← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 93

Sashe 40

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajiyar ta daka mata tsawa, sai kawai ta fashe da kuka ta tashi taje gurin wata dattijiwar dake jiranta suje tare. Sai da suka taba yar fira da Hajiyar sannan ta tashi tare da kama hannun Hafsatu manga suka fice. Tana isa bakin titi ta tari Napep suka hau basu zame ko ina ba sai 88 estate. A bakin gate Mai napep din ya sauke su saboda ba a bari masu Napep ko a achaba su shiga ciki, da kafa suka taka har 54 block, a bakin kofar ta tsaya ta danna bell.
Wata kyaukawar mace ce ta bude kofar gidan, fuskarta ba yabo ba fallasa ta shigarda idanuwanta can ciki kamar bata son kallon mutane.

“Oh ke ce”

Tana fadar hakan, sai matar dake rike da Hafsatu manga ta washe hakora.

“Ee ni ce Hajiya ya gida?”

“Lafiya kalau, shigo”

Ta fada tana wangale mata kofar falon. Cikin falon suka shiga daga ita har Hafsatu manga kasa suka zauna, sama sama take amsa gaisuwar da Matar take mata kamin ta kalli Hafsatu manga.

“Wannan ce yarinyar?”

“Ee ita ce ke gaisheta”

Hafsatu ta sakar mata ido kawai tana kallonta ba tare data gaisheta ba.

“Dee ga yarinyar”

Wanda matar ta kira da Dee ya dago kansa daga kan computersa jiyo ya kalli inda suke zaune, karaf idonsa suka sauka kan Hafsatu manga wacce itama kallonsa take. Kara dagowa yai da kyau dan tantance abunda idanuwansa suke gani, tasowa yai ya dawo kusa da matarsa ya zauna yana cigaba da kallon Hafsatu manga, awarwaron da ya gani a hannunta ne ya tabbatar masa da ita din ce.

“Ita ce yarinyar da zata dan taya ni aiki”

“Okay ai kun gama magana ko”

“Ee 15000 per month”

“Yayi kyau, Allah ya bamu ikon riketa da amana”

“Amin amin Allah ya taimaka alhaji, ke kuma ban da rashin ji ban da shegen kukan nan da kike”

Hafsatu manga ta lake kafada kamar ba data ita matar ke magana ba, Sai yai murmushi Hafsatu na kallonta ya kashe mata ido daya.
[3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *HAFSATU MANGA*

29

Yana zaune a gurin a kai yi knocked kofa, be dago ba be kuma motsa daga inda yake ba mai knocked din kuma be fasa ba, har sai da Farhat dake dakinta ta fito ta nufi kofar ta bude. Ganin Anty Ummi yasa ta murmushi ta rumgume irin tayi missing dinta sosai din nan.

“Sannu da zuwa Anty”

“Yauwa Amarya”

Zain be dago kansa ba har Anty Ummi ta shigo cikin falon ta zauna kusa da shi tana kallonsa zuciyarta cike da tsoro.

“Zain”

A maimakon ya amsa mata sai kawai ya tashi ya dauki wayarsa da keys dinsa ya fice daga falon. Da kallo ta bishi har ya fice sannan ta maida dubanta gurin Farhat tana sauke ajiyar zuciya.

“Idonki ya kumbura Farhat kuka kika yi?”

Farhat ta dan kawar da idonta.

“Ina jin kamar ba zan iya zama a gida nan ba, baki da hankali, useless, karki sake shigo min daki, kalmomi ne masu daci da Zain ya fada min a tsakanin jiya da yau”

Anty Ummi ta bar kujerar da take zaune ta koma kusa da Farhat ta zauna ta kama hannunta ta rike.

“Haka naji lokaci da mahaifiyarmu ta tafi ta barmu, nauyin komai sai ya koma a kaina, you know aurena na farin ban taba son mijina ba, sai abun ya zame min biyu babu t inda zan jidadi”

Farhat ta dago ta kalleta idonta cike da kwalla.

“Amman wannan yana da banbanci Anty, bana son shi shima baya so na, amman ina kokarin danna nawa na masa biyaya, sai dai komai na masa kamar bana burgeshi, a dayan bangaren kuma ga wadannan yan'uwan nasa da basa so na, bana son kashe aurena a yanzu saboda za a min dariya, mahaifiyata kuma ba zata karbeni a yanzu ba”

“I know how my brother is, amman mutum ne mai sauki kai da hakuri, be kamata ki fara complain tun yanzu, aure ba kika yi kin shiga wata sabuwar rayuwa kuma wata sabuwar ibada wacce sai kin yi da gaske tukuna zaki iya yakar zuciyarki akan abubuwa da dama”

“I know Anty, zan yi kokari na danna zuciyata ko dan hakan na nufin na cutar da kai ne, gudun kar na baki kunya, amman Anty minene alakar Zain da Hameeda? Miyasa wannan tsohuwar Dada bata son Zain? A yadda na fahimta kamar dukansu basa son shi”

Ta fada tana share hawayen idonta.

“Na gode, zan sanar miki amman ba yanzu ba, yanzu ina son ki fada min abunda kike bukata”

“Ina da bukatar jin muryar Mahaifiyata, ina son wayata a kusa da ni”

“Akwai sim Pack a hannunki? Zan sa a miki welcome sai na siya miki sabuwar waya”

“Eh yana hannuna, amman Anty miyasa Zain yake fushi da ke? Ko duk saboda aurena ne?”

“Ba saboda ke ba ne, saboda wani abun ne na daban, zan koma tashi ki dauko min pack din”

Ba musu ta tashi taje ta dauko ta dankawa Anty Ummi sannan Anty Ummi ta tashi ta fice cikin yanayin damuwa, daga part din Zain part din Hajiya Hadiza ta shiga suka gaisa, daman ta saba a lokacin da Haleema take cikin gidan idan ta zo sai ta biyo ta gaishe da Mai Martaba da Hajiya Hadiza sannan ta wuce.

Fita yai daga gidan gaba daya, ba shi tabbacin tsanar Anty Ummi yai ko aa sai dai yana da tabbacin baya son ganinta ko magana da ita a yanzu.
Tunani biyu yake zuwa masa a lokacin daya, taya zai bar wannan abun daya faru ya shiga tsakaninsa da Anty his own sister macen daya ke daukarta kamar mahaifiyarsa, what if mahaifiyarsa tana raye tai Hafsatu manga haka zai iya fushi da ita kuwa? Wannan abun yake ta tunani, while zuciyarsa already ta tsani Anty Ummi a yanzu?

“To mi tazo ta fada min? Mi zata ce min? Dama na tsaya naji selfishness dinta”

Ya fada dai dai lokacin daya faka motarsa a harabar asibitin, wayarsa tai ringing yana dubawa yaga Anty Ummi, sai ya maida wayar cikin aljihunsa. Ya fita ya nufi office dinsa, wayarsa ta sake ringing a karo na biyu bayan shigowarwa cikin asibitin sai dai wannan karon ba Anty Ummi ba ce Ibrahim ne.

“What”

“Kana ina”

“Office”

“Okay gani nan zuwa”

Zain ya maida wayar aljihunsa sannan ya kai hannunsa ya tura kofar office din ya shiga, saman kujerarsa ya zauna ya lumshe ido yana juyawa a hankali.
Kamar an tsikareta shi sai kuma ya tashi da sauri, tashinsa yayi daidai da shigowar Ibrahim a office din.

“Ina zaka je?”

“I was thinking of mu saka cigiyarta a gidan redio”

“Matsayinka na wa?”

Ya kasa amsa masa.

“Baka da tabbacin inda yarinyar nan take Zain, maybe ma bata cikin garin nan abunda nake ganin yafi ka kawarda fushin dake cikin ranka ka fuskanci Anty Ummi kui magana ko zaka samu wani bayani ta yadda zaka ganota”

Hannayensa ya zuba cikin aljihu ya nufi window office.

“Duk inda yarinyar nan take Ibrahim tana cikin damuwa yanzu haka, jikina na bani yanzu tana can tana ihu wata kila wani abun ake mata”

“No no bafa matarka ba ce, kuma ba yar'uwarka ba ce kana daukar abun nan da girma Zain, ni a ganina be kamata akan yarinyar da baka sani ba ka bata da Anty Ummi har kake kokarin jefa kanka cikin wani hali”

“Ina son yarinyar nan Ibrahim fiye da tunaninka, ina jinta kamar wani bangare na jikina ta shiga cikin raina ta zauna irin zaman da ko nuninta akai raina ba ci yake, karamar yarinya ce wacce bata san komai ba, ina jin kamar ba zan taba samun sukuni ba idan har ban gano inda yarinyar nan take ba, duk halin da take ciki a yanzu saboda ni ne ta shiga”

“Ba saboda kai bane, karka dorawa kanka laifi, yanzu zanje nai magana da Anty ko zamu samu wani abu daga gareta”

“Thank you”

Zain ya fada murya can kasa alamar mood dinsa ya canja. Suna tsaye Doc Hafsat ta shigo bayan ta yi knocked tana rike da wasu files.

“Good morning Doc ga files din friday”

“Aje kan tebur”

Ya fada ba tare daya kalleta ba.

“Wai Doc ta ina takwata ta a miss her”

Wannan karon Doc Ibrahim take kallo.

“Bata nan”

“Bacewa tai?”

Kasa amsa masa da Ibrahim yai ne yasa tace

“Daman na san za a rina, Allah kadai yasan iya duniyar da yarinya zata tafi...”

Zain ya juyo ya kalleta.

“What do you mean?”

Kasa cewa komai tai sai kallon tsoro take masa.

“Talk”

“I mean saboda bata jin magana”

Doc Ibrahim ya daga mata hannu.

“Okay just go”

Bayan ta fice Zain ya kalli Ibrahim

“Kasan wani abu ni fa ban yarda da yarinyar ba and...”

“And what Zain? Sai kuma ya biyo ta gurin Anty Ummi? Ka manta ta hanyarta ne yarinyar ta bata”

Ibrahim ya dafa shi.

“Calm down Zain, haba dai kana kokarin wani hali da ban sanka da shi ba”

Zain ya ture masa hannunsa ya nufi kofar fita, da kallo kawai Ibrahim ya bishi har ya fice sannan ya girgiza kai.

HAFSATU MANGA POV.

Bata cin abinci da aka bata ba, kuka tai ta yi har garin Allah ya waye, da safe aka tarasu tare da wasu yara wadanda suka darata girma aka raba musu abun kari mai kyau. Amman Hafsatu manga bata ci ba babu abunda take kira sai Mamanta, hankalinta be kara tashi ba sai da likitan da zai mata allura ya zo a gaban idonta akai ma wasu yaran allura, ana kawo gareta ta rika ihu kamar za a cire mata rai, sai da mutum biyu suka riketa sannan aka mata allurar.

Hajiyar na tsaye tana kallon abunda yake faruwa, tun jiya ta soma tsarguwa da sha'anin Hafsatu manga saboda kuka da take tayi tun jiya.

“Ina jin yarinyar nan kamar ba da son ranta aka kawo ta nan ba, kukan nan da take yayi yawa ni bana son kuka Wallahi”

“Waya kawo miki ita Hajiya”

“Wallahi wani daga cikin masu kawo mana yan aiki, shiyasa bana son amsar irin yaran nan a hannun namiji saboda ba a gane gaskiyarsu”

“Haka ne, amman ai data saba Shinkenan”
Chapter 40 · 0% Book details