Sashe 17
Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zain ya fada yana saka hannayensa duka a aljihu. Sai Doc Hafsat ta wara ido.
“Oh kai na tuna haka ne a jikin file dinta shiyasa take jin magana ai”
Zain dai be ce komai ba ya nufi kofar fita. Daga asibitin gidan Anty Ummi ya nufo, yana yin parking ya fito ya nufi cikin falonta, tana zaune cikin falon amman fuskarta babu annuri idanuwanta duk sun kumbura kamar ba nata ba, sallamar da yai ma can kasan makoshinta ta amsa masa, hakan ne ya karantarda shi damuwarta tun gabanin ta gabatar masa da ita, ko da yake yasan dalilin damuwarta baya nasaba da mutuwar makociyarsu wato Anty Rukaiya yayar Farhat wacce yaga ana jana'iza dazu daya dawo da rana.
Yayi tsammanin zata tambayeshi Hafsatu manga ne, amman sai yaji shiru bata masa maganar ba, sai kawai ta bijiro masa da maganar Farhat.
“Zain yarinyar nan tana cikin wani hali, kuma duk abunda ya faru nice, da ace ban yi maganar da Rukaiya ba da duk haka be faru ba”
“Haka Allah yaso”
Ya fada kamar be damu ba, sai wara ido yake dan bega Amal da yan'uwanta sun fito ba.
“Na sani, amman kadai yasan halin da yarinyar nan zata shiga, yanzu kauye zata koma da zama, taya mace kamar Farhat wacce ta saba da zaman birni zata iya zama kauye? Ga rashin yar'uwarta ga cin amanar da wannan Auwal din yai mata da wanne zata ji?”
Ta karasa idonta na cika da kwalla. Shi kuma ya bata amsa kai tsaye yana canja channel din tv.
“Da wanda yafi mata ciwo...”
Wata banzar harara Anty Ummi ta watsa masa, taya zai bata irin wannan amsar wato be ma damu ba, shi bata bashi tausayi.
“Tashi ka bar min gidana”
Juyowa yai ya kalleta yana kokarin tuna irin amsar daya bata, sai kawai yai murmushi. Sometimes Anty Ummi tana acting kamar wata karamar yarinya, da ace kyaleta yai sai kuma tasa complain tace tana ta magana ya shareta kamar ita ba yayarshi ba ce, tayi tai mitar cewar isar da kasaitar da yake a gidansu ko wani gurin har da ita zai yi ma, ko da yake wani lokacin duk irin maganar da zata yi ba zaice uffan ba indai ba yan maganar ke saman kai ba, idan kuma ya cilastawa kansa amsawa maganar ba zata mata dadi ba musamman idan akan Farhat ko familynsu take maganar, sai kawai ta sauke masa haushi, haka take masa ko da da mijinta ta samu tsabani shi da yayanta take saukewa haushi saboda shine a gidan kullum.
“Wai ina maka magana kana watsomin wata amsar marar dadi ta dabam, mafita fa nake nemawa yarinyar nan...”
Be kula zancen ba, sai ya dauko mata wata magana da daban.
“Mama ta farka dazun nan, kuma abun ya zo mata da sauki sosai...”
Tasan wa yake nufi da mama wato Hafsatu manga.
“Dan Allah dan Annabi Zain ka rufe babin yarinyar nan bana son ka sake min magana akanta”
Tana kaiwa nan ta tashi ta nufi dakinta cikin bacin rai, a tunaninta ga abunda ya kamata ya maida hankali suyi magana akai amman ya kasa sai wata banza can yake dauko mata zancenta.
Shi na tashi yai ya fice, a Masallacin unguwar yai sallah isha'i sannan ya isa Kanwurin, yayi mamakin ganin Hameeda a harabar aje motoci tsaye da wani magidanci suna fira, ba komai ke bashi mamaki ba but this one ya bashi mamaki sosai, ko da yake be san alakar dake tsakaninsu, amman be kama da mai neman wani abu a gurinta ba, amman idan har son ta yake ai da cikin gidan zata shiga a shi miyasa ta tsaya da shi inda ba a tsayuwa dan fira? Kuma gurin da kowa zai iya ganinta ciki har da shi? A zahiri ba yayi ma abu kallo biyu da sunan kwankwancewa ba halinsa ba ne, sai dai yana daya daga cikin dabi'unsa kurawa abu ido sau daya yai masa kallon tsab ya kawar kai ko minene kuwa, ba dan haka ba da sai ya sake kallon mutumen dan kara tantancewa.
‘To kai miye abunda ya dame ka?’
Wata zuciyar ta tambayeshi, sai kuma dayar ta bashi amsa.
‘So if ta fara kula wani hakan yana nufin tayi giving up akai na, zata barni na huta am happy for her’
Ya fada a ransa yana kunna kansa a sashen Mai Martaba.
*** *** ***
Ba karamin fama Doc Hafsat tai da takwararta Hafsatu manga ba, kamin ta sami ta yarda a cire mata drip din ta shiga tai fitsarin shi ma kuma da rigima, bayan ta fito Doc ta kara duba halshenta sannan ta dauke da kanta ta dorata saman gadon tana mata murmshi kasancewarta mai yawan far'a ga son mutane, abu ne mai wahala kaga fushinta.
Tana kokarin daura mata drip din ne wayarta tai ringing alamar kira, cikin sauri ta fiddo wayar ta cire safar hannunta tai picking.
“Hello Ya Auwal...”
Bayan wani lokaci sai ta amsa da.
“Ban manta ba Wallahi akwai abunda nake, da zarar na gama zan bar asibitin gaba daya sai na kawo maka am sorry”
Daga haka ta maida wayar aljihun Lapcoat dinta, ta kama hannun Hafsatu manga tana murmushi.
“Rumtse idonki na nuna miki wani abu”
Ba musu ta runtse dan a tunaninta wani abun ne da gaske, ko da ta bude har ta maida drip din a hannunta. Fita tai ta dawo dauke da allura har biyu a hannunta, Hafsatu manga na ganin allura ta zabura ta tashi zaune kamar zata sauka saman gadon sai kokarin kwalla take.
“Ke ba allura zan miki ba, ai ke kawata ce ba zan miki komai ba”
A cikin ruwan tai allurar, kamin tai ta biyu har bachi ya buge Hafsatu daga zaune, sai data gyara mata kwanciyarta, sannan ta fice daga dakin.
GIMBIYA HAMEEDA POV.
Burinta ya cika, abun nema ya samu daman son kawai take Zain ya ganta tsaye da wani tana zance, wannan dalilin ne yasa taki shiga da bakon can cikin duk kuwa da kasancewar ba girmansu ba ne, ko ba komai tasan Zain zai raya wani abu a zuciyarsa. Ta jidadi sosai da Allah yasa yau a nan ya faka motarsa ba a sashensa ba ko da yake ko a sashensa yai dole zai gani tunda zai ya wuce wannan hararar kamin ya isa part dinsa. Bata kara bata minti biyar a gurin ba ta sallami bakon ya wuce ita kuma ta dawo cikin gida ranta fari kal...
______________________________________
Al-hamdulillah am back...
Kwana biyu bana online saboda matsalar wayata ne, da fatar ba kuyi fushi ba😍🥰
*HAFSATU MANGA*
_Yarinyar Kauye_
Wattpad @KhadeejaCandy
1⃣5⃣
GIMBIYA HAMEEDA POV.
Cike da fadinciki ta dawo part dinsu, ta wuce dakinta fuskarta shimfide da murmushi, ji take kamar ta fara taka wani matakin nasara a yanzu, ba kamar da ba ne, yanzu kam ta shirya yin komai dan cinma burinta, tsoro fargaba tsaiko inda inda duk ba nata ba ne a yanzu.
Matukar abunda tai abaya tace zata sake yi a yanzu, zata iya rasa Zain har abada rasanwan na gaba daya ba wai karo na biyu ba.
“Muna yawaita mafarkai, wani lokacin abunda yake nesa ake nuna mana wani sa'in kuma abunda yake kusa da mu ne, babu abunda zai iskeka a zaune har sai ka motsa...”
Ita kadai take magana da kanta, tana tsaye bakin gadonta sai kallon bedsheet din take.
“Shin ni ban cancanci jindadi ba ne a rayuwata? Dukan abunda yake nawa kokarin wuce ni yake sakaci yana sa na rasa abubuwan da yawa masu muhimmanci a gareni, shin laifine dan na nuna ina son Zain bayan kuma shi ya fara nuna min haka har ma ya bani dama...?”
Ta nufi gaban madubi tana kallon kanta.
“Me na rasa a jikina mi wata macen tafi ni da shi? Da har Zain zai gan ni kuma ya kawar da idonsa? Dole na gina sabuwar rayuwa da kai dole ne na tsara yadda komai zai tafi lokaci baya tsayawa kuma baya jiran kowa...!”
Ta kusan kwashe awa daya tana ta magana da kanta kamar mahaukaciya, daga karshe ta dauki mayafin abayar dake jikinta ta saka akanta ta fito ta nufi sashen Dada Yalwa.
A natse ta tura kofar falon as usual yau ma Hajiya Yalwa tana dakinta dan haka ta nufi dakin kai tsaye, ba tai zaton akwai wani a cikin ba bayan Dada dan haka ta fada dakin tana fadin
“Dada Yalwa Surukinki ya ce zai zo... ”
Makale mata maganar tai ganin Zain zaune saman gadonta yana shan kankan, tufafin dake jikinsa dazu ba sune a yanzu ba hkan ya tabbatar mata da wanka yai ya canja kaya. Sai tai saurin juyawa zata koma.
“Hameeda shigo mana”
Dada Yalwa ta fada tana dago mata hannu.
“Anjima zan dawo”
“Zo nan Hameeda”
Dada Yalwa ta sake kiranta, sai da ta kalli Zain dake shan kankanarsa sannan ta karaso cikin dakin fuskarta duk a fisgice, kusa da Dada ta zauna.
“Dada bana son nai wani abun ya ce na bata masa rai”
Ta fada muryarta na rawa kamar da gaske tsoronshi take. Dagowa yai ya kalleta sai tai saurin sadda kanta kasa ta mike tsaye.
“Zamu maganar anjima Dada”
Bata tsaya komai ba ta fice daga dakin da sauri. Daga shi har Dada da kallo suka bita har sai da ta fice sannan Dada ta maida dubanta gurin Yarima Zain.
“Wani lokacin ina jin kamar saboda ku nake rayuwa kai da Hameeda, a dakin nan kuka tashi tare muke kwana da ku mu tashi daku wani lokacin ma abinci tare muke cinsa, na fi son ku fiye da ko wane jika nawa, saboda kawai kuna marayu a lokacin ina jin kamar idan baku kusa da ni zaku rasa wani abun ne, wannan yasa lokacin da mahaifiyarka ta rasu na zabi rikaka da hannu domin yi maka duk abunda ka kake so, a lokacin da Hameeda ta rasa mahaifiyarta ita sai nasa aka kawo min ita, haka na raineku ku biyu, a da kai da ita babu abunda yake raba ku sai bachi, akwai kyakkyawar alaka da fahimta a tsakaninku kamin Ummi ta shiga ciki...”
“Ki daina zargin Anty Ummi Dada, babu ruwanta a cikin wannan”
Ya fada ba tare da ya kalleta ba.