← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 93

Sashe 52

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wane Isma'il?”

“Doc Isma'il, na asibitin ka likitan yara”

Ibrahim da Zain sun kalli juna Zain ya ce

“Ya aka yi ya sani?”

“Lokacin da kake kwana asibiti ne, ya zo yana tambaya wai yaji labarin ka daina kwana gida saboda aiki ya maka yawa a asibiti, shine nace wata kake jinya, shine ya dinga bugun cikina yana ta tambaya a akan yarinyar, har zamanta gidanmu sai ya zo da wata mata itama tana ta bincike akan yarinyar”

Tunda take maganar tana murza yatsun hannunta.

“Wace mace kuma”

Wannan karon Ibrahim yayi mata tambayar.

“Sunanta Hameeda tace ita kanwarka ce, wai baka son kowa yaji maganar amman kace mata kana ajiyar yarinya a gidanmu ta zo ta ganta, daga baya kuma tace min karna fada maka”

Zain ya zaburo kamar zai daketa sai Ibrahim yai saurin tashi ta tareshi.

“Miyasa baki fada min ba tutuni? wace irin banzar macece ke?”

“Ai na maka text daga baya”

Ta fada tana shirin yin kuka. Zain ya dafe kansa ya juya baya yana dora hannunsa daya a baya.

“that's it, daman nasan dole akwai wani abu a ciki”

Sai kuma ya juyo.

“Fada min Hameeda tana da alaka da Yayanki nan”

“Bata da”

Ta fada tana share hawayenta.

“Make sure you are telling me the truth”

Ya fada yana nunata da yatsa, idonsa na nuna tsananin bacin ransa har wani cizon baki yake.

[3/16, 9:51 PM] 😍🌹خديجة كاندي♥️🖤: *Karki karanta min novel idan baki biyaba, masu sharing Novel dina na barku da Allah. Idan kina son biya ki turo 300 ta 0314795884 Abubakar Hadiza Gt bank, sai ku turo da shaidar biyan ta wannan number 08036126660, ko kuma katin MTN na 300 ta wannan number 08036126660*

38.

Sai da yamma ta fito daga dakinta ta fito part Dada Yalwa. Bata falo dan hakata wuce dakinta zaune ta sameta saman carpet tana rike da carbi da alama sallah ta gama kusa da ita ta zauna, fuskarta gwanin tausayi Dada ta juyo ta kalleta.

“Yau duk baki shigo ba”

“Ina dakina bana jin fita ko'ina shiyasa”

“Baki da lafiya ne?”

“Lafiyata kalau, kawai dai...”

Sai kuma tai shiru ta sadda kai kasa, Dada ta kai hannu ta shafa kanta.

“Yi hakuri Hameeda komai zai wuce kinji?”

“Sai yaushe Dada? Sai yaushe? Ina ganin ina bata kaina lokaci ne kawai, na hakura zan zauna da kowane irin miji zan fitar da wani na aura”

“Aa wannan ma ai duk laifinki ne, sai da naso na hanashi auren nan amman kika ce a kyale shi, amman ko yanzu be sha ba nasan yadda zan bulla masa, tafiyar nan na ba zan bari ya yita ba, waya sani ko so yake ya gudu ya bar kasa”

Hameeda ta mata kallon rashin fahimta.

“Ina zai je?”

“Wai Paris gurin honeymoon shi da matarsa”

Rasss gabanta ya fadi, tashin hankalin da bata san daga ina ya fito ba a take ya sameta kamar wacce aka ce ma Zain ya mutu ya barta.

‘Honeymoon’

Ta maimaita a ranta tana kallon Dada, with so much confusion on her face, bata ankaro da inda take ba har sai da taji hannun Dada a fuskarta.

“Ki kwantar da hankalinki, ba zan barshi yaje ba, kuma kwanan zan tirsasa Mai Martaba ya aureki”

“Mai Martaba ba zai cilasta dansa ba Dada, yafi son dansa da kowa, da yana da niyar yin haka da ya aikata tuntuni”

“Ki saka idonki kiyi kallon komai zai zo miki a yadda baki yi tsammani ba”

‘Ko kuma shi ya zo masa a yadda be yi tsammani ba, idan har ban samu farinciki da Zain ba, wata mace bata cancanci samun farinciki da shi ba’

Ta fada a ranta, a fili kuma sai ta sake kallon Dada tai murmushi.

“Zan yi ta addu'a idan alheri ne Allah yayi, idan kuma ba alheri ba ne Allah ya kawo min mafita”

“Amin Allah yai miki albarka, karkisa komai a ranki, nasan yadda zan yi”

Ta gyada kai sannan ta tashi ta fito daga dakin cikin wani zafin rai da mamaki.

“Shikenan ya manta da ni kenan? Ya manta irin rayuwar da nake da burin mu yi, da gaske baya so a yanzu? Idan har ta tabba gaskiya Anty Ummi kina ciki matsala domin ke kika lalata komai, ke kika shiga tsakaninada Zain...”

Magana take a fili kamar ta manta da a cikin gidan take, wani zai iya jinta. Cikin hanzari ta koma dakinta ta banko kofar dakin da karfi

“Daga kai har Farhat har Wannan bakar Ummi baku cancanci zama ciki kwanciyar hankali ba, bani da sauran amfani idan har ban saka ku kun fahimci babu farinciki a rayuwarku idan babu a rayuwar Hameeda ba, wannan wasa yanzu zamu fara Zain, sai na baka mamakin wannan karon Zain, duk halin da na shiga Kai ne sila, saboda haka ya kamata ka dandani dacin rashina a rayuwarka, idan har ban ragawa yar'uwata ba, to be kamata na ragawa kowa ba, hakurina ya kare babu wani sauran jira a yanzu kam”

Wayarta ta dauko ya lalubo number kawarta Fauziya. Bugu daya ta daga tana zolayarta.

“Amaryar Zain, Uwargidan Sarki gobe”

“Uhmm Fauziya Zain honeymoon zaije da matarsa a Paris”

“What? Ke kuma kina me?”

“Nima, yanzu Dada take fada min”

“Kina da matsala Hameeda, ke kika yi saka har ya auri yarinyar nan yanzu kuma duk kika sa ke sake ya bar kasar nan da ita ko da zasu dawo da ciki zata dawo kinga ta samu gida kenan”

“Kema kin san babu yadda ban yin ba, amman komai yaki tafiya Zain shegen mutum ne Fauziya magani be kamashi, babu yadda ban yi ba amman be taba kamashi ba”

“Dole sai ta hanyar magani? Kina abu kamar ba yar boko ba?”

“Zan gwada wata hanyar, karki damu nima a yanzu ai be kamata na ragawa kowa ba, Farhat ba zata taba haihu da shi ba, ko ma ta haihu daga ita har shi ba zasu rayu ba, saboda Zain nawa ne ni kadai”

“Haka nake son ji yar gari, yar'uwarki ma bata raga miki ba, baki raga mata ba balle kuma wata banza can, idan kin gwada hanyoyi ba su yi ba, ya kamata mu canja wata hanyar”

“Zan shigo gidanku gobe insha-Allah. Ya kamata mu yi shawarar wasu abubuwan”

“Okay sai kin zo”

Daga haka ta aje wayar hannun, ta tashi ta bude bedside drawer ta dauko makulli ta ta bude wata karamar drawer ta dauko hotunan Haleema tana kallona, wani gurin sun yi tare wani gurin ita da Zain da Hameeda wani kuma ita da shi, dayan kuma ita kadai, hawayene ya fara sako mata.

“Da ace na san ba zan taba samun Zain a matsayin miji ba, da ban raba ki da shi ba na yi nadamar abunda na aikata, Zain ne silar komai ki yafe min Yayata”

Ta rumgume hotunan tana wani irin kuka mai ban tausayi.

ZAIN POV.

“She betrayed us, daman na fada maka ba zata iya aje mana sirrinmu ba, shiyasa tun farko ban yarda da ita ba, munafuka”

Anty Ummi da tunda aka fara abun bata saka baki ba, ta tashi tsaye tana dagawa Zain hannu.

“Yanzu dai ya isa, ba laifin kowa ba ne tun farko laifinka ne, babu yadda ban yi akan a sanar da police zaman yarinyar nan a gidan nan sai kan rika kareta akan tana jin tsoro, na san Mai Martaba ba zai taba hanaka ba idan ka dauketa ka shiga da ita Fada a matsayin yar gudun hijira amman kaki, sai kace yar da aka sato, wannan boye boyen da kake shi yaja har Hameeda ta samu damar yi maka haka”

Ibrahim ya kalli Hafsat dake kuka ya ce

“Hafsat tashi kije wajen mota ki jirani ina zuwa”

Tashi tai sunsun ta fice hawaye na mata zuba. Sannan Ibrahim ya kalli Zain

“Yanzu miye abun yi?”

Anty Ummi ta ce

“Ibrahim ina ganin be kamata mu shiga ciki ba, wannan tsakaninsu yan'uwan, dukan abunda Hameeda tai miki ko tai ma Mama saboda shi tai, be kamata mu shiga ciki ba”

Sai kuma ta kalli Zain

“Ya kamata ka san yadda zaka yi da ita, domin idan baka iya kama barawo ba sai barawo ya kama ka, karka je mata da wannan zafin ran, karka ce zaka mata da karfi domin wayonta ya girmi shekarunta, abu na biyu kuma kansan Mai Martaba be san da wannan maganar ba, sai kasan yadda zaka yi ta, ka kuma san yadda Dada bata son jin sunana a fadarku, dan haka kai taka tsantsan gudun karka sake saka rayuwar Mama a cikin matsala”

“And please kar sunan Hafsat ya fito a ciki, kar ta sake shiga wata matsalar”

Cewar Ibrahim, sai Zain yai masa wani kallo.

“Really? Ita ba rayuwar wata ta saka a ciki matsala ba? Idan ma na gama da Hameeda sai na yi da Yyanta Allah kadai yasan abunda suka hada baki suka mata”

Ibrahim ya kara matsowa kusa da shi.

“Yadda kasan yana jin yarinyar kauyen nan haka nake jin Hafsat, ya kamata ka san haka they are all women”

Yana gama fadar hakan ya juya ya fice daga falon zuciyarsa na mugun bugawa. He see no reason da Zain zai rika cin zarafin Hafsat akan abunda ko wane dan'adam be wuce aikata kuskure ba.
Wayarsa ya dauka yai nemo number Hameeda ya aika mata kira, yayi mamakin da wayar tai ringing har ga katse bata dauka ba, yasan bata cika nisa da wayarta ba, kuma indai shi ya kira tana saurin dauka. But this time around sai da ya jera mata kira biyar ana shida ta dauka.

“Hameeda kina ina?”

“Miyasa ka tambaya?”

“Ba amaida min tambaya da tambaya and you know me”

Ya fada yana wani abu da fuska kamar ance masa tana gabansa.

“Fada min inda kake na zo na sameka”

Ya katse wayar, sai ya aika mata da text. Anty Ummi ta kalleshi

“Ka tabbatar wannan hanyar zata bulle? Ina ganin kamar yafi dacewa ka bullo mata ta karkashin kasa, ina tsoron karta maka ZAGON KASA, yarinyar nan shu'uma ce”

“Ba zan iya wannan ba Anty, kara na fuskance ayi ta ta kare”

Yana gama fadar hakan ya maida wayar aljihu ya fice, Anty Ummi ta bishi da kallo.

*** *** ***
Chapter 52 · 0% Book details