← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 93

Sashe 67

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da ya shiga office dinsa be fito ba, ya zauna a ciki har dare, babu irin magana da hakurin da Ibrahim be bashi ba, amman uffan Zain be ce ba. Har sai da Mai Martaba ya aiko kasanensa waziri ya tafi da shi. Ana isa ya bude motar ya fita ya nufi part din Mai Martaba, ko da ya shiga shi kadai ya samu a karamin falonsa, be daga kai ya kalli Mai Martaba ba kuma be bude baki ya yi masa sallama ba. Mai Martaba na kallonsa ya san dansa yana cikin damuwa domin alamu sun nuna haka ga idonsa da yai mugu ja kamar an watsa masa barkono a ciki, kusa da Mai Martaba yaje ya zauna ya sadda kansa kasa yana sauraren abunda Mai Martaba zai fada masa, shiru shiru be ji Mai Martaba yace komai ba, hakan yasa ya dago kansa ya kalli Mai Martaba sai hawaye suka zo masa.

“Dan Allah karka sa bakinka a cikin maganar nan Mai Martaba, ba sheri nake son yi ma Hameeda ba, ina da yakini da tabbacin cewar ita ta kashe Farhat, abubuwa da yawa suna faruwa ban tba sanar maka ba, saboda bana son tashin hankalinka, na san baka son Farhat, amman ni hakkinanne na kareta ko da bata da rai...”

Mai Martaba ya kalleshi irin kallon nan na natsuwa dake tsakanin da da uba.

“Ka ji abunda na ji a lokacin dana rasa mahaifiyarka, ka akwai ciwo sosai Zain karasa mutum mai muhimmanci a rayuwarka, ina tausayin rashin mata biyu da kai da kurciyarka, amman ina son ka kwantar da hankalinka, kuma kai hakuri, ba zan goyin bayan matarka a cima Hameeda mutunci ba, haka kuma ba zan goyi bayan Hameeda a cutar da kai da karamar yarinya ba, ba zan hana ka saka karar a kotuba, amman ina rokon ka janye zancen kama Hameeda a cell, a dawo da ita gida, ka taba mutuncin masarautar nan Zain kuma ka taba mutuncin Hameeda ma sawa a kamata a kaita cikin cell a kulleta”

“Mai Martaba Hameeda shu'uma ce, ita ta kasheta”

“Na san shu'umace tun daga lokacin da Hajiya Hadiza ta fada min abunda ta aikata maka, amman baka da tabbacin ita tai kisan Zain dan haka karka yanke hukunci a take, ka bar hukuma da kotu su yi aikinsu”

“Mai Martaba Hameeda ta kashe Farhat ne saboda tana tsoron kar asirinta ya tonu, ita ta siyar da yarinyar nan a masarautar Damagaram....”

Daga nan Zain ya tsakurawa Mai Martaba abunda ya faru from AtoZ. Mai Martaba ya jinjina kai yana mamakin karamar yarinya kamar Hameeda amman ta iya shirya wannan abun, ba zai karyata dansa ba dan yasan ba zai fada masa karya ba, dama ya yanke da lamarinta tun daga lokacin da Hajiya Hadiza ta labarta masa abunda Ikram ta fada mata wanda ita da Ikram din suke zargin ita ta shirya komai, domin Ikram din ta fada mata ko da suka je baya cikin hayyacinsa.

“Hakan ba zai hanani saka baki a cikin lamarin ba, domin a karkashina take, tana zama ya a gurina, da hukuma ce zata yai aikinta ba zan hanata ba, amman kai ba zan zuba maka ido ka ci mutuncinta ba, dan haka ina umartarka da kasa a saketa, kotu zata bayyana komai, adalci daya zan maka Zain ba zan hanaka rawar gaban hantsi na kwatowa matarka hakkinta ba”

Zain yaji dadin jin wannan maganar daga bakin Mai Martaba, hakan ya nuna yana goyon bayan aje kotun ba kamar yadda yake ganin kamar zai bari ba, daga nan Mai Martaba ya dora masa da nasiha da kuma nuna akan halin rayuwa. Hakan yasa Zain ya dan sake har ya tashi ya fita, da kansa yaje station din yasa aka saki Hameeda sai dai be yarda ko ido biyu sun yi ba ya dawowarshi, ita ta ari wayar wani a cikin gurin ta kira Dada ta sanar mata ansake ta, da Dada aka zo daukarta da Hajiya Maryam, tana ta kuka gwanin tausayi kuka kisan data aikata take gaba daya jin take ta tsani kanta, natsuwarta ta bar jikinta, bata jin abunda take ji a yanzu ba, ko a lokacin da Haleema ta mutu bata ji irin wannan ba wata kila saboda ita ba wukar ta soka mata kamar yadda tai ma Farhat ba. Hajiya Maryam da Dada hakuri kawai suke bata sun dauka ko tana kukan ne saboda kazafin da tozarcin da Zain yai mata. Sai dai har aka isa gida bata daina kukan ba, tana shiga dakinta ta kulle kanta cikin dakin ta fadi kasa ta fashe da kuka, Dada Ma kuka take a dakinta ganin Yar lelenta na kuka, wai ai dole Hameeda tai kuka saboda Zain ya tsaneta ya wulakantata.

*** *** ***

Cikin damuwa da bakinciki ya koma Kaduna, yana ta neman dalilin daya hanashi neman matar amman ya rasa, yana ta tunanin ya shiga ciki gari ya nemanta ko kuma ya dawo garin daya hadu da yarsa sai yaji ba zai iya ba, amman tabbas ya san wannan yarinyar yarsa ce, amman yana jin kamar ba zai iya komai a kai ba. Tunani yai masa yawa ta ina zai fara me zai yi yana cikin ransa amman shi da wani kuzarin aikatawar. Yana sauka jirgi direbansa ya zo daukarsa, sai yasa aka wuce dashi asibiti saboda yana jin kamar jininsa ya hau.

Likitan daya saba duba shi ne ya duba shi wato likitansa, sai dai yai masa magana akan yawan tunani kamar yadda yake masa ko yaushe, sannan ya bashi kyakkyawar kulawa domin jininsa ya hau kusan 230, kwantar da shi akai asibiti, duk yadda ya so ya sha ruwan sanyi sai lokitan ya hana saboda lafiyarsa.

Sam ya manta da ya kashe wayarsa sai yanzu da yake da zimmar kiran Hajiya Safiya ya fada mata cewar ya iso, kunna wayar yai ita ce wacce ya fara kira sai akai rashin sa'a Hajiya Halira ta dauka wato yayarta. Bayan sun gaisa take sanar masa cewa bata da lafiya.

“Me ya same ta?”

“Ciwon kai ne wai kan take jin kamar zai tsage”

“Kuje asibiti mana, nima gani anan zan dan huta kamin anjima jinina ya hau”

“Subhanallahi lafiya dai? Ko wani abun ya faru”

“Ba komai”

Ya kashe wayar, sai ya kira Number Ummi kamar yadda yake rubuce a number, ta dade tana ringing sannan ta daga ciki yanayin damuwa.

“Ummi dan Allah yaron nan nake son magana da shi, ina son ki hadani da shi”

“Ya Wallahi yanzu ba zan iya ba, muna cikin matsala yarinyar da ka ce yarka ce ita ake zargi da kisan kai ta kashe matar Zain yanzu yanzu haka tana hannun yan sanda”

“What..?”

Ya furta da karfi yana tashi daga kwancen da yake.

“Garin ya haka ta faru”

Nan ta zayyana masa abunda aka fada mata akan maganar da kuma matsayarsu. Yana sauke wayar ya kira direbansa ba tare da sanin likitan ba ya bar asibiti ya koma gida. Cikin tashin hankali ya shiga falon Hajiya dan labarta mata abunda ya gani, sai ya tararda yayarta da kanwarta suna zaune ita kuma tana bedroom tana shiryawa dan zuwa asibitin ganin ciwon kanya matsa mata.
Da sallama ya shiga falon suka gaisheshi ya amsa musu suna masa ya jiki.

“Al-hamdulillah”

“Alhaji da ka rage yawan tunanin nan ance shine yake kara janyo maka hawan jini fa”

“Wato wani abun ne na gani wanda ya tashi hankalina sosai, wata yarinya na gani mai kama da Rufaifa, kuma ina da tabbacin yarta ce”

“Wace Rufaidar dai Alhaji?”

“Rufaida Matata mana uwargidana”

“Wallahi karya ne Alhaji ba yarka ba ce, duk wanda ya ce maka yarkance yana son ya yaudareka ne kawai”

Cewar Hajiya Safiya wacce ta fito daga dakinta ba tare da ta karasa shirin da take ba, sakamakon zancen da taji Alhaji na yi.

“Babu wanda ya ce min yata ce, ni na ganta da idona a gidan yar'uwata, domin naga awarwaron dana siyo mata a lokacin da ba haife ta ba, sai dai ita yarinyar dana gani yanzu karama ce”

“Ka gani ko? Rufaida ta bar gidan nan da ciki yanzu sama da shekara ashiri da biyar ko zamanta gidan nan da cikin nan ai ta shekara biyar, sai kuma ace ta haifi karamar yarinya ace yarkance, wallahi ba yarka ba ce yaudararka kawai ake son yi karka yarda”

“Sai na yi bincike sannan zan tabbatar da yata ce ko ba yata ba, amman alamu sun nuna cewar yata ce, dole ne na nemo Rufaida duk inda take a duniyar nan”

“Na shiga uku, Wallahi karya suke maka Alhaji ba yarka ba ce, dan girman Allah karka kawo Rufaida gidan nan, wayyo Allah na...”

Sai ta dafe kanta tana jin kamar zai rabe mata biyu.....

_______________________________

Ku yi hakuri da rashin Editing, kuma ku yi hakuri da yadda nake rushing din rubutun, maybe ba zaku ji dadinsa yadda ya dace ba, amman ina son mu gama ne kamin azumi. Ga wadanda basa son mutuwar Farhat kuma kuyi hakuri, haka na tsara labarin tun farko, idan wasunku basu manta ba na fadi cewar Hassana da Husaina za su tsaya a gaban alkali domin shari'a that's means akwai kisan kai a ciki kenan. Ina fatar za ku fahimta. Thanks ♥️🖤
[3/24, 5:02 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 48.

Da saurin ya karasa kusa da ita ganin yadda ta rike kan, Hajiya Halira ta mike tsaye tana fadin

“Bari na dauko miki ma fi muje asibiti”
Chapter 67 · 0% Book details