Sashe 50
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A lokacin na dauki Mai Martaba kamar wani makiyina ganin Mahaifiyata ta zabeshi ta bar Mahaifiya bayan kuma shima yana sonta, a lokacin da na fara girma ina zama matashiya Zain na tasowa bama samun jutuwa ko kadan, yadda kika san kare da mussa haka muka taso, idan yaje gidanmu na dakeshi, idan naje gidansu ma sai na dakeshi, hakan yasa tun ina karama bama samun jutuwa da Dada, domin idan na buge mata jika sai ta bugeni ita kuma mahaifiyata sai ta shigarmin. A haka dai wata rana Mahaifiyarmu ta tsareni tai ta min fada ta nuna min nice Babba kuma wata rana ni zai rike Zain, ina karama a lokacin amman sai Allah yasa min natsuwa da hankalin daukar maganar, daga lokacin ban sake fada da Zain ba ko da kuwa shine ya ja ni. Ba ta dade da yi mana wannan fadan ba, rashin lafiyar kwana biyu ta kamata ta sai ta tafi ta barmu.
A wannan Ranar mun sha kuka ni da Zain, sai Dada ta dakeshi ta maida shi dakinta tana kula da shi, Mai Martaba kuma ya dauki son duniya ya dora masa, hakan ne yaja masa kiyayyah a gurin Hajiya Maryam tana ganin kamar ita ba a son yayanta kamar yadda ake son Zain. Shekara daya da rasuwar Mahifiyata sai iyayen Hameeda suka rasu, sanadiyar hadarin mota da suka a tare ciki har da Babban dansu Haleema ce kawai ta tsira ita da Hameeda a lokacin suna kamana amman Haleema ita ce babba, a tsakanin Ibrahim da Adamu wato Mai Martaba da Mahaifin Hameeda akwai shakuwa da soyayya da har ta wuce ta yan'uwan juna, suka zama kamar abu daya, rasuwarsa ce tasa ya dauko Hameeda a lokacin tana karama domin kawai ya rika ganinta tana rage masa kewa, Hameela kuma wata kanwar Mahifiyarta ta dauke ta tafi da ita bauchi, sai Dada ta karbe ta ta ajeta a dakinta sai ya zama Hameeda da Zain da Dada Yalwa, a kwana daya suke cin abinci, a tare da suke fita komai zasu yi a tare da Dada suke yi.
A tsakanin yan Hajiya Maryam da Zain basa samun jutuwa, ga Zain Allah ya saka masa son yan'uwa da kuma yara kanana tun yana yaro, hakan yasa shakuwa da soyayya ta shiga tsakanin Zain da Hameeda, a lokacin Zain Humee yake kira Hameeda, a tare suke zuwa makaranta duk kuwa da kasancewar ba ajinsu daya ba, idan aka taba Hameeda sai inda karfin Zain ya kare, idan zai siyowa kowa abu to na Hameeda zai fi na kowa yawa. A lokacin nai aurena na farin, every week sai Zain da Hameeda sunje inda nake, a lokacin Zain yana University, Hameeda kuma tana Secondary school, ni kuma na gama NCE sai nai aure.
Ana daf da nada Mai Martaba a sarauta ya auro Hajiya Zarah, a lokacin tana da yara uku da wani mijin, sai suka taru ita da Hajiya Maryam suka dorawa Zain kiyayya, hakan yasa Mai Martaba ya sakesu gaba daya, saboda baya son abunda zai taba masa yaro, ya auro Hajiya Hadiza, Hajiya Hadiza macece mai kirki da sanin ya kamata ta rike Zain kamar dan cikinta,m ta yadda har baka iya banbanta shi da yaranta wandanda ta zo da su gidan da kuma wandanda ta haifa a gidan, Bayan nada Mai Martaba a matsayin Sarkin Rishim sai ya dawo da matansa guda biyu daya saka,wato Hajiya Maryam da Hajiya Zarah, a maimakon su daina nuna masa kiyayyar sai suka koma a boye suna nuna masa kiyayyar. Suka shiga tsakaninsa da mahaifinsa da kuma Dada, wata rana Lahadi da rana tsaka Zain ya zo gidana ransa a mace, wai Mai Martaba ya koreshi kuma ya karbe komai nasa, shi kuma Zain be san abunda yai masa ba, Dada kuma ta kasa cewa komai. Muna da dangin uwa, Zain kuma yana da dangin uba amman ya barsu ya zabi zuwa gurina ya fada min damuwarsa kuma ya nemi zama tateyda ni. A gidan da nake aure Babban gida ne, dan haka na ware masa daki daya a cikin dakunan da suke waje. A dakin ya tare a nan yake komai nasa idan zai je makaranta sai ya zo na bashi kudi ko da yana da bukatar wani abun. Daman can Zain ba mutane mai yawan abokaiba, abokinsa daya ne Ibrahim wanda suka taso tare a makarantar jami'a, Ibrahim dan asalin jihar gobe ne, karatu ya kawo shi a makarantar har ya hadu da Zain.
A inda yake zama a lokacin shi ma kamar a labe yake, domin wani dan karamin shago ne yake kwana, idan yai kwadagonsa sai ya zo su raba kudin da Zain, domin Zain baya iya aikin wahala a lokacin. A wannan lokacin ne Hajiya Maryam tasa aka dauki yayanta mata aka turasu waje karatu.
Tun daga ranar da Zain ya dawo gidana, kullum sai mun fada da mai gidana, saboda yana ganin kamar ni kadai ya auro amman na kawo masa wani a gida yana ciyarda shi. Babu ranar da Hameeda bata zuwa gidan gurin Zain, wani lokacin daga makaranta take tserewa ta zo, wani lokacin kuma daga gida take zuwa, ko kuma ta same shi a makarantar, Hameeda ta siyar da duk wani abu data mallaka ta hada kudin tana yi ma Zain hidima, kamar an rufe bakin kowa babu wanda ya taba zuwa daga familyn Zain yace zai tambayi dalilin barin Zain gidan ko kuma ya shirya shi da Mai Martaba sai kowa ya saka mana ido, ni Hameeda Ibrahim muke dauke da nauyinsa.
Rashin jutuwar ta cigaba da shiga tsakanina da mijina na wacan lokacin har ta kai ya bani zabi akan aurena ko kuma dan'uwana, ni kuma na zabi dan'uwana, sai ya sakeni a lokacin ina da ciki na farko na tattara na dawo gidan mahaifina, bakinciki yasa cikin ya zube, a lokacin Zain ya samu wani gidan haya na siyarda kayan dakina na biya masa, ba dan mahaifina ba shi da kudin da zai bani nai masa hidima ba, sai dan bana son kowa ya san halin da dan'uwana yake ciki, kuma bana son dorawa kowa nauyin dan'uwana. Muna ta karatu da addu'a akan lamarinsa, a lokacin ne na koma makaranta domin aure ya fita kaina bayan na cika idda, a lokacin ne na gane amfanin karatu a rayuwar mace, ko ba komai zai taimaki rayuwata na san yancina kuma zai taimakamin na daina tambayar kowa taro ko sisi, mace bata zama sai dan dayan abubuwa biyu, karatu ko kuma sana'a.
Sannu sannu, abun ya fara karyewa, sai son da Mai Martaba yake ma Zain ya dawo sabo, ya aiko da kansa aka dauka masa Zain, ya maida shi cikin gidansa har ta kai ko daga nan zuwa can Zain bashi hali dagawa saboda Mai Martaba yana ganin kamar zai tafi ya barshi ne, a lokacin ne Mai Martaba ya fitar da Zain waje gurin karatun likita tare da Ibrahim, kamin ya dawo Mai Martaba ya gina masa private hospital mai sunansa, Zain ya fito kwararren likitan zuciya. kamin ya dawo kasar nan Hameeda duk ta shiga damuwa. A lokacin da Zain ya dawo sai ya fara sabuwar rayuwa mai cike da jindadi da walwala, ni kuma a lokacin nai aure na auri Abban Amal, ban haihu ba sai da nai digree na biyu, a shekara goma na haifi yara uku, I Aliyu, Muhammad da kuma Amal, bayan na haifi Amal na haifi Amal naje nai digree na na uku na samu aiki da Human Rights, haka rayuwarmu take ta tafiya, Zain bashi da yar'uwa ko kuma na ce uwa sai ni, nima bana da abokin shawara kamarsa... ”
Anty Ummi ta kare tana share hawayen idonta fuskarta kuma dauke da murmushi. Farhat ta gyara zamanta.
“Amman Anty miyasa Zain be aureta ba?”
“A lokacin da Zain ya dawo kasar nan, akwati daya yai ma Hameeda ita kadai, Zain ya zo so Hameeda kamar ba gobe, sai dai ba so na soyayya ba, ita kuma ta so shi, ni kaina na dauka Zain son aure yake mata, hakan yasa wata rana da suka je gidana nake masa maganar tun da har ya gama karatu yana aiki ya kamata ya fito ai maganar aurensu sai yace min ba Hameeda yake so ba, shi sam bata cikin tsarin matan da yake so, a nan nai mamaki kuma na bashi shawarar ya rage shiga rayuwarta domin ita son aure take masa, daga lokacin sai ya fara canjawa yana ja da baya, a lokacin ne Dada Yalwa da ita Hameeda suke min kallon makiyiyarsu, suna ganin kamar ni na hana aurenta da Zain, ana haka kwatsan wata rana Haleema ta zo ganin gida ta ziyarci Fadar Mai Martaba gurin kanwarta, sai Zain ya ganta ya fara sonta, ita kuma tai na'am, suka kulla soyayyarsu gwanin sha'awa har ta kaisu ga aure, bayan sun yi aure Mai Martaba ya hada Hameeda da wani dan abokinsa, amman Hameeda ta ki zaman auren saboda tana son Zain, ta fito da ciki ta zubar da cikin, ta dawo gidan nan ta zauna tana ta hada Zain da matarsa, wani lokacin kuma da Dada ko Mai Martaba, sai ayi ma Haleema fada ita a bata gaskiya, ga kuma ciwon daya samu Haleema tun a darenta na farko wanda tun a lokacin Zain yake zargin Hameeda, domin babu asibitin da be nema mata magani ba ciki da wajen kasar nan amman ko ina sai ace lafiyarta kalau, amman idan ta tashu sai tai ta aman jini kamar zata mutu, sanadin hakan yasa ta wahala lokacin da take da ciki, Zain ne yai mata tiyata ya cire mata yaron cikinta, awa daya yaron ya koma ga Allah, kwana biyu ita ma koma ga Allah, Zain yana son matarsa sosai, ya kasa yafewa kansa yana ganin kamar shine silar mutuwarta saboda shi yayi mata tiyata, a lokacin Zain ya koma kamar mahaukaci ya shiga damuwa yana ganin kamar ba zai sake samun wata mata da zai so ta kamar Haleema ba.
Zain mutumen da baya son a raina shi, yana son a bashi girma, a lokacin da yake zaune da Haleema suna zaune kamar kawaye, a tare suke komai suna nunawa kansu soyayya da kulawa”
Anty Ummi ta kama hannun Farhat.