← Book details Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 93

Sashe 70

Hafsatu Manga Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ba ni da tabbaci, amman Abbanku ya ganta kuma ya ce yarsa ce, ba dan ma wannan abun da ya faru ba da gwajin jini zamu yi a tabbatar idan hakan ne ko a a”

“Amman Anty ta fada miki sunan Mahaifiyarta?”

“Ban taba tambayarta ba, amman ta fada min cewar mahaifiyarta mahaukaciya ce”

“Na gode”

Ta sauke wayar, sai ta unkura ta tashi daga falon tana share hawayenta.

“Yan biyu lafiya dai? Ko jikin Hajiyar ne?”

Adama ta tambaya ganin yadda tun dazu take zubar da hawaye.

“Aa ba jikinta ba ne”

Ta fada a takaice sannan ta fice daga falon ta nufi inda Falon Abbah yake, tana dosar gurin gabanta na kara faduwa tana misalta irin halin da zai shiga idan ta fada masa, zai yafe ma Mama kuwa? Me zai biyo baya idan ta fada masa? Babu abunda zuciyarta bata saka mata amman a haka ta danne komai ta shiga falon.

“Assalamu Alaikum”

Tayi sallama cikin muryar dake nuna alamun ta yi kuka, yana daga tsaye yana gyara hannun babbar rigarsa da alama ma can zai je gurinta.

“Lafiya dai yan biyu?”

“Wata maganar na ke son mu yi da kai”

Ta fada ba tare da ta kalleshi ba.

“Minene Hajiyar ce wani abun ya faru a ita?”

Ganin yadda hankalinsa ya tashi yasa tai saurin ce

“Aa akan maganar Yarinyar da kaga ni a gidan Anty Ummi ne”

Ajiyar zuciya ya sauke ya zauna a kujerar da ke kusa da shi yana cigaba da kallonta tare da tattara hankalinsa guri daya ya mika mata.

“Abbah....”

Sai kuma tai shiru hawaye ya sauko mata, tana jin nauyi da kunyar kallonsa saboda abunda mahaifiyarta ta aikata, amman a haka ta daure ta daga ido ta kalleshi tare da kara kiran sunansa a karo na biyu.

“Abbah. Shi dan'adam ajizine, wani lokaci shaidan da zuciya suna yaudararmu mu aikata abunda zai kai mu ga halaka, wasu suna aikata hakan saboda kishi wasu saboda so wasu saboda kiyayya, wasu saboda hassada, amman abunda zan fada maka a yanzu na fi alakanta shi da so, so kuma mai tsanani, irin son nan da a yau kake fargabar mutuwa da raba ka da ni ko Husaina”

“Ba gane wannan karatun na ki na ke ba, idan ma mahaifiyarku mutuwa tai ki fada min kawai”

“Ba mutuwa tai ba, yanzu haka na barota tana can tana kuka da nadamar abunda ta aikata, sai a yanzu ta gane ta yi kuskure babba, amman komai zai zo da sauki idan ka sassauta fushinka a akanta, ko ba dan ita ba, ni Husaina yayanka ne kuma ba zamu so ganin bacin ran mahaifiyarmu da wani balle kuma da kai”

“Ke Hassana ki fada min ko minene bana son dogon sharhi”

“Yarinyar da ka gani a gidan Anty Ummi yarka ce Abbah, yar Mama Rufaida ce kanwarmu ce...”

Ya mata wani razanannen kallo.

“Ta ya akai kika sani? Kin tabbatar da hakan?”

Ta gyada kai tana cigaba da hawaye.

“Tabbas yarka ce Abbah jininka ce”

Yaja wani dogon numfashi na jindadi ya sauke tare da tashi tsaye yana takawa a hankali kamar zai fita kuma ba fitar zai yi ba, sai ya juyo ya kalli Hassana

“Ya aka yi kika sani?”

“Mama ce ta fada mana”

“Ita ya aka yi ta sani?”

“Saboda.... ”

Nauyin furta maganar take ji sai dai bata da wani zabi.

“Saboda ita ta aikata abunda ya sa ta bar gidan”

“Ban gane ba”

Ya tambaya cikin nuna rashin fahimtar zancenta. Ba karamin Jihadi tai na tsayawa ta tsara masa komai yadda zai fahimta ba. Ta tsammaci jin wata yasasshiyar magana daga bakinsa sai kawai taga yayi murmushi ya lumshe ido sai hawaye, zuwa can kuma ya dauki hannunsa ya dora a kirjinsa saitin zuciyarsa. Saurin tasowa tai ta matsa kusa da shi tana kiran sunansa.

“Abbah, dan Allah ka kwantar da hankalinka, zan yi iya abunda zan iya na fiddo da ita daga gidan yari ta dawo gareka”

“Taya taya tay?”

Yanzu kam kuka yake yana nuna hannayensa.

“Zata dawo Abbah ba ita ta aikata kisan kan ba, sheri aka mata na san Hassana ba za ta taimaketa ba, saboda tana tsoron kar abun ya dawo gurin Mama, amman ni zan karbi case din kuma zan tsaya mata, dan Allah Abbah karka tashi hankalinka”

Ta furta ciki kuka hankalinta a tashe tana tsoron kar wani abun ya same shi.

“A duk tsawon shekarun nan da nai ina tunani Rufaida amman na kasa yin komai ashe laifin Safiya ne? La'ilahaillah”

Ya kwantar da kansa jikin kujerar yana kuka.

“Haba Abbah dan Allah ka daina kukan nan, da wanne zan ji kai ko Mama? Karka jama kanka wani ciwon kuma”

Sai yai saurin ciro handkerchief dinsa ya share hawayensa.

“Gobe zan koma gida zan yi Anty Ummi bayani komai sai na karbi case din, inshallah zata fito”

Kai kawai ya gyada mata ya tashi ya shige bedroom dinsa.

*** *** ***
*Two days later...*

Gaba daya Zain kwaura yai daga cikin gidan, tun ranar da abun ya faru be sake kwana a cikinsa ba, sai ya koma gidansa dake can gra ya tare, baya zuwa office baya yin komai tun a ranar be sake zuwa masarautar ba, sai dai Mai Martaba ya aiko a dubashi, Ibrahim ne yake kawo masa abinci safe rana da kuma yamma, sai dai yadda ya kawo su haka yake daukarsu wani lokacin ya kan tirsasa masa ci, shi kanshi yana cikin damuwa ganin irin damuwar da abokinsa yake ciki.

“Zain ka rage yawan tunanin nan, ba zai amfaneka da komai ba”

Ya aje kofin shayin da ke hannunsa.

“Ba tunani na ke ba Ibrahim, idan tunani na ke ban san wanne zan yi ba, rashin Haleema ko Farhat? Ko kuma zaman Hameeda a gidan nan, ko kuma rayuwata ta nan gaba? Mama da aka kai aka rufe ko kuma me? Kawai ina nisanta kaina ne da mutune saboda na fi jindadin hakan, bana son na cigaba da rayuwa a gidan da Hameeda take zaune, bani da wani buri yanzu wanda ya wuce na ganinta ta ta wulakanta”

“Ba abu ne mai sauke mutum ya fuskanci kalubale kamar wannan ba, amman ka san sai special people Allah yake jarraba har haka ko?”

Zain yayi dariyar data kara fito da ramar da ke fuskarsa.

“Sa cina ne Ibrahim, na san yarinyar nan tana da hannu a mutuwar Haleema but still na yarda na zauna gida daya da ita da Farhat, wannan ai isgilanci ne na yi wasa da ran yar mutane, am such a bad guy na wahalar da yar mutane ban taba samun damar fada mata wata kalma mai dadi ba, ko da bata so na, ai aurena tai yi, na shirya yin rayuwa mai kyau da tsabta da ita amman Hameeda ta wargaza komai, duka wadannan kalubalen ta fuskance su ne saboda ni”

Yayi saurin mikewa tsaye saboda hawayen da suka cika masa ido. Wayarsa ce tai ringing sai ya daga kansa sama yana kokarin maida hawayen and he can't pick the call. Dan haka Ibrahim ya kai hannu ya dauka yana karawa a kunne Anty Ummi ta ce masa.

“Zain ga mu nan kan hanyar zuwa gurin Mama ka taho yanzu”

“Okay”

Ya amsa a madadin Zain sannan ya maida wayar muhallinta ya kalli Zain.

“Anty Ummi ce tace tana hanyar zuwa gurin yarinyar nan ku hadu a can”

Hannu Zain yasa ya matsi idanuwansa sannan ya dauki jacket dinsa dake kan kujera ya saka suka fito tare da Ibrahim. A mota daya suka shiga Ibrahim ke driving yana ta masa hira sama sama amman har aka isa Zain be ce uffan ba. A waje ya tsaya ya kira Anty Ummi ya sanar mata waje ta kwatanta masa inda take sannan suka shiga.
Kato gidane mai kamar ma'aikata, daga wajen gate din sai ka dauka babu kowa haka a harabar gurin, sai dai reception dinsa kamar ko wane reception yake, a cikin ma'aikatan dake gurin akwai marar uniform wasu sam ba zaka dauka police ba ne. Da kwatanccen da Anty Ummi tai masa yai ta bi har ya iso inda suke. Tana zaune saman wani tebur tare da Barrister da be rike sunanta ba, ya san dai ita ce wacce Anty Ummi ta fada masa cewar yar yayarta ce kuma yai magana da ita a lokacin da suke kan mata bayanin yadda komai yake, sai kuma mutumen nan na ranar nan wand ya ce Hafsatu manga yarsa ce, Zain baya cikin mood din tambaya dan haka be ce masa komai bayan kallonsa da yai ya dauke kai ya kalli wani mutum daban dake tare da su.

“Sunnanta Barrister Hassana, ba wacan ba ce amman twin sister dinta ce”

Anty Ummi ta fada masa yana kokarin zama shi da Ibrahim.

“Miya faru da waccan?”

Ya tambaya yana kara kallon Barrister dan kara tantancewa, lallai wannan ta fi wacan haske ita kuma wacan ta fi wannan jiki.

“Labari ne mai tsawo idan mun fita a nan zan maka bayani”

Sai duk suka maida hankalinsu a gurin Hafsatu manga wacce aka fito da ita a yanzu, Alhaji Habib ne yai saurin mikewa tsaye ya doshi inda take tun kan ta karaso sai ta zo ta guje kamar za ta je gareshi ta gauce ta je ta rumgume Zain tana kuka. Tsaye Alhaji Habib yai yana hawaye, Anty Ummi kuma ta tashi ta karasa inda Hafsatu manga take ta shafa kanta tana kuka.

“Mama...”

Sai Hafsatu manga ta buge mata hannu ta kara lafewa a jikin Zain.

“Ita ce Hafsat..?”

Hassana ta tambaya tana nunata. Sai Zain ya dauketa ya dora saman kafafunsa yana mai jin kukanta har cikin rans.

“Yi shiru Mama, fada min mi akai miki?”

“Ba a min komai ba, bana son nan din ne”

“Wahala suke baki?”

“A'a suna samu shara dai da daukar kaya kuma suna cewa mu wanke bandaki”

Wani irin tausayinta ne ya kamashi.

“Ki yi hakuri zan dauke kinji? Nan da wani dan lokaci kadan za ki bar nan”

“Ba yau ba?”

Ta bata fuska. Sai ya rasa me zai ce mata har sai da Barrister Hassana ta matsa ta kama hannunta ta rike.
Chapter 70 · 0% Book details