Sashe 65
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin mahaukaci Faki Zain yai a lokacin da ya iso gurin, ya fito cike da tashin hankali ya tura kofar falon ya shigo, jini kawai ya tarar domin tuni an wuce da Farhat zuwa asibiti, kukan Hafsatu manga da yaji ne yasa shi kallon inda take labe tana lekensa. Kai ta girgiza masa.
“Ba... Ba... Ba... Ba ni... Ni ba ce”
Ta hannu yai mata alama da ta zo sai ta taso da gudu da nufo inda yake, kamin ta karaso police suka shigo falo Dada Yalwa na biye da su a baya, tare da wasu mayan dogaran Sarki. Juya tai da gudu ta koma gurin ta labe ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
“Gata can ja'izar yarinya Annoba”
Dada ta nunawa police din ita. Sai ya mike tsaye da idanuwansa da suka kada suka yi ja ya kallo police din ya ce
“Ba ita ba ce karku taba”
“Ka yi hakuri ranka ya dade babu abunda zai hanamu aikinmu”
Biyu daga cikin police din suka nufi inda take suka daukota tana wani irin ihu kamar za'a cire mata rai. Zain rigansu fita yai ya koma cikin motar ya fisgeta kamar zai tashi sama, asibitinsa ya nufa dan yasan can za a kaita domin can ake kai familynsu idan basu da lafiya, ko parking din kirkir be yi ba ya fita ya shiga cikin asibiti tafiyar ce tai masa nisa har sai da ya hada da dan gudu ko da ya isa, Hajiya Hadiza da Hajiya Zarah da wasu kanensa suna tsaye bakin emergency room.
“Tana da rai?”
Ya tambaya tun kan ya karasa kusa da su, gabansa dai dukam uku uku yake.
“Bamu sani ba, suna ciki suna dubata”
Hajiya Hadiza ta amsa masa tana share kwalla dake mata zuba, har ya nufi gurin ya shiga sai kuma ya tsaka cak ya dafw kansa ya runtse ido, juyawa yai ya fice daga gurin gaba daya, gurin motarsa ya koma sai kuma ya rasa abunda zai yi, jinginawa yai jikin motar ya rumtse idon, zuwa can kuma ya bude ya ciro wayarsa dake aljihu ya kira Dcp, Dcp na picking Zain ya ce
“Ka aiko min da yaranka biyu yanzu nan, masarautar mu an yi kisan kai”
“Subhanallahi wa...”
Be karasa tambayar ba, Zain ya kashe wayar ya bude motarsa ya shiga ya dauki hanyar fada. Ya riga su isa a cikin motar ya zauna har sai da suka iso, sannan ya fita daga motar yai musu magana suka rufa masa baya kasancewar shine a gaba, part din da su Hameeda suke ya nufa yana taba kofar dakin ya ji ta a rufe sai yai knocked, shiru bata bude ba, juyowa yai da su suka nufo part din Dada, yadda kasan an aikoshi haka ya banki kofar dakin ya shiga, tana falo zaune ita Dada Yalwa da alama maganar ce suke tattaunawa. Tana ganin Zain din da police sai ta mike tsaye da sauri tana kallonsa.
“Ga nan”
Ya nuna musu ita, sai tai baya baya idonta na cika da hawaye.
“Mi nai?”
“Ana zarginki da kisan kai”
Dan sandan dake kokarin rika hannunta ya saka mata handcuffs ya fada mata, sai Dada ta saka salati tana tashi tsaye.
“La'ilaha'illallah, Zain ko ka haukace ne, ga yarinyar da kanzo da ita jiya ita tai aika aikar fa, zaka lakawa Hameeda kamar wanda baya gani”
“Idan ma da ke ta hada baki ake kokarin kashe min mata, zan ba ku mamaki, idan kuma yin kanta ne a karan kanta zata fuskanci hukunci”
Ya furtawa Dada cikin bacin rai sannan ya kalli police din ya ce
“Ku wuce da ita”
Suna janta ta fara ihu tana kiran sunan Dada Yalwa.
“Dada za su tafi da ni, wayyo Allah na Dada ko taimakeni....”
Wani irin kuka take tana kiran Dada, gani take kamar idan sun tafi fa ita gidan prison za a kaita kai tsaye. Ihunta ne ya dago hankali duk wanda ke kusa da part din Dada kowa ya fito yana kallon ikon Allah, dan kowa mamakin ganin an kama Hameeda ya ke, Ikram ce tai saurin zuwa kusa da Zain tana fadin.
“Yarima ba fa ita ta aikata ta....”
Bata karasa ba ya wanke mata fuska da mari har sai da yai baya kamar za ta fadi. A bayan motar yan sanda aka saka ta tana ta kuka hannunta sanye da handcuffs.
Kuka sosai Dada take cikin rashin karfi irin ana dattawa tsofi ta fita ta nufi part din Mai Martaba.
Tsaye Zain yai a harabar gurin yana kallonta har sai da aka wuce da ita sannan ya nufi motarsa ya shiga gabansa na mugun faduwa. Asibiti ya koma wannan karon da yai parking kasa fita yai daga motar sai hawaye ke sauko masa daya bayan daya, wani dogon numfashi yaja ya sauke ya jingina kansa ga sitarin motar.....
Ku yi manage please bana gida ne, rabin page ne gobe zan yi two page karashin cikon da kuma ma goben inshallah.
[3/22, 11:51 AM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: 46b
Yafi karfi awa daya a cikin motar wayarsa sai ringing take amman ya kasa daga kansa ma daga sitarin balle har ya duba mai kiran wayar, wani iri yake jin kansa abubuwa mabanbanta yake tunani. Kama Hafsatu manga da kuma Farhat, Farhat din ce ta fi tsaya masa a rai rayuwarta da mutuwarta yake tunani. Knocked glass din motar akai hakan yasa shi dago kansa ya kalli Ibrahim sai ya kai hannu a zoke gilashin motar yana kallonsa da idanuwansa suka kade suka yi ja sosai.
“Ya kamata ka kira iyayenta ka sanar musu”
Sai ya dauke kansa daga barin kallon Ibrahim sannan ya ce
“Ta musu ne?”
Ibrahim be amsa masa ba, sai kawai ya ce
“Bari na kira Anty Ummi”
Wayarsa ya ciro ya nemi number Anty Ummi ya aika mata kira, tana picking ya fada mata abunda ya faru kuma ya sanar mata suna asibiti, Zain ya kasa kunne sosai yana son yaji ko zai fada mata tana raye ko mace amman ya be ji ya fadi ba. Har ya kai hannu ya bude motar ya fito, sai kuma yaji ba zai iya ba, jikinsa y mutu sosai ko lokacin da Haleema za ta rasu be ji irin wannan abun ba, be san takaimaiman abunda yake ji ba a yanzu, iyakar abunda ya sani akwai tsoro da fargaba a tare da shi, tsoron kar yaje ya ga gawar Farhat, fargabar kar ya ganta cikin mawuyacin halin da take ciki, taya raye ko a mace, bashi da amsar wannan tambayar a yanzu.
Cikin rashin kuzuri ya kai hannu a karo na biyu ya bude motar ya fito ya nufi hanyar office din, domin baya son zuwa emergency din kar yaga Farhat. Cikin office dinsa ya shiga ya zauna ya dora hannayensa saman tebur din ya dafe kansa, haka kawai hawaye ke masa zuba, rabon da ya zubar da hawaye haka har ya manta. Shigowar Ibrahim ne yasa yai saurin tashi daga saman kujera ya nufi gurin windows ya tsaya dan bayan son Ibrahim din ya ga hawayensa. Cike da tausayinsa Ibrahim ya karasa inda yake tsaye ya kai hannu ya dafa kafadarsa.
“I'm sorry Zain, she can't survive ita ma ka rasa ta...”
Ibrahim ya fada yana kuka. Kamar daga sama Zain ya ji maganar, sai da numfashinsa yai nisan zango na yan seconds sannan ya dawo jikinsa. Wasu hawaye ne masu mugun za fi suka zubo masa, juyowa yai yana ture hannun Ibrahim dake kafadarsa.
“Mata nawa zan rasa ne? Mace nawa zan aura su mutu? Miyasa bakinciki mutuwa yake ta daummawa a rayuwata ne? Ko yaushe sabon babi ake bude min, ko yaushe sabon tabon mutuwa na ke samu a zuciyarta....”
Ya fada yana fashewa da kuka. Sai kuma ya dafe kansa yana fadin.
“Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un”
Ibrahim yayi saurin rikeshi, kamar an zame kafafunsa daga kasa haka ya tafi rifff ya fadi jiri na dibansa, ba suma yai ba sai dai har yanzu dakin juya masa yake hakan yasa shi saurin rumtse idonsa. Sai Ibrahim ya sake shi da sauri zai nufi kofa Zain ya kira shi.
“Karka kira kowa, bana bukatar a amin komai”
Cikin karfi hali ya tashi tsaye ya share hawayen idonsa ya nufi kofar fita tare da Ibrahim, Emergency din ya nufa har yanzu Hajiya Hadiza da kanensa biyu suna tsaye a gurin suna aikin kuka, a bakin kofar dakin Ibrahim ya tsaya, Zain kan kai tsaye ya tura kofar dakin da take ya shiga. Har gurin gadonta ya karasa an rufeta da farin zane tun daga kanta har zuwa kafafunta. Hannu ya kai ya yaye zanen yana ta kallon fuskarta gata wance kamar yai mata magana ta amsa amman idonta a lumshe, risinawa yai ya sumbanci goshinta sai ya rika hannunta ya fashe da kuka. Yana haka Anty Ummi ta shigo jakar hannunta ta saki ta dora hannu saman kai tana hawaye.
“Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un”
Ta maimaita hakan yafi sau ashiri sannan ta fashe da kuka, kamar wacce ta tuna wani abu sai tai saurin share hawayenta ta nufi inda Zain yake risine yana aikin kuka ta janye hannunsa daga na Farhat ta rufe ta dafa kafadunsa tana fadin
“Ka yarda da kaddara Zain, haka Allah ya rubuta maka kuka ba zai dawo da ita ba, kuma ba kuke abunda take bukata a yanzu ba”
Hakuri take bashi amman ita ma hawayen take. Mikewa yai tsaye sai ya juya ya fice daga, karaso tai ta dauki jakarta ta fito tana share hawayenta.
“Ina Hafsatu manga take?”
Abunda ta tambaya kenan daga fitowarta daga cikin dakin. Hajiya Hadiza ta ce
“Ban sani ba ni dai ko da na fito gida mun baro Dada tana fadin a kira police su tafi da ita”
Anty Ummi ta kalli Ibrahim.
“Ibrahim a aje mana gawar Farhat, kar a bar kowa ya taba ba, kuma kar a fita da ita, na fadawa yan'uwanta suna nan zuwa, su kadai na yarda su dubata, kar ka bari a fita da ita, wukar tana gurinku ko gida?”
“Tana nan”
“Aje min ita please”