← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 93

Sashe 49

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

“Na san yadda kake ji Zain, but remember Allah ya baka Haleema a lokacin da kake sonta kuma kuke kaunar junanku, daya tashi dauke abarsa sai ya dauke ta ka isa ka hana faruwar haka? Yanzu kuma shi ya kaddara maka auren Farhat, da Hameeda Allah ya kaddara maka aure ya zaka yi da ita? Ita kanta Farhat din ba kai take so ba, amman Allah ya hada ku baka tunanin imaninka Allah yake gwadawa? Look at you cikin kankan lokaci Allah kawo Yarinyar nan ya gata karamar yarinya wacce zaka san inda ta fito ba, baka san iyayent ba, amman ya saka maka sonta, lokaci daya kuma wani abun ya shiga tsakani ya nisanta ka da ita, baka tunanin duk wannan yana rubuce a cikin kaddararka? Idan kai hakuri ka kawarda idonka kasan iya sakamakon da Allah zai maka a cikin lamarin nan? Trust me Zain zaka samu kwanciyar hankali a can, kuma zaka samu fahimtar matarka zaku nisanta da Hameeda saka samu damar nemawa matarka lafiya”

Dafe kansa yai yana jin kamar ba zai iya ba, yasan Ibrahim yana da gaskiya, shi kanshi yana jin komai na duniyar nan ya isheshi ba shi tabbacin idan ya bar kasar zai samu kwanciyar hankali amman yana da tabbacin idan yai hakuri zama da Farhat Allah zai masa sakamako da wani abun, and yes idan ya bar kasar nan dole Hameeda ta shafa masa lafiya ita da Dada, amman anya Mai Martaba zai amince yai nisa da shi mutumen daya ki yarda ya barsa ya zauna wani gurin sai cikin masarauta zai yarda ya barshi yaje wata kasar ya dade...?

“Kuje mana ko five years kui a waje, I promise you zaka dawo ka tararda farinciki”

“Mai Martaba ba zai yarda nai nisa da shi ba”

“Ba kai tsaye zaka nuna masa kana son tafiyar ba, ka nuna masa honeymoon zaku je, daga can zaka binciki matsalar lafiyar matarka, daga nan sai kai ta zamanka, idan har ya matsa maka sai ka rika zuwa kana dubashi har zuwa lokacin da zaka samu natsuwa da kwanciyar hankali sannan ka dawo, i promise you i will surprise you”

Ya shi tsaye cikin rashin jindadi.

“Zan yi tunani akai”

Tare suka fito da Ibrahim yana ta jaddada masa irin alfanun dake tattare da barinsa kasar nan, da kuma irin illar da zamansa a nan zai masa.

Bayan ta gama breakfast ta koma cikin dakinta tai wanka ta shirya cikin farar atamfa mai shudin ja, ba laifi ta yi kyau duk da kasancewar ba tai kwaliya ba, ta yi mamaki kuma taji dadin da kafafunta a yau ba su yi ciwo ba. Rike da mayafinta ta fito a falo ta tsaya ta sanya mayafin sannan ta nufi part din Dada, sai da tai sallama sannan ta shiga falon, Dada na hakimce saman kujera ta kasa daga kai ta kalleta har ta karaso inda take zaune ta kai kasa tana mata ina kwana.

“Lafiya”

Ta amsa mata kamar wacce bata son magana, sannan ta dago tana mata wani kallon wulakanci. Har ga Allah Farhat ta ji babu dadi, ba tsararta ba ce balle ta ce zata rama abunda tai mata kuma ta san duk wulakancin da Dada da Hameeda suke mata suna mata ne saboda ita din ba kowa ba ce. Cikin rashin kuzari ta taso ta fito daga falon, ko da ta dawo part dinta hawaye ya cika mata ido.

“Ba dai hawaye nake gani a idonki ba”

Kamar daga sama taji maganar, sai tai saurin kallon kujerar Anty Ummi ce zaune fuskarta dauke da murmushin. Tayi saurin fadawa jikinta.

“Laaa Anty yaushe kika shigo?”

“Yanzu nan na shigo, naga kofar falon ma a bude kika barta, fada min me kika ma kuka?”

“Ba komai, ya jikinki?”

“Ke zan tambaya ya jiki ai daman ke na zo na gani saboda shekaranjiya na san baki da lafiya, amman yanzu fara fada min dalilin wannan hawayen na ki”

Zaunawa yai saman kujera kusa da Anty Ummi ta maida dubansa gurin center carpet fuskarta abar tausayi ta ce

“Anty ban san abunda yasa Dada da Hameeda basa so na ba, dukan abunda zan yi ba zan taba burgesu ba”

Anty Ummi ta dafata tana murmushi.

“Har a bada Dada da Hameeda ba zasu taba so naba balle ke su so ki”

Ta dago ta kalli Anty Ummi.

“Amman miyasa”

“Je ki kawo min ruwa na sha”

Tashi tayi tana dariya ta je ta dauko ruwan da kofi ta nufo inda Anty Ummi take.

“Anty Amman naga kamar Zain ma baya samun jutuwa da Hameeda”

Sai da Anty Ummi ta karbi ruwan ta sha sannan ta ce.

“Ina mijinki?”

“Baya nan ya fita tun dazu”

“Je ki tura kofar falon ki dawo”

Ba musu taje ta tura kofar falon ta saka mata keys sannan ta dawo ta zauna kusa da Anty Ummi.

“Kuma Anty ita wannan Hameedar ba yar nan gidan ba ce ko?”

“Juri'ar gidan nan ce. Mahaifin Zain da mahaifin Hameeda uwarsu daya ubansu daya, mahaifin Zain wato Mai Martaba shine babba, Hajiya Hafsat mahaifiyarsu ita ce uwargidan Mai Martaba, a lokacin ba a bashi sarauta ba, Allah ya jarrabi mahaifiyarmu da wabi, idan tana haihuwar yaya suna mutu wasu su kan tasa wasu kuma tun kuna kanana suke rasuwa, wannan dalilin yasa ya auro Hajiya Maryam tana zuwa ta fara haifa masa yaya mata, bakin kishi da kiyayya irinta ta Hajiya Maryam ya hana mahaifiyarmu zama a gidan Mai Martaba duk kuwa da irin son da take masa, a lokacin da Mai Martaba ya saketa sai taje ya auri Mahaifina wato Alhaji Salisu, ko da ta auri mahaifina yana mata biyu ita ce ta uku, Hajiya Binta ce uwargidansa tana da yaro daya a lokacin, sai kuma Hajiya Mariya, ita tana da yara hudu a wancan lokacin, Alhaji Habib shine babba a gidanmu, bayan auren mahaifiyarmu da wata shida Hajiya Binta ta fita gidan mahaifinmu ta koma garinsu Kaduna da zama ita da danta, wanda a yanzu haka a can take rayuwa ita da zuri'arta, Mahaifiyarmu bata shekara a gidan ba sai da ta haife ni, ina da shekara shida mahaifiya ta rika unkurin barin gidan mahaifinmu, iyakancin kulawa da kauna Mahaifina yana mata amman hankalinta yana gidan tsohon mijinta saboda shi take so, ba dan komai yafi mahaifinmu komai ba, domin a lokacin ba a bashi sarauta ba, a haka ta kashe aurenta ta koma gidan tsohon mijinta wato mahaifin Zain Alhaji Ibrahim Tukur dan maliki, Sarkin Rishim na yanzu.
Mahaifina ba bari an tafi da ni ba, duk kuwa da kasancewar Mahaifiyarmu taso taje da ni a matsayin agola amman Mahaifina ya hana, a hannu Hajiya Mariya na zaune, ita ta rike ni kamar mahaifiya, wani lokacin tana kan hana yayanta abu ni ta bani, ta nuna min so da kulawa sosai wanda nake ganin ko da mahaifiyata a tare da ni iyakar abunda zata min kenan.
Bayan Mahaifiyarmu ta koma a gidan Mai Martaba da shekara biyu sai Allah ya bata ciki ta haifi Muhammad Zainudden, ita kadai mace data haifawa Mai Martaba dana namiji, ta samu kulawa da soyayya a gurin Mai Martaba da Dada fiye da tunanin mai tunani, bayan Haihuwar Zain ne mahaifina yake bari na zo nan gidan idan mun samu hutu ko kuma idan ana wani abun.
Chapter 49 · 0% Book details