← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 93

Sashe 68

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gurin ta zauna tana ta kuka saboda kanta da take jin kamar zai rabe gida biyu. A motar suka saka ta duk da irin nauyin zuciya da jiri dake diban Alhaji Habib be hana shi binsu zuwa asibitin ba, suna isa aka basu gado aka daura mata drip suka sa mata maganin a ciki nan da nan bachi yai gaba da ita, su Hajiya Halira da Maimunatu ne suka tsaya shi kuma ya juyo tare da direba ya nufi Family house din su Rufaida. Yana dosar gidan gabansa na faduwa, a harabar gidan direbansa yai parking, sannan ya fita ya nema masa uzini shiga cikin gidan, an fada masa Mai gidan baya nan amman jin shine yasa aka bashi izinin shiga. Da kansa ya bude motar ya fita a hankali yake takawa yana jin wani zafi da zuciyarsa ke masa numfashinsa na yin sama kamar zai fita. Dan Madaidacin falo ne ba a kawatashi sosai ba, amman an masa gyaran da babu wanda zai shigo ya raina gidan. Be yi zaman mintuna uku ba sai ga wata dattijiwar mace ta fito sanye da hijabi hannunta rike da sandar karfe ta dafawa a hankali dayan hannunta kuma rike da carbi, idonta na sanye da gilashi irin wannan na tsufi, mafara ce sosai kana ganinta ka ga ruwan fulani duk da kasancewar tana da jiki. Kallo daya zaka mata ka fahimci cewar mahaifiyar Rufaida ce domin babu abunda ta rage daga kammamin Rufaida.
Cikin girmamawa Alhaji Habib ya gaisheta, ta amsa mishi tare da daga masa hannu.

“Hajiya daman na zo ne akan maganar Rufaida”

Daga kai tai ta kalleshi sai ta kai hannu ta cire gilashin idonta sai ga hawaye ya cika idonta.

“Jiya duk a nan yan'uwanta suka taru suna kukan rashinta, shekaru kusan talati bata tare da mu amman babu wanda ya taba magana, kuma babu wanda ya taba nemanta, ashe tana cikin ran kowa furtawarne kawai ba a iya yi, kullum da ita nake kwana da ita na ke tashi, ban san hali da yata take ciki ba, ban san wace irin rayuwa take ba, tana a raye ko a mace ban sani ba”

“Nima kaina ban san abunda ya hanani nemanta ba, ni dai na san na dawo daga jumma'a na shigo gida sai na samu bata cikin gidan, ban tambaya ba sai kawai na saka aka rufe part din ba tare dana nemeta ba, amman Wallahi Hajiya kullum da ita nake kwana da ita na ke tashi, a gusau naje gaisheda mahaifina sai..... ”

Ya tsakura mata labarin Hafsatu manga wacce yake zargin yar Rufaida ce saboda awarwaron dake hannunta da kuma kammaninsu. Hajiya tasa hannu ta share hawayenta tana girgiza kai.

“Wata kila yarta ce, tun ko da ta bar gidan nan ta tsoho ciki ta tafi, cikin data kasa haifewa shekara hudu, wata kil ta rayu a can ne ta haifi yar ta mutu”

“Inshallah tana nan raye Hajiya, zan nemota a duk inda take, zan saka cigiya a gidajen redio nan da can kuma zan bada tsofin hotunanta da nake da su, zan kuma bincika gidanjen asibiti da mahaukata da yake can, saboda yarinyar tace mahaifiyarta mahaukaciyace”

“Sai dai a sa a can, nan kam yan'uwanta sun saka tun jiya, har gidanka sunje basu sameka ba, Allah ya bayyanata mu dai mun rike Innahu ala raja'ihi lakadrin indai tana nan raye zata dawo garemu da yardar Allah, ko da ko kasar nan ta bari. Duk abunda ya bata ka karanta ta sai ya dawo gareka da yardar Allah, (Amman ta batan mutum ana karantata sau 300k sai salatin annabi 11, bayan ko wace carbi 100k bayan magariba ake yinsa)”

“Nima zan cigaba da addu'a inshallah kuma zan yi duk abunda ya dace, gobe ma ke jin zan koma garin saboda na tabbatar, ina son a gwada jinina da na yarinyar dan tabbatarwa”

“Haka ma yayi Allah ya bayyanata, kuma zan fadawa yan'uwanta idan sun zo”

Daga haka yai mata sallama ya tashi ya fice.

Sai da sallah isha'i sannan Hajiya Safiya ta farka, har kuma lokacin ciwon kan be saketa ba har bata iya bude idonta sosai.

“Sannu...”

Hajiya Halira tace mata cike da tausayawa, hannu ta daga mata tana maida idonta ta rufe.

“Ina Alhaji...?”

“Tun da muka kawo ki ya koma, kin san shima hankalinsa bakwance yake ba, gashi lafiyarma bata isheshi ba”

“Be hakura ba ko neman Rufaida zai je?”

Ta tambaya a wahalce.

“Wallahi ban sani ba, amman dai ai kara ya nemeta duk da ina jin kamar bata raye”

“Indai har ya nemota, to ni ce cikin matsala Ya Halira”

Cike da tsananin mamaki Hajiya Halira ta ce

“Saboda da me, ke kam ai jindadinki ne domin ko ba komai mijinki zai samu lafiya”

“Samun lafiyarsa akan Rufaida ciwona ne, gashi tun yanzu na fara balle kuma idan ta dawo, asirina zai tonu sirrin dana shekara talatin ina rufewa zai tuno, haukar dake kanta kuma a kaina zata dawo indai har tana raye”

Hajiya Halira taja baya da kujerarta tana ma kanwarta kallon tsoro.

“Ban gane ba, kina nufin duk abunda ya faru da Rufaida laifinki ne?”

Ta hade yawu a wahalce sannan ta sake bude idon ta kalli yar'uwata hawaye na zubo mata.

“Ban taba fadawa kowa ba, babu wanda ya san wannan daga ni sai kawata sai kuma Allah, amman idan har aka dawo da ita ni ce zan haukace, domin haka bokan ya fada”

“Innalillahi Wa'inna ilaihiraji'un, amman Safiya baki kyautawa kanki ba, kuma wannan halin ba halinmu ba ne, kin cutartarda ita kin cuci iyayenta kin cuci mijinta me tai miki?”

“Bata min komai, ina tsoron kar sonta yasa Alhaji ya wulakantani ne, saboda na san wacan gidan da na fito hanani zama suka yi, ina ganin kamar idan ban yo haka ba, nan ma fita zan yi, kuma bana son aurena ya sake mutuwa, lura da irin son da Alhaji yke mata, ga son da Hajiyarsa take min ya koma kanta saboda ta samu ciki, sannan ina tsoron ta haifi Namiji, shiyasa nasa akai mata aiki aka danne ciki ta shekara hudu a gidan nan da shi, daga baya kuma nasa akai mata wanda zata bar gidan saboda ina kishin irin kulawar da Alhaji ke bata”

Hajiya Halira ta fashe da kuka.

“Haba Safiya, kin san irin mugun halin da kika saka baiwar Allah nan? Mace ko wata tara ta dauki ciki ya take ji balle shekara da shekaru, kila ma ta mutu baki sani ba, kin dauki hakkinta kin cutar da ita ba gwaira ba dalili, miye amfanin fada min wannan maganar ma? ”

“Naje daga baya na ce a warware aikin, amman kaddara ta riga fata, ban samu bokan da yai min aikin ba, sai dai ya fada min tun farko cewar duk ranar data dawo cikin gidan ni ce zan haukace, kuma ina jin kamar hakan na dap da faruwa, saboda ciwon kan nan da nake bana lafiya ba ne, kuma yan'uwanta sun zo nan jiya suna tambayarta ,alamune dake nuna cewar aikin na daf da karewa, tun da kika ga shi ma yana nemanta”

Hajiya Halira ta taba hannayenta tana salati.

“Lallai Safiya duniya ta rude kuma ta yaudareke, gashi kin jama kanki yanzu ina amfanin wannan abun?”

“Na dade ina jin nadamar abunda na aikata, sai dai ban san yadda zan yi ba, na rasa ta yadda zan tinkari Alhaji da wannan maganar, yanzu kam na san lokaci na ya kare ba zan iya hana shi neman matarsa ba”

“Karki kuskura ki fada masa wannan maganar, kar kuma ki bari kowa ya ji wannan maganar, ki zubama sarautar Allah ido kawai, kuma ki karbi sakamakon abunda zai zo miki”

“Amman yana da hakkin ya sani”

“Idan har ya sani ba zai taba zama da ke ba”

Hajiya Halira na rufe bakinta Alhaji na turo kofar dakin ya shigo, sai tai sauri share hawayenta tana amsa sallamarsa.

“Ya mai jiki?”

“Al-hamdulillah ya naka jikin”

“Al-hamdulillah, Hajiya kuka kike yi?”

Ya tambaya yana kallon Matarsa wato Hajiya Safiya wacce ke kallonsa tana hawaye, sai ya zauna bakin gadon kusa da ita cikin yanayin damuwa.

“Kan be daina ciwo ba?”

Hajiya Halira ta tashi ta fice daga dakin ta basu wuri. Rumtse ido Hajiya Safiya tai tana kokarin tsada kukan ta ce

“Ya daina, ya naka jikin?”

“Al-hamdulillah, na yi waya da twins na fada musu halin da kike ciki, gobe za su zo, da nima na so naje Gusau gobe amman saboda zuwansu zan hakura har jibi, ina son na kara bincikawa, yarinyar Ummi ke rikonta kamin shi yaron ya karbeta kuma ta fada min cewar wai yarinyar tana gidan yari ana zarginta da kisan kai”

Zabura tai ta tashi zaune.

“Wace Ummin?”

“Kanwata wacce Gusau Ummi dai wacce kika sani”

Tayi saurin rike kanta.

“Lafiya dai?”

Sai ta canja maganar dan kar ya gane halin da take ciki.

“Ai da baka fada musu ba, kar hankalinsu ya tashi”

“Hakkinsu ne su sani, nima ai nawa mahaifin na je zubawa har na ga wannan yarinyar ban samu na gaisa da su ba na dawo, kuma daman sun ji gurin Hajiya Halira dan Hassana ta fada min ta kira wayarki sai ta dauka ta fada musu kina bachi baki da lafiya, har na fada mata zancen yarinyar nan mai kama da Rufaida”

Gabanta ya fadi, sai ta lumshe ido, ta kai hannu ta rika hannunsa.

“Duk abunda nai saboda kai nai Alhaji, dan Allah karka juya min baya”

“Ban gane ba...”

Ya fada yana kama kallon rashin fahimta, sai ta bude idon ta saki hannunsa ta ce

“Ya kamata ka huta saboda ciwonka yana bukatar hutu, ni na naji saukj ina ganin zuwa anjima ma go be likita zai sallameni, na damu lafiyarka sosai”

Ya gyada mata kai.

“Zan yi kokarin hakan inshallah”

Sai goma da rabi na dare ya bar asibitin, bayan ya bata wayarsa tayi waya da yaranta kuma sun jadadda mata cewar gobe suna nan tafe ganinsa yasa ta daure ta nuna kamar taji sauki har ma da cin abinci dan kar ya damu.

*** *** ***
Chapter 68 · 0% Book details