← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 93

Sashe 69

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari da misalin takwas da rabi ya dawo asibiti tare da breakfast din da mai aikinsu ta girka. Nan ma ta ci ba laifi sai dai ta rame sosai kamar wacce ta shekara guda kwance tana ciwo. Misalin sha daya na safe twins suka iso gida, ko hutawa ba su yi ba suka dauki hanyar asibitin kowa wacce hankalinta a tashe ance mahaifiya babu lafiya gashi jiya sun ji muryarta ba a yadda suka saba ji ba.
Sun tararda da ita fiye da yadda suke tsammaninta, ramar da tai ta daga musu hankali sosai ga kamaninta duk sun canja, a asibitin suka wuni da ita duk wani motsi nata yana idonsu abun uwa da yayanta, sai dai sun kasa gane dalilin hawayen da take tun da suka zo har yanzu.
Bayan sallah magariba Husaina ta shigo da waya a kunnenta ta mikawa mahaifiyarta.

“Mama ga Anty Ummi za ta miki ya jiki”

Ta karba tana amsawa ahankali sannan ta mayar mata da wayar.

“Okay shikenan zuwa jibi idan naga jikin Mama da sauki zan yi kokarin na dawo inshallah”

Daga haka ta kashe wayar. Ta zauna kusa da Hassana wacce ke bare ayaba tana ba mahaifiyarta. Hassana ta kalleta.

“Karbar case din za ki yi?”

“To ya na iya Anty Ummi ce kin san ai ba zan ki ba”

“Amman kin fada min Aliyu ya hana ki karbar criminal case irin wannan”

Hussaina ta juyo ta fuskanceta da kyau.

“Yarinyar nan is innocent, ba ita ta aikata laifin nan ba, dole na taimaka mata, ko Anty Ummi ce tai request wannan bukatar sai kuma naki karba, bayan bata taba nuna tana son wani abun ba. Kinga ai ba zata jidadi ba”

“Yarinyar ta ba ni tausayi, taya za a ce ta iya kisa, duk da ban ganta ba amman a yadda kika fada min ta bani tausayi sosai, ya kamata ki taimaka mata kam, amman ki fara magana da mijinki tukuna”

“Ee zan fada masa ai, rashin lafiyar nan ce ta Mama tasa ban yi masa maganar ba, kuma kinga yau ya kamata ace na karbi case din naje naga yarinyar amman bana gari, amman idan Hajiya ta samu sauki zuwa jibi zanje, dan karshen watan nan take son a shiga kotun, and the most painful part yarinyar bata da iyaye ba a san inda mahaifiyarta take ba, haka ma mahaifinta”

“Amman ina Anty Ummi ina ta hadu da ita?”

Hannu ta kai ta dauki abaya ta bare ta soma ci sannan ta ce.

“Kanenta wanda suke the some mother, shi yaga yarinyar kofar gidanta ya shigo da ita, ita yarinyar daga kauye take, yanzu haka bata san inda kowa nata yake ba, ai kinsan shi ma Zain”

“Oh na sanshi dan Sarkin nan ko? Amman waya laka mata kisan kan?”

“Wata cousin dinsa ce, ita muke tunanin ta kashe ta, tare da shi ma suka zo da Anty Ummi, saboda yarinyar a gurin Anty Ummi take sai ta hada baki aka siyar da yarinyar a wata masarautar, shi yaje ya dawo da ita”

“Kai amman Hussaina case irin wannan yana da hadari sosai, kin san ita kuma yarinyar zata yi kokarin ganin baki ci nasara ba”

“Amman nima zan yi kokarin ganin na ci nasarar”

Hawayen da suka ga suna zuba a idon mahaifiyarsu ne yasa suka daina firar da suke suka maida hankalin gunta.

“Lafiya Mama?”

Hassana ta tambaya. Sai tai murmushi dan ta fahimci inda zancensu ya dosa.

“Hausawa sun yi gaskiya da suka ce sheri dan aike ne, kuma alhaki kwaikwayo ne, ta ko ina gaskiya kara bayyana take daman komai nisan dare dole ne gari zai waye...”

Basu fahimci abunda take magana akai ba, san basu dauka akan maganar yarinyar ne ba. Hussaina ta tashi ta koma kusa da ita ta zauna.

“Mama me kike nufi da wannan maganar?”

Kallon Hussaina tai sai ta fashe da kuka.

“Abunda n aikata ne zai dawo min, shekara talatin da suka wuce na binne wani sirri wanda yanzu yake bayyana kansa, ba zan iya cigaba da aje wannan maganar ba”

“Ni ban gane abunda kike nufi ba”

“Yarinyar da kuke zance a yanzu, ita ce yarinyar da mahaifinku ya zo yana min zancen cewar yarsa ce”

“Taya...?”

Duk su biyu suka hada baki gurin tambayarta.

“Shekara goma sha biyar da suka wuce, lokacin kuna primary school, ai kun san Rufaida ko? Aboiyar zamana”

“Yes yes yes yes”

Cewar Hasana cike da son jin labarin.

“Da ciki ta bar gidan mahaifinku, bayan ta shekara hudu da shi a gida, nice sila ni na mata asiri aka taushe ciki, kuma nai mata asiri aka haukata ta ta bar garin....”

Ta fashe da kuka. Husaina ta rufe baki tana zaro ido, yayinda Hassana kuma ta jefar da ayabar dake hannunta ta dade kunnuwanta.

“Aa Mama wannan ba gaskiya ba ne, ba ke ba ce”

Ta kalli Husaina wacce tai maganar tana nuna kanta.

“Ni ce nina aikata, kuma na san Allah ba zai barni ba, bokan ya fada min duk ranar da ta shigo cikin gidan nan, ni ce zan haukace kuma nasan ranar ta kusa zuwa indai tana raye”

Husaina ta rumgumeta da sauri tana fashewa da kuka. Cikin kuka Hassana ta ce

“Mama mi yasa kika aikata?”

“Saboda kar Mahaifinku ya koreni, na yi aure na farko ina son mijina matar ta rabani da shi, babanku kuma saboda yana son haihuwa na aureshi, duk da cikin dana samu be taba nuna min so kamar yadda yake nunawa Uwargidansa ba, ina jin tsoron irin son da yake mata, musamman lokacin data samu ciki sai hankalin kowa ya koma kanta shiyasa na aikata saboda kar na rabu da mahaifinku”

Ta kara fashewa da kuka. Husaina tai saurin sa hannu ta share mata hawayenta ba tare da ta tsayar da nata ba.

“Ba laifinki ba ne Mama, laifin Abbah ne da be nuna banbanci ba, da duk haka be faru ba”

“Wane irin laifin Abbah? Wannan son zuciya ne kawai, ta biye zuciya akan namiji ta aikata abunda zai iya kaita wuta, kuma at the end gashi zai dawo kanta”

Husaina ta yi saurin kallon Hassana wacce ke maganar tana hawaye.

“Ba zai dawo ba, indai har sai yarinyar ko mahaifiyarta ta dawo zai koma kan Mama, to ba zai taba dawowa kanta ba har abada”

Hassana ta share hawayenta cikin muryar kuka ta ce

“Me kike nufi?”

“Ina nufin zan aikata duk abunda zan iya, wajen ganin ita da mahaifiyarta basu dawo ba, saboda ta mu mahaifiyarmu”

“No wait don't tell me kema wani abun za ki aikata...? This is unfair”

“Zan aikata komai akan mahaifiyata, saboda mu tai haka, ba zan bar wani abu ya cutar da ita ba ko baki gane ba?”

Hassanata girgiza kai tana hawaye.

“No no no ban gane ba, ita ba mahaifiyar wata ta cutar ba? Matar wani? Uwara wata? Kanwar wasu? Yar wasu? A maimakon ki taimaka mata wajen neman yafiyarsu sai ki ce zaki aikata wani laifin kuma? Wannan wane irin son zuciya ne? Sai yanzu na gane wahalar da na ke sha a gidan aure saboda ke ne Mama, mijina yana da abunda zai ciyarda ni ya tufafatar da ni amman baya yi, tun da na aureshi ban taba jin dadin rayuwar aureba, komai a cikin salary na nake yi na yi ma yara na, ya gwammace yaje ya bawa matan banza a waje mu ya barmu, idan nai magana ace nai hakuri auren zumunci ne, ashe duk laifinki ne Mama, yar wasu kika azabbatar shiyasa ke ma ake azzabtarda ni, ki nemi yafiyar wadanda kika cutar Mama, kuma ki sanar da Abbah dan nasan be sani ba”

Husaina ta mike tsaye.

“Wane irin a sanar da shi? Babu wanda zai san da wannan maganar sai mu kadai, zata nemi yafiyar Allah kawai, amman sirrin Mama ba zai taba fallasuwa ba, ba zan bari wani abun ya cutar da ita ba”

“Ki kirga Husaina, dakika bayan dakika, minti bayan minti, awa bayan awa, yini bayan yini, dare bayan dare, wata bayan wata, shekara bayan shekara, shekara nawa baiwar Allah nan yai tana dauke da wahala? Yanzu kuma ga yarta nan tana wahala duk sanadin Mama, ciwon da Abbah yake saboda rashinta ne sai kuma ki ce ba za a sanar da ita ba, wannan game din da Mama take playing ta kare, shekara talatin tana cutar baiwar Allah, idan ke ce ya zaki ji? Dole ne Abbah ya san da wannan dole na fahimtar da shi komai, sannan na nema mata yafiyarsa”

Hassana na gama fadin hakan ta kai hannu ta dauki veil dinta, sai Husaina ta rika ta juyo da ita.

“Ki yi tunani kamin ki aikata abu Hassana, ko ki fadawa Abbah ko karki fada masa ba zan bar yarinyar da mahaufiyarta su dawo ba, tunda dawowarta na nufin tafiyar tawa mahaifiyar ne mark my words...”

“Ki yi duk abunda zaki iya Husaina but trust me ramen karya kurarrene, kuma gaskiyar ta bayyana kenan...”

Tana kaiwa nan ta dauki handbag dinta ta fice.
[3/25, 9:04 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 49

“Ki yi shiru Mama ki kwantar da hankali, abunda ya faru kaddara ce baki isa ki kauce mata ba”

Husaina ta fada tana share mata hawayenta. Ita kuma ta kasa daina kukan ga azabebben ciwo da kanta yake. Husaina ta nufi jakarta ta bude ta dauki wayarta ta kira yar'uwarta, ta dade tana ringing sannan ta dauka.

“Hassana ki yi tunani kamin ki aikata abunda za ki aikata, wannan mahaifiyarmu ce tana da muhimmanci a garemu, yanzu kin fi son ki sakata a damuwa...?”

Bata amsa mata ba, ta kashe wayar, ta jingina kanta jikin kujerar tana hawaye, fadin da rashin fadin su suka tsaya mata a rai, zuciyarta nata raya mata fadin shine alheri. Wayar da ke hannunta ta cire ma key ta kira Anty Ummi, sa da ta dauka sannan ta fara tambayar kan abunda zata ce mata.

“Hello Hasana baki jina ne?”

“Ina ji Anty Ummi, wata tambaya nake son nai miki, wai yarinyar da ke gurinki yar Abbah ce”

Daga can cikin wayar Anty Ummi tai shiru kamar ba za ta amsa ba.

“Miyasa kike tambaya?”

“Ina son sani ne, Hajiya ce tai min wata maganar wacce ta daure min kai”
Chapter 69 · 0% Book details