata taba bari ba ya tashi hankali sosai tana ganin kamar ba zata taba haihuwa ba. Fargabarta ya koma damuwa tun daga lokacin da Safiya ta cika wata uku a gidan Habib, yanayinta da wasu abubuwan da take sai suka canja, saboda ta lura da cewar Safiya tana dauke da juna ba, Habib be fada mata ba ita kuma bata tambaya ba, amman taga alamun hakan a gurin Safiya saboda yawan amai da tashin zuciya da take, har ita da kanta take labarta mata cewar wannan shine wata na uku da bata ga al'adarta ba.
A week later kanen Habib mata na bangaren uwarsa suka zo har cikin gidan suka fada mata wai Safiya nada ciki wata uku, duk wani kokari ta yi na karta nuna musu damuwar a fuskarta, sai ta nuna musu ta jidadi da farincikinta duk kuwa da kasancewar sun yi mata hakan ne dan su bakanta mata rai.
A daren ranar ta samu Habib da maganar, sai ya rasa yadda zai kalli fuskarta kamar yai mata wani laifin.
“Ba a boye farinciki Habib, ni nafi kowa dacewar naji labarin nan amman baka fada mim ba sai da kanenka suka zo suka fada min”
“Na yi tunani abun ba zai miki dadi ba ne”
“Haba Habib shekara goma sha daya muna neman haihuwa fa, yanzu kuma ka samu sai nace be min dadi ba? Na maka murna Allah ya sauke ta lafiya”
Sai kawai ta fashe da kuka mai karfe.
“Akwai ciwo Habib, akwai ciwo sosai ga mace mai auren da zata bude idonta a gidan mijinta bata ga yayanta ba, Allah be nufa ni zaka haihu da ni ba saman ni na san matsalar daga gareni ne”
“Ban cire daga haihuwarki ba, ko Safiya zata haifi yaya ashiri ba zan sakawa daya daga cikinsu sunan yar da kike so ba, ke kadai zaki haifa min Hafsat, insha-Allah sai an kiraki da Maman Hafsat”
Tun daga lokacin da cikin Safiya ya fara girma, kullum Rufaida cikin kuka take saboda abunda yan'uwan Habib suke mata, kai kace basu san Allah ba, kamar ita ta hanawa kanta haihuwa. A kullum Safiya sabon hali take kirkirowa domin kawai ta musgunawa Rufaida ita kuma tana kokarin hade damuwarta ta nuna abun be dame ta ba..
Lokacin da cikin Safiya ya cika wata tara edd ta ya cika ta haifowa Habib tawayen mata biyu masu kama da shi, a ranar Rufaida ta raina kanta a gurin ya'uwan Habib babu kalar wulakanci da gorin da basu mata ba, balle ma ranar suna sai kanenta ne suke kare mata fadan da kuma shi Habib din da kansa. A yadda yanayin ya canja saboda damuwar matarsa sai ka dauka baya farinciki da haihuwar.
Wannan dalilin ne yasa Safiya ta fara shiga Malamai gudun kar nan ma Rufaida ta koreta ta hanata zaman aure kamar yadda wadancan kiyoshin suka mata, sai dai bata yi nasaraba, matukar Habib tai ma baya kamashi tayi kashin kudi har ta gaji. A haka suka kwashe shekara goma a tare, a lokacin twins sun yi wayo sai suka fi kaunar Rufaida fiye da mahaifiyar data haife su saboda kulawa da soyayya da take nuna musu, ta nan ma bata tsira ba sai suka ce ta shanye twins din suma magani tai musu.
Ana cikin haka Allah ya bawa Rufaida ciki baya ta kwashe shekara ashiri da daya a gidan aure babu ko bari, farinciki gurin yan'uwanta da Habib da ita kanta ba a magana, Hajiyar Habib ce kawai sai yan'uwanta da Safiya ne basu jidadi ba. Hankalin Safiya ya tashi sosai ganin yadda Habib yake rawar jiki da Rufaida ko kasa baya son ta taba, sai ta sake shiga gurin malamai tasa aka taushe cikin Rufaida, ga ciki ya tsufa amman ba haihuwa tun ana kidayar kwanaki har lissafi ya bace musu, idan aka je asibiti sai su ce su basu ga komai ba babu ciki a jikinta bayan kuma gashi nan ya kumburo haihuwa ko yau ko gobe.
Wannan damuwarce ta shiga zuciyar Rufaida ta hanata sukuni da walwala duk tabi ta rame ta lalace kamar ba ita ba, babu irin neman maganin da ayi amman ba a dace ba, a haka har ta kwashe shekara biyar dauke da cikin bata haihu ba. A lokacin duk wanda ya kalleta sai ya zubar mata da kwalla saboda mawuyacin halin da take ciki.
Hakan be wadatar da Safiya ba, ganin har yanzu Habib yana sonta yana bata kulawa kusan kullum ma yana tare da ita, yasa ta koma gurin bokan da yai mata wacan aikin ya sake yi mata wani na a haukatarda Rufaida ta bar gidan ko mijinta ya daina nemanta.
“Za'ayi miki aikin, amman fa duk ranar da ta tako kafarta cikin gidan nan, akanki zai koma”
“Ai ni so nake ayi mata wanda zata bar garin gaba daya ta tafi can inda ba a santa ba, ta bar min mijina ni kadai”
Sai da bokan ya jadda mata abubuwan da zata kawo da kuma ka'idar aikin, sannan ta zube masa kudi ta tashi.
Kwana biyu da yin aikin ya kama Rufaida, ranar wata juma'a babu kowa sai ita kadai a part dinsa domin Kuwa Safiya ta saka yayanta a part dinta ta rufe saboda ta san mugun abun da tai, ji tai kamar an tsikareta sai ta tashi tsaye da sauri, a take kanta yai mugum sarawa sai da dafe kan a hannu biyu saboda taji yana juna mata, dakinta ta shiga ta bude durowa ya dauko awarwaron da Habib ya bata mai sunanta dana Hafsat ta riko ta fito daga dakin tana ta kukan da bata san inda yake fito mata ba. Kanta ta daga sama tana ta kallon falon kamar bakonta sai kuma ta nufi kofa da sauri tana ta dafe kanta ta fita daga gidan gaba daya. Bata yi tafiyar minti talatin ba amman da yake sihirine sai aljanun suka dauketa sai gata cikin kauyen Kufawa dake karkashin karamar hukumar Maru.