Sashe 83
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sun jidadi sosai lokacin da Anty Ummi da Dpo Auwal suke fada musu irin hukuncin da aka yankewa Hameeda, hakkin Farhat da suka bi ya faranta ran mahaifiyarta sosai. Daman sun samu labari tun ranar da aka yanke hukunci domin akwai yan'uwanta da suke can wadanda suke halararta zaman kotun. Sai a lokacin ne Anty Ummi ta fadawa Mahifiyarta dalilin kin auren Ya Bashir da tai da kuma dalilin mutuwar Anty Rukaiya, Inna ta yi kuka sosai tare da nadamar da bata da amfani, a dayan bangaren kuma tana ganin laifin Farhat na kin fada mata gaskiya tun farko.
Auwal dai tun sha biyu ya bar anka ya koma gida Anty Ummi kam sai da yamma lis ta dawo bayan sun yi mata dubin alheri na amfanin gona, da kuma fura da hoce abincin zamfara, sai kuma kuli da daddawa abubuwan da aka fi saffarasu a kauye...
*AFTER 15 YEARS.... @2020*
*Who's is already for their new life...?*
[4/5, 6:31 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *57*
*New life 2020*
Yan mata ne guda hudu dukansu suna sanye da doguwar riga iri daya, uku daga cikinsu su yi rolling kansu da jan mayafi wacce ta kara fito da kyau gown din kasancewarta shudiya. Dayar kuma ta dora mayafin a kafadarta dayan hannunta rike da jar jaka, idanuwanta kuma sanye da katon gilashi kanta ya sha daurin first lady. Kallo daya zaka musu ka san cewa yayan manyan mutane ne, kama daga tufafinsu yanayinsa da kuma fatar jikinsu da ke amsa amon naira ta ko wane bangare. Ko wace da kalar kashim turaren da take, ba zaka iya bambance wanne ya fi dadi ko tsada ba, uku daga cikin yan matan fafaren yayinda da dayar kuma ta ke black beauty. Iska ne ya fara kadawa da dan karfi sakamakon hadarin dake haduwa a sararin samaniya.
Lokaci daya suka dariya suka bushe da dariya su ukun, ban da dayar wacce ta saka hannayenta ta toshe kunnenta sakamakon cidar da aka soma yi, ta nufi mota da sauri ta bude front seat ta shiga ta zauna. Dariya suka ta mata har suka shiga motar sanin yadda take tsoron tsawa da cida.
“Ohhhhh to yanzu mun ciro kudi me ya kamata mu fara ci, dan gaskiya yunwa na ke ji”
Black beauty ta fada tana kallon yan'uwanta.
“Vanilla ice cream...”
Dayar ta fada sai dayar ta tari numfashinta.
“No girl coffee²”
“No Indomie”
Wannan karon wacce ke front seat din ce tai maganar tana kallon wani gurin daban fuskarta dauke da murmushin da ya karawa fuskarta annuri.
Beauty da ke driver side taja wani dogon tsaki.
“Dan rufe mana baki, ke kullun indomie”
Daya daga cikin wadanda suke zaune bayan ta leko kanta.
“Beauty don't mind her she's indomie generation”
Sai duk suka sa dariya har ita wacce tai maganar. Ta juyo ta kallesu.
“Ai kara ni indomie ce, ke coffee, pearl ice cream, dukanku babu wacce take cin abincin gidansu, amman ni ina cin abincin gidanmu”
Bauty ta kalleta.
“Please zip up your mouth Pretty, idan ana maganar mutane ki daina kwatantawa da kanki, and i mean people, ke ma din da kike cin abinci gidanku ai mun fiki abun arziki”
Wacce aka kira da Pretty ta kalleta.
“To be frank indai ba indomie za mu siya a yanzu ba, ba zan biku ba”
“Haba dai Pretty shikenan sai muje mu zauna a restaurant mu ci indomie?”
Pearl ta fada.
“Fine kuje ku ci abunda kuke so, ni daman gida na ke son zuwa saboda hadarin nan”
Dayar da bata cika magana ba tunda suka fara magabar bata cika saka bakinta ba ta bude motar ta zagaya inda Pretty take zaune ta bude motar.
“Fito malama ba dole”
Ta kallesu da dai daya.
“Are you guys for real?”
Beauty ta daga mata kafadu. Pretty fita tai a motar tana kaiwa diamond duka cikin wasa.
“And lemme remind you something, Abuja ba kamar Kaduna ba ne, kamin ki samu abun hawa a nan zaki sha wahala, sai idan kira za ki yi a zo a dauke ki”
Beauty ta fada tana yi ma motar key.
“Mind your business Malama tun ba a haifeki ba na san Abuja”
Sai suka saka mata dariya, ita kuma ta nufi gurin titi. Wata farar motace ta sha gabanta wanda ke cikin motar ya sauke gilashin motar ya dan leko yana kallonta fuskarsa da murmushi.
“Pretty ke ce haka”
Fadada fuskarta tai da murmushin da ya fitar da dimple dinta dake gefen kumatunta.
“MB”
Ta fada kamar mai jin kunya.
“To miye abun jin kunya ai na san ba laifinki ba ne laifin kawayenki ne, ina zaki je haka gari duk hadari”
“Wallahi gida zanje, wannan Beauty din ce ta ce mu rakota Atm ta cire kudi kuma wai yanzu take min wulakanci wai na cika cin indomie... Imaging”
“Gaskiya ta fada Pretty kin cika cin indomie ai”
“Au kai ma haka zaka fada?”
“Am sorry Friend, shigo na rage miki hanya”
“Ai ban ce maka ta min tsawo ba”
“Zan kaiki ki ci indomie”
“Hubby ba zai ji dadi na ci abinci public ba, amman zan yi farinciki idan ka sauki ni gida”
Ya dan tsaya kallonta for a seconds sannan ya mika hannu ya bude mota motar.
“As you wish”
Sai da ta shiga motar ta zauna sannan ta rufe ta maida hankalinta gurin titi. A hankali ya soma driving kamar baya son su isa da wuri.
“Na fadawa Madam yau zaki zo ganin Babynmu”
“Wallahi teams suka ki raka ni, amman gobe zanje ko da ni kadaice”
“Da dai yafi, Allah ya kaimu”
“Amin”
Bata sake cewa komai ba, shi ma be sake yi mata magana ba, sai dai yana daga kansa lokaci zuwa lokaci ya kalleta. Ko da yai horn a bakin gate din gidansu har an fara yayyafi mai karfi, da gudu mai gadi ya bude masa gate. A harabar gidan ya faka motarsa ya juyo ya kalleta
“Ke zaki zo ko zuwa zan yi na dauke ki”
“Aa ni zan zo da kaina ai na san gida”
“Okay”
Ta kai hannu ta bude motar ta fita da sauri zuwa main door. Shi kuma yai ribas ya juya da motar ya bar gidan.
Sai da ta kai gaban balcony da ke gurin sannan ta daina gudun tana tafiya a hankali, hannu ta kai zata bude main door din hakan yayi daidai da bude kofar falon da Raheem yai ya fito yana kallonta.
“Waya saukeki yanzu?”
Ya tambaya tare da janyo kofar ya rufe.
“MB ne”
Ta fada kai tsaye.
“Ban ce kar na sake ganinki da shi ba?”
Har ta bude baki za ta yi magana sai ga Hajiya Asma'u ta bude kofar falon tana kallonsu.
“Fada kuke yi?”
Sai da ta kalleshi sannan ta kalleta.
“Aa”
Sai ta ratsa gefenta ta wuce ciki. Hakan ya bawa Hajiya damar dakowa ta fito tana kallon dan ta.
“Lafiya dai Raheem?”
“Hajiya MB ne ya kawo ta fa”
“Haba Raheem take it easy mana”
Tana fadar hakan ta juya ta koma cikin falon, shi kuma ya zauna a daya daga cikin kujerun da ke jere kusa da kofar shiga falon. Cikin bacin rai ta shiga dakinta, dakin da aka kawata da komai na cikinsa pink. Gurin da take rataye jakunkuna ta nufa ta rayata jakar tare da dora wayarta saman madubi sannan ta cire tufafin jikinta ta daura tawul ta shiga bathroom. Gaban madubin da ke bandakin taje ta tsaya tana kallon kanta for a seconds sai ga hawaye ya sauko mata.
“I can't tolerate this”
Ta furta sannan tasa hannuta ta share hawayen ta cire tawul din ta kunna shower. Bata fi minti goma ba ta fito, bata damu ta shafa komai ba, ta nufi wardrobe ta dauko gown ta saka, har ta nufi kofar fita sai kuma ta tsaya tana kallon kanta, no ba zata iya fita da wannan kayan ba ya matse ta, dawowa tai ta dauki Hijab ta saka.
“Hubby ba zai jidadi ba idan ina barin jikina sake”
Ta fada tana kara gyara zaman hijab din a jikinta. Gaban madubi taje tana kallon kanta.
“Da Hijabin ma kin fi kyau Pretty”
Ta fadawa kansa tana mitsisika ido, sannan ta juyo ya nufo kofar fita.
Tun ta fito daga dakinta ya daga kai yana kallonta har ta karasa cikin falon inda suke sannan ya dauke idonsa daga barin kallonta. As usual a kasa ta zauna dan ta fi jindadin zaman kasa fiye da zama saman Cushion.
“Tashi kije ki ci abincin ki”
“Me aka girka?”
“Tuwo”
“Tuwo? Indomie na ke so”
Ta fada tana yamutsa fuska.
“Ai gaki ga hanyar kitchen”
Cewar Hajiya, sai ta mike tsaye tana dariya.
“Macen da bata da ra'ayin kanta sai na wani tana cikin damuwa, ki koyawa kanki cin abunda ba abincin ki ba saboda wani selfish interest na ki ga wanda be san kina yi ba”
Yanayin yadda yai maganar sam ba zaka ce shi ne ba, dan babu wata alama wacce ta nuna cewar shi yai magana ban ma aikin lasar wayarsa babu abunda yake. Juyowa tai ta kalli Hajiya sannan ta kalleshi.
“Ina Mamakin mutumen da zai yi ta damuwa fa abunda be kamata ya dame shi ba, sai yaushe zaka fahimce kwakwalwata ta kasa haddace shiriritar da kake ta min mita a kunne? Miyasa ba zaka damu da abunda ya kamata ya dame ka ba?”
Shi take fadawa maganar amman ita ke hawaye. Dagowa yai ya kalleta
“Kin gani ko? Ba dama ayi magana sai ta ce da ita ake”
“Da ni kake mana na san ai da ni kake, ba sai ka fada min ba”
Ta fada da muryar kuka.
“Amman Hafsat ai ya kamata ki bashi girman shi ko ba komai ya girme ki”
Hajiya ta fada, sai Pretty ta nuna kanta ta nuna shi sai kuma ta kasa magana sai sakin baki da tai tana yi ma Hajiya kallon Mamaki. Sai kuma ta fashe da kuka ta nufi dakinta da sauri har tana hadewa da dan gudu. Sai da shige dakinta sannan Hajiya ta kalli Raheem.
“Takurawar da kake mata Raheem ta yi yawa, ya kamata ka saka mata ido hakan nan yanzu kam”
Kwantawa yai jikin kujerar da yake zaune ya lumshe ido yana sauke numfashi a hankali.